African LanguagesHausa

Wai wata ‘yar ƙasar Brazil wadda ta auri dan tsana ta haifi yara uku, shin da gaske ne? 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wata yar ƙasar Brazil da ta auri dan tsana ta haifi yan Uku 

Wai wata ‘yar ƙasar Brazil wadda ta auri dan tsana ta haifi yara uku, shin da gaske ne? 

Hukunci: Yaudara ce! Bincike ya nuna cewa babu yadda za’a yi mutum da ’adam ya haifi dan tsana.

Cikakken bayani

Shafin A yau da ke Facebook ya yi labarin da ke bayani kan wata mata yar kasar Brazil mai suna Meirivone Rocha Moraes wadda ta yi ikirarin haifar yan Uku tare da mijinta dan tsana.

Bisa bayanan da A Yau ta bayar,  matar ta ce ta yanke shawarar aurar dan tsanar ne bayan da ta gaza samun namijin da za ta iya natsuwa da shi, mai rikon amana.

A karshe dai mahaifiyarta ta hada mata dan tsana wanda suka sanya wa suna Marcelo inda suka yi soyayya ta aure shi, gashi har an samu albarkar aure…

Wai wata ‘yar ƙasar Brazil wadda ta auri dan tsana ta haifi yara uku, shin da gaske ne? 

Wannan labarin ya dauki hankalin jama’a sosai domin jin kadan bayan wallafa shi mutane sama da dubu daya suka latsa alamar like, ya kuma sami tsokaci sama da 400 yayin da aka sake rabawa sau 50.

Da DUBAWA ta duba irin ra’ayoyin da jama’a suka bayyana, yawanci sun gwada cewa karya ne kuma ma rainin hankali misali Abdulmumin Ibrahim Khalil ya yi bayani kamar haka: “Cewa za ku yi an samu wani ya yi wa ‘yar ysana kokari kawai ya yi masa ‘ya’ya uku.” Yayin da shi kuma Abdoulrasheed Sami Mai Atamfa ya ce “da na gida da na asibit Allah ya ba su lafiya.” Bisa la’akari da yadda ake yawan wallafa labarai irin wadannan a shafukan sada zumunta wadanda yawanci su kan kasance yaudara ne ya si DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan batun da fadakarwa da wayar da kan jama’a

Tantancewa

Mun fara da binciken mahimman kalmomi inda muka gano cewa lallai labari ne wanda ya faru a zahiri a kasar Brazil da wata mata yar shekara 37  Meirivone Rocha Moraes ‘yar kasar Brazil wadda ta auri dan tsana a ranar 20 ga watan Nuwamba 2021. Labarin ya ce ta haifa  masa yara uku, da mai shekara 1 Marcelinho da yan biyun da ta haifa bayan shi wadanda aka radawa sunayen Marcela and Emilia, wato namiji da na mace. 

Bayan nan mun cigaba da bin labarin inda muka gano makalar shafinta na Instagram inda a nan ma muka ga cewar da gaske ne ta aurin dan tsanar da mahaifiyarta ta dinka mata. A A wannan shafin ne ma muka ga hotuna da bidiyoyi da yawa na ta da iyalin ta na ‘yan tsanan. 

To sai dai duk da cewa akwai wadannan hotunan na ta wadanda suka nuna cewa tana cikin walwala da nishadi, hakan na iya faruwa a zahiri?

Domin karin bayani akan lamarin, DUBAWA ta tuntubi likita kwararre mai su na Dr. Joshua Badi, in da ya shaida mana ba zai taba yiwuwa ba mutun dan adam ya haifi dan tsana saboda shi kan sa mahaifin su Marcelo dan tsana ne mara rai dan haka bazai iya haihuwa ba. Ya shaida mana da cewar kila tana da tabin hankali ne yasa ta ke zaton tayi auri dan tsana har da haifan masa yaya ko kuma dai kawai tana yi ne dan farin jinin kafar yada zumunta.

A Karshe

Bincike ya nuna wannan labari Yaudara Ce! Duk da cewa matar ta fito fili tana cewa ta haifi yara da maigidanta wanda mahaifiyarta ta dinka mata kuma kowa ya sani, babu yadda mutum dan adam zai haifi ‘yan tsana.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button