Zargi: Wani mai amfani da TikTok na zargin wai lokacin da su ke wani taro na APC Bola Tinubu, ya fadawa masu goyon bayan shi su kwace akwatunan zabe a daidai lokacin da ake jefa kuri’ar. Mutumin ya ma hada da hoton bidiyo.

Ko daya bidiyon bai ambaci akwatunan zabe da ranar zabe ba. Bisa dukkan alamu, wanda ya sa hoton ne ya gyara shi ya sa wannan labarin dan yaudarar wadanda ba su ji ba su gani
Cikakken bayani
Makwanni kalilan ya rage ‘yan Najeriya su jefa kuri’ar da za ta samar musu da sabon shugaban kasa. Dan haka magoya bayan manyan ‘yan takara sun fara taka rawar gani a yakin neman zabe.
Domin shawo kan al’umma su zabi ‘yan takaran su, magoya bayan ‘yan takaran na rarraba bayanai, karairayi da ma dai duk wani abun da zai hana mutane zaben ‘yan hammaya.
Sakamakon haka ne wani mai amfani da TikRok Mr_Noble Godson (@nobleboss8) ya wallafa wani bidiyo da ake zargi ba da sanin wadanda ke ciki aka wallafa ba inda Tinubu dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC ke ce wa magoya bayansa su kwace akwatunan zabe daga an je jefa kuri’ar.
Bidiyon ya sake bulla a tiwita a shafin wnai Honyfactory (@Honyfactory) wanda shi ma ya ce an fitar da bidiyon ta barauniyar hanya ne ba tare da sanin wadanda ke ciki ba.
Da ya ke mayar da martani a kan bidiyon, @cent3ric ya bayyana cewa babu yadda za’a iya yin hakan a wannan zaben. “Sai dai ya yi haka a Legas ba a Najeriya baa, ba taba ganin hauka ba ke na,” ya rubuta.
Wani mai amfani da tiwita kuma O:G:B (Ogbonna_ugwuowo) cewa ya yi abin da ke cikin bidiyon ne ya hana dan takarar shugabancin kasar sabya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla. “Yanzu mun ga dalilin da ya sa ya ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya,” ya rubuta.
Bidiyon har ma ya kai WhatsApp inda ake raba hoton tare da gajeren bayani kan abin da ake zargi Tinubun ya fada.
Bisa la’akari da yadda irin wannan labarin zai iya janyo rikici musamman tashin hankali lokacin zabe ne ya sa DUBAWA ta ce za ta binciki gaskiyar wannan lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da sauraron bidiyon baki daya inda ta kula da cewa ko daya ba’a yi amfani da mahimman kalmomin da su ka hada da “akwatin zabe” ba lokacin jawabin da Tinubun ya yi, mun kuma ga cewa bidiyon bai fara daga farko ba ke nan an yanke wani bangare kuma akwai wanda ya fi wannan tsawo.
“Ku yi nazarin batutuwan da suka shafi illimin halin dan adam. A ina mu ke? Ba za a raba ikon siyasa a gidan abinci ba. Ba za’a raba shi kamar irin abincin da akan saya a je gida a ci ba. Sai dai ta abin da mu ke yi. Dagewa ne ko ta kowane hali. A yi yaki domin shi! A anshe! A kwace da karfi a tsere da shi”
Kalmomin da dan takarar shugaban kasa a inuwar APC ya yi amfani da su ke nan a bidiyon mai tsawon dakiku 48.
Mun kuma gano wani rahoto da jaridar Gazette ta rubuta a watan Disembar 2022, inda ita ma ta yi amfani da wannan bidiyon tana zargin Tinubu na kira ga magoya bayansa su yi amfani da karfi su kwace akwatunan zabe.
“Dole a kwace iko, a kwace da karfi ko ta halin yaya: In ji Tinubu,” taken rahoton ya bayyana. A cewar Gazette, Tinubu ya kara yawan kwanakin ziyararsa a Burtaniya bayan da ya gabatar da kasida a Chattam House daga farkon wannan makon.
Wani mutumi wanda ya bulla a karshen bidiyon shi ne ya nada, mun kuma gano cewa sunarsa Mustapha Abdullahi, wanda shi ne mataimakin shugaban ‘yan jam’iyyar APC reshen Burtaniya. Mun iya amfani da manhajar tantance hotuna wato reverse image search na Google.
A wani rahoton da jaridar NNN ta wallafa, Abdullahi ya tattauna jawabin da Tinubu ya yi a Chattam House.
Da muka yi amfani da mahimman kalmomi wajen bincike a YouTube mun gano bidiyon amma wanda ya fi tsawo. An wallafa shi a kafofi da dama wadanda su ka hada da OmoELuBlogTV, Prime Reporters News, DIVINEVIBESTV da sauransu.
Haka nan kuma an sake wallafa bidiyon ko a makon da ya gabata a shafin NIGERIA POLITICS TCGM, inda su ka ja hankalin jama’a kan cewa Bishop na cocin Anglica a Najeriya Bishop Seun Adeoye na kira da jami’an tsaro da su gayyaci dan takarar APCn bisa wadannan kalaman da ya yi su kuma yi ma sa tambayoyi.
Wadannan bidiyoyin wadanda su ka fi tsawo sun nuna Tinubu yana kwatanta dimokiradiyya da tattalin arzikin Najeriya da ta kasar Indiya. Inda ya ce kasar Indiya ce ke da dimokiradiyya mafi girma a duniya kuma wadanda ke da matsakaicin karfin tattalin arziki a kasar sun fi na kowace kasa a duniya arziki.
“…. Ba su suka yi ba. Ba za mu danganta komai da kaddara ba; kwacewa ake yi. Yanzu muna gwagwarmaya kan sa ne. Me ne? Iko. Iko. Ikon siyasa, lantarki. Wutar lantarki na zaman daya daga cikin samu mafi mahimmanci da dan adam ya yi a shekaru fiye da duba dayan da suka gabata. Ku je ku yi nazarin illimin tarihin dan adam.”
Wannan ne abin da Tinubun ya fara fada kafin bangaren da ake ta yawo da shi a TikTOk da sauran shafukan sada zumunta. Wannan ya nuna cewa furucinsa ba shi da wani dangantaka da kwace akwatunan zabe.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa bayani da Tinubu ya yi a bidiyon mai tsawo – wato inda aka yanko mai tsawon dakiku 48 din da ake ta yawo da shi a soshiyal mediya – bai ambaci akwatunan zabe ba. Duk da cewa dan takaran shugaban kasar ya baiwa magoya bayansa karfin gwiwar “karba” da “kwace” iko ko ta kowane irin hali, bai ce a je a kwace akwatunan zabe yayin da ake jefa kuri’a ranar zabe ba. Dan haka wannan zargin ba gaskiya ba ne.