African LanguagesHausa

Yaudara ce! Sojan da aka kama ya na baiwa ‘yan ta’adda makamai ba tsohon dan ta’adda ba ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa  bidiyon da ke da’awar cewa wani tsohon mamban kumgiyar Boko Haram ya shigo hannun mahukunta bayan da aka kama shi ya na saidawa ‘yan ta’addan makamai.

Yaudara ce! Sojan da aka kama ya na baiwa ‘yan ta’adda makamai ba tsohon dan ta’adda ba ne

Hukunci: Yaudara ce! Rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana wanda aka kama a sunan yana saidawa ‘yan ta’adda makamai a matsayin soja, sai dai, babu wata hujjar da ta nuna cewa tsohon mamban Boko Haram din ya shiga soja bayan da ya fita daga kungiyar. Bacin hakan, a shekarar 2022 ne aka nadi bidiyon ba kwanan nan ne ba kamar yadda ake fadi.

Cikakken bayani

A shekarar 2022, gwamnatin jihar Borno ta sanar cewa ta yi nasarar mayar da tsoffin mambobin kungiyar Boko Haram cikin al’umma. Shekaru uku bayan nan a watan Afrilun 2025 tsoffin mambobin kungiyar fiye da 390 suka yi bukin kammala karatu a shirin gwamnatin na sauya akidu masu kaifi da sake maido da su cikin al’ummar bayan da suka shafe watanni suna horaswa a jihar Gombe.

Shugaban hafsar sojoji, Christopher Musa, ya kwantanta shirin matsayin wata dabara ta sojoji wajen rage rashin tsaro a kasar.

Daga baya wani mai amfani da shafin X  @Chude ya wallafa wani bidiyon da ke da’awar wai sojojin Najeriyar ne ke neman wani tsohon mamban kungiyar Boko Haram 

Ana iya gani wadansu labaran makamantan wannan a wadannan shafukan na Facebook, a nan, nan, da nan

A ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025 mutane sama da 54,000 sun kalla bidiyon, wasu sama da 1,300 sun latsa alaman like sa’annan wasu 950 sun yi amfani da labarin, 173 sun adana wasu 81 sun yi amfani da labarin.

A cikin wurin tsokaci ko wato kwament section, yawancin wadanda suka tofa albarkacin bankinsu sun gaskata da da’awan sun kuma soki shawarar gwamnati na sake maido su cikin al’umma su zauna kafada da kafada da wadanda suka muzgunawa.

“Abun takaici ne, domin daga karshe, sojojin da suka kama shi ne za su fiskanci hukunci da wulakanci a wajen mahukunta,” a cewar  @Afrisagacity .

“Ta yaya za’a ce wai kasa ta yafewa ‘yan ta’adda ta kuma sanya su cikin rundunar sojojin Najeriya?”@Henryobi ya tambaya.

“Gwamnatin Najeriya ce babbar matsalar Najeriya. Wannan guntun wai shi ma na daya daga cikin tsoffin ‘yan boko haram din da aka yafewa,” in ji @Forsby31 .

Domin irin sarkakiyar da ke tattare da wannan batun da ma yadda gwamnatin Najeriya ta fi muradin sauya akidun tsoffin ‘yan Boko Harama a maimakon hukunta su, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan bidiyon.

Tantancewa 

DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance asalin bidiyoyi da hotuna na Google wato Google Reverse Image Search. Nan da nan ya hada mu da wani rahoton da aka wallafa a shafin CEOAfrica a watan Oktoban 2022. 

Rahoton ya bayyana cewa abokan aikin tohon sojan a rundunar sojojin Najeriya suka kama shi yayin da ya ke sace makaman da ya ke saidawa kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka da ‘yan ta’adda. A cewar shafin, sunan tsohon sojan  Iorliam Emmanuel.

Bayan haka DUBAWAta gudanar da wani karin binciken ta yin amfani da mahimman kalmomi dan gano sauran rahotanni makamantan wannan. Jaridar  Punch ma ta dauki rahoton ranar 13 ga watan Oktoba 2022 inda su ma suka ce an kama Emmanuel ne sadda ya ke kokarin kai bindigogi da makaman da ya sace zuwa wurin ‘yan ta’addan.

Haka nan ita ma jaridar Cable ta dauki labarin a shekarar 2022, inda ta kara da cewa tsohon dan asalin jihar Binuwai ne, kuma na mika shi ga sashen kula da leken asiri na sojoji dan gudanar da bincike mai zurfi.

Wasu karin rahotanni makamantan wannan wadanda kafofin yada labaran suka dauka a cikin watan Oktoban 2022 sun hada da wadannan biyun  wannan da wannan. A cikin irin wadannan rahotannin, babu inda aka kwatanta Emmanuel a matsayin mamban Boko Haram.

A Karshe

Wannan da’awar yaudara ce kawai kuma bidiyon na cikin shafukan yanar gizo-gizo tun watan oktoban 2022.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »