|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu masu amfani da shafin Facebook sun yada bidiyo kala-kala da ke nuna yadda robot ko mutum-mutumi ke ayyukan gona a wasu gonakin ‘yan kasar Chaina ko Sin abin da ke zama barazana ga makomar ma’aikatan gona a sassa na duniya.

Hukunci: KARYA CE. Bincike da nazari ya gano cewa wannan bidiyo an yi masa kwaskwarima ko sauya shi, duba da cewa an yi amfani da fasahar zamani ta digital inda aka dauke mutane da ke a bidiyon aka maye gurbinsu da mutum-mutumi ko robot.
Cikakken Sako
Ci gaban fasahar zamani da sauyin yanayi da sauyin dabi’ar masu bukatar kayayyaki ta sauya yadda harkokin aikin gona yake a duniya. Yayin da kasashe suka himmatu wajen samun wadatuwa ta fuskar abinci da samar da kayayyakin ayyukan gona, matsalar tsaro da karancin abinci na ci gaba da zama manyan kalubale musamman a yankin Afurka kudu da hamadar sahara. Duk da cewa bangaren aikin gona na samar da aiki (employing) ga ‘yan Najeriya fiye da kowane bangare inda yake da kaso 22.6% a ma’aunin GDP bayan watanni hudun farko a 2024, akwai dai tarin kalubale a gaban harkokin na samar da abinci ga ‘yan Najeriya.
Bayanai da aka samu daga Babban Bankin Duniya kan harkokin na samar da abinci (Food Security Update) sun nunar da cewa an samu hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya da kaso 37.5% ya zuwa watan Agusta, 2024.
Musabbabi na wannan matsala bai rasa nasaba da matsalar tsaro a yankuna da dama na kasar. Ta’addancin Boko Haram ya haifar da illa ga ayyukan gona (agricultural production) a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, haka nan rikicin manoma da makiyaya (farmers and herders) a Arewa maso Yammacin kasar ya kawo cikas a hanyoyin na samar da abinci a kasar. Wadannan matsaloli sun kara ingiza farmaki kan manoma. Rahotanni sun nunar da cewa akwai manoma (165 farmers) da suka rasa rayukansu saboda matsalar rikici da ke shafar manoma a shekarar 2024 ita kadai.
Samar da wata hanyar samar da abinci da za ta dauki lokaci mai tsawo za ta iya zama abar so ganin yadda ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsala, ga ta tsaro ga kuma ta rashin abinci. Wannan ne ma ya sanya ko da masu amfani da shafin Facebook suka yi ta yada wadannan bidiyo (video) kan yadda robot ke gudanar da ayyukan gona a wani kauyen kasar Chaina basu fuskanci turjiya ba.
Sakon da aka rubuta a kan bidiyon mai tsawon dakikoki 27 ya nuna cewa an gano wani robot a wani karamin kauye a Chaina yana gudanar da dukan ayyukan gona. Ga ma irin wadannan bidiyo a nan (here, here, da here). ‘Yan Najeriya da dama sun yaba da wannan wallafa wacce suka yi amanna cewa bidiyon abin a yaba ne kuma irin wannan shine abin da ake bukata cikin gaggawa a fannin ayyukan gona a Najeriya. Sai dai kuma wasu na cewa wannan bidiyo ne da aka yi masa kwaskwarima.
Duba da yadda ake samun mabanbantan ra’ayoyi kan wannan bidiyo ya sanya DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike a kansa.
Tantancewa
An dora bidiyon a manhajar Deepware.ai, wata manhaja da ake amfani da ita don gano ko bidiyo na gaskiya ne ko akasin haka. Uku daga cikin hanyoyi hudu da aka bi (four model) Deepware da Seferbekov da Ensemble sun nunar da cewa bidiyon hada shi aka yi kamar yadda sakamakon ya nunar da kaso 55%, 97%, da 83% daya-bayan-daya.
Sakamakon da aka samu. Asalin hoto: Deepware.ai
DUBAWA ta kuma gano wasu abubuwan da suka saba ka’ida bayan amfani da wata kafar ko manhajar wato ta Vid WeVerify,wacce ake amfani da ita don tantance bidiyo inda ake dauko wasu fannoni daga bidiyon don tantance su.
Ga misali an yi tsammani cewa za a rufe kafafun na robot lokacin da yake tafiya a cikin ruwa, sai dai an ga kafar na yawo a saman ruwa baki daya.
Alama da ke nuna kafar ta robot. Asalin inda aka dauko: InVid WeVerify
A wani bangaren kuma shi robot din baya iya kama abu da kyau da hannu, abin da ke nuna cewa dora robot din aka yi akan asalin wanda yake aikin.
Jar alama na nuna yadda robot ya kama tukunyar. Asalin hoton: InVid WeVerify
Mun gani a lokuta da dama a Chaina ko kasar Sin yadda robot suke gudanar da ayyukan gona amma babu wata kamanceceniya da robot da aka nuna wanda bidiyonsa ya zaga ko’ina. Ga misali robot a gonar Diantian Farm a wajen birnin Shanghai
Agribot a Diantian Farm, Shanghai. Asalin hoto daga: China Daily.
Karshe
Duk da cewa kasar Chaina ko Sin na amfani da robot ko mutum-mutumi da kirkirarriyar basira wajen gudanar da ayyukan gona, wannan hoton bidiyo da aka gani wanda ya bazu a shafukan sada zumunta, an yi dabaru ne na masu fasaha aka hada shi, don haka karya ce.




