African LanguagesHausa

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook Mamman Modukur, ranar tara ga watan Yunin 2025, ya yi da’awar cewa Abba Kyari ya kai matakin mataimakin supeto Janar na ‘yan sanda kuma yanzu ya isa ya sami karin girma zuwa sufeto Janar na ‘Yan sanda. Mannan Modukur ya kuma yi wasu karin bayanin da ke bukatar tantancewa.

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Hukunci: Karya ce. Wadansu daga cikin bayanan karya ne, a yayin da wasu kuma yaudara ne kawai babu isashen hujja.

Cikakken bayani

Ranar tara ga watan Yunin 2025 , wani mai amfani da Facebook Mamman Modukur, ranar tara ga watan Yunin 2025, ya yi da’awar cewa Abba Kyari ya kai matakin mataimakin supeto Janar na ‘yan sanda kuma yanzu ya isa ya sami karin girma zuwa sufeto Janar na ‘Yan sanda. Mannan Modukur ya kuma yi wasu karin bayanin da ke bukatar tantancewa.

Daga cikin bayanan da ya wallafa, Modukur ya kuma yi da’awar cewa turjiya a cikin hukumar ‘yan sandan na nuna cewa “akwai masu ki shi sosai cikin hukumar ‘yan sandan” ana kuma zargin wadansu wadanda ba’a bayyana ko su wane ne ba da kasancewa “maciya amana a hukumomin tsaron Najeriya” wadanda suke kaskantar da aikin da Kyari ya yi.

Mai da’awar ya ce akwai wata babbar badakalar da ta hada har da kungiyar ‘yan awaren IPOB, abun da ke nufin cewa tsauraran matakan da Kyari ya dauka kan kungiyar ne ya jawo mi shi bakin jini daga manyan hafsoshin tsaron kasar. Ya kuma kara da cewa babu sauran kararrakin da aka shigar kan Kyari har ma da cewa masu safarar kwayoyin da aka danganta su da shi ma an riga an sake su.

“Babu wata kara a kan Abba Kyari domin ko su wadanda aka kama da aikata laifukan da aka danganta da shi su ma an sake su, wato masu sayar da kwayoyin da wasu yaran shi suka kama. Kotu ta sake su fiye da shekara dayan da ya gabata. Wannan Najeriya ke nan,” wani bangare na labarin ya bayyana.

Yayin da wasu suka yi wa Kyari barka dangane da karin girman da aka ce ya samu, wasu sun nuna shakkunsu ne.

Aboubakar Yousouf tambaya ya yi dangane da da’awar inda ya ce “Anya Abba Kyari ya sami karin girma zuwa AIG? Ke nan ya tsallake DCP da CP?”

Joseph Oyerinde kuwa kai tsaye ya kushe da’awar da kiran shi labaran bogi wato “Fake news.”

DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar dan dakile yaduwar bayanan da ba daidai ba masannan ganin yadda Abba Kyari mutun ne sananne sosai ga jama’a.

Tantancewa

Da’awar farko: Abba Kyari ya kai mukamin mataimakin sufeto janar (AIG) kuma ya cancanki samun karin girma zuwa sufeto janar na ‘yan sanda wato IGP

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Hukunci: Karya ce

Abba Kyari mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne wanda aka dakatar da shi ba mataimakin sufeto janar ba ne. A watan Agustan 2021 aka dakatar da shi biyo bayan zarge-zargen cewa da hannunsa a wata zambar yanar gizo na kimanin dalar Amurka miliyan daya da digo daya tare da Ramon Abbas (Hushpuppi). Babu wata takardar da ta shaida cewa ya kai mukamin AIG bare ma ce ana kokarin kara masa girma zuwa IGP. 

Shugaban sashen kula da manema labarai da hulda da jama’a na hukumar ‘Yan sandan, Ikechukwu Ani, a cikin wata hirar da ya yi da DUBAWA, ya karyata zargin. Ya ce, “ainihi ma ba’a karawa mutane girma zuwa mukamin IGP; shugaban kasa ne ke zaben IGP. Da’awar wai an kara mi shi girma daga DCP zuwa AIG abu ne da ba zai yiwu ba. Hukumar ce ke kula da karin girma kuma ba’a kawo wannan batun a gabanmu ba. A iya sani na, hukumar ba ta sa hannu a kan wannan batun ba kuma ba wani karin girma kamar haka.”

A shekarar 2024, Hukumar ‘Yan sanda a karkashin jagorancin shugaban shi, DIG Hashimu Argungu mai ritaya, ya  sanar cewa an dakatar da karin girma irin na Alfarma a Rundunar “Yansandan Najeriya.

Da’awa na 2: Babu sauran tuhume-tuhume a kan Abba Kyari; wadanda ke zargin shi ma an sako har ma an wanke shi daga kowane irin zargi.

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Hukunci: Karya ce

Daga watan Afrilun 2025 Abba Kyari na fuskantar zarge-zarge da dama na aikata miyagun laifuka.  Da shi da wasu da dama ne Kotun Tarayya a Abuja ta umurce su da su kare kan su bisa zarginsu da ake yi da hannu wajen wani cinikin hodar ibilis mai nauyin kilogram 17.55 kilograms. Haka nan kuma ya na fuskantar tuhume-tuhumen da ke da alala da rashin bayyana kaddarorinsu. Sakin wadanda ake zarginsu tare ba wai ya na nufin an wanke Kyari daga na shi zarge-zargen ba ne.

Da’awa na 3: An wanke Abba Kyari daga duka zarge-zargen da ake masa

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Hukunci: Yaudara ce. 

Ofishin Antoni Janar (AGF) ya fitar da shawara a watan Maris 2022 inda ya bayyana cewa bisa hujjojin da ake da su, akwai alaka tsakanin Kyari da magudin wanke haramtattun kudade a shari’ar Hushpuppi.  AGF din ya kyma fayyace cewa bai wabke Kyari daga wani zargi ba. Wannan zargin da ma a kan tuhumar da ake ma sa na wanke haramtattun kudade ne. Kyari na cigaba da fuskantar shari’a kan miyagun kwayoyi da sauran laifukan da ke da alaka da wadannan zarge-zargen. DUBAWA ta tuntubi matamaikin antoni janar din na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da jama’a Kamarudeen Ogundele, ta wayar tarho dan tantance gaskiyar wannan da’awar. Sai dai cewa ya yi “zan mayar da martani da zarar na sami karin bayani.” Ko da shi ke har zuwa lokacin da muka hada wannan rahoton bai mayar da wani martani ba.

Da’awa na 4: Kyari na fuskantar matsalolin shari’a ne saboda kishi da irin makarkashiyar da aka yi ma sa a hukumar ‘yansanda saboda rawar da ya taka a batun IPOB.

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Hukunci: Babu isasshen hujja

Wannan ra’ayi ne ba zargi ba. Dakatar da tuhume-tuhumen da ake wa Kyari sun danganci binciken da Najeriya da hukumomin kasa da kasa ke yi ne ba wasu bayanann da ba su da tushe ba ko kuma wani batun kishi tsakaninsu su ‘yan sandan. 

Da’awa na 5: Kotu ta saki duk wadanda aka kama da safarar miyagun kwayoyi a karkashin Kyari, kuma wannan na nuna gaskiyarsa.

Tantance gaskiyar da’awar da aka yi kan Abba Kyari, halin da ya ke ciki, batun karin girma da inda aka kwana a batun shari’arsa

Hukunci: Yaudara ce

Yayin da aka yanke hukunci kan wasu daga cikin wadanda aka kama su tare, matakin bai wanke Kyari ba. Har yanzu ana bukatar shi ya kare kansa a shari’ar da ake yi inda ake zargin shi da taba kayayyakin da aka ajiye a matsayin hujjoji ko kuma shaidar laifukan da ake zarginsu da tabkawa. 

A Karshe
Abba Kyari bai sami karin girma ba kuma ba’a wanke shi daga zarge-zargen da aka yi masa ba. Rahotannin da muka gani ba su goyi bayan duk wadannan batutuwan ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »