Zargi: Wani mai amfani da tiwita, ya na zargin wai ministan ilimi Adamu Adamu ya ce za’a dakatar da yajin aikin Malaman ASUU a mako mai zuwa.
Bincikenmu ya nuna mana cewa babu wani furuci makamancin wannan da aka danganta da ministan. Mai magana da yawun ministan shi ma ya karyata wannan zargin
Cikakken labari
Kungiyar Malaman Jami’a na ASUU ta kara wa’adin yajin aikinta da makonni 12 a watan Mayu, domin ta cigaba da tattaunawar da take fata zai sanya gwamnatin Najeriya ta amince ta kuma cimma bukatunsu.
Wannan wa’adin ya fara ne a ranar 9 ga watan Mayu bayan da ta cimma wannan matsaya a taron majalisar zartarwarta.
Daluban Najeriya sun yi zanga-zangar nuna bacin ransu da yajin aikin sun kuma yi kira da bangarorin da abin ya shafa da su yi kokari su ga an daidaita an dakatar da yajin aikin domin gyara masu makoma nan gaba
Sakamkon irin tasirin da yajin aikin ke da shi da irin tattaunawar da kowa ke yi da yajin aikin da ya ki ci ya ki cinyewa na tsawon shekaru da dama yanzu, an fara yada labaran karya dangane da batun.
Ashafin kungiyar na tiwita mai suna ASUU News (@ASUUNews), sun wallafa wani labari wanda ke cewa ministan ilimi, Adamu Adamu, ya ce za’a dakatar da yajin aiki a mako mai zuwa, a cikin labarin kuma an sanya hoton ministan.
Mutane sama da dubu hudu suka nuna sun amince da labarin wasi dubu daya kuma suka sake raba labarin a yayin da mutane 700 suka yi tsokaci a akn labarin.
Wata mai amfani da shafin tiwita mai suna _lexa (@Alicefaluyi), daluba a Najeriya cewa ta yi, “Thank you jesus ,” abin da ya nuna cewa ta yarda da labarin.
A yayin da wani mai amfani da shafin da sunan (@Aayomide9) ya mayar da na sa martanin yana nuna shakkun ya
“Ka da fi yi godiya tukuna, ba za’a iya yarda da wadannan mutanen ba.”
Tun ba yau ba ake yada bayanai iri-iri a soshiyal mediya dangane da yajin aikin. Daluban Najeriyar da abin ya shafa sun kasa kunne ne suna neman kowani irin labarin dangane da batun domin su san ko yaya makomar su za ta kasance. Dan haka ne DUBAWA ke tantance gaskiyar labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi.
Mun gano cewa ASUU ta samu cigaba a tattaunawar da ta ke yi da gwamnatin tarayya. Haka nan kuma, mun mun gano wani labari a jaridar Vanguard mai cewa ASUU na jira ta ji daga wurin gwamnatin tarayya bayan wata gabatarwar da ta yi mata
DUBAWA ta kuma gano wani labarin a jaridar Business Day inda gwamnatin tarayya ta ce “yajin aikin ASUU na cike da sarkakiya, batun ya wuce yadda ‘yan Najeriya ke tunani.”
Haka na kuma wani rahoton ya nuna matsayar kungiyar ASUU dangane da yajin aikin. Taken wani labari a jaridar Punch ya ce, “Mu ba mabarata ba ne, yunwa ba zai tilasta mana komawa bakin aiki ba – ASUU.”
Duk cikin wadannan labaran da mu ka gano, babu wanda ya yi bayanin cewa ma’aikatan za su dakatar da yajin aikin na su kamar yadda labarin ya bayyana.
Daga nan DUBAWA ta tuntubi mai magana da yawun ministan ilimin kasar, Mr Ben Goong dan jin karin bayani. Mr. Goong ya fada mana cewa labarin da ake dangantawa da ministan ilimin karya ne “fake News.”
A karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa furucin da ake dangantawa da ministan ilimi karya ne, mai magana da yawun ministan ya karyata labarin har ma ya kira shi “fake News” labaran bogi.