Zargi: Wani mai amfani da shafin tiwita ya wallafi bidiyon wani tarin kudi yana zargi wai sabbin takardun kudin Najeriya ne

Takardun kudin da ake zargin wai sabbin takardun kudin Najeriya ne a wani bidiyo karya ne. Takardun kudin wannan bidiyon takardun kudin euro ne kuma an gayara bidiyon ne ta yadda zai fadi wani abu daban ya kara haddasa rudani dangane da sabbin nerorin.
Cikakken bayani
Babban bankin Najeriya ta sanar cewa ta sake fasalin wasu daga cikin takardun kudin Najeriya wato Nera kuma daga watan Disembar 2022 za ta fara fitar da sabbin takardun kudin N100 N200, N500, da N1000 wadanda su ne sauyin ya shafa.
Sakamakon wannan sanarwar ta CBN ne wata mai amfani da shafin (DIVINE T) @folasheycrown22 ya wallafa wani bidiyo mai dauke da sabbin takardun kudin inda ya yi wa bidiyon taken “Sabbin Takardun Kudin Najeriya???”
An kalli bidiyon sosai, fiye da dubu 25 inda da yawa suka yi amanna da bidiyon sai dai cikin ire-iren tsokacin da aka yi a karkashin bidiyon wani mai suna Ahmed Musa LP (@generalzango) bai amince da wannan labarin ba.
Ya ce: “ wannan ba zai iya kasancewa takardun kudin Najeriya ba! A cikin sanarwar da aka yi babu nera 10.”
Q (@tokqboy) shi ma ya yarsa cewa kudin da ke cikin bidiyon ya fita daga wata kasar Afirka ne. “Sun yi kama da kudin Afurka ta Kudu,” ya bayyana.
Ana cikin haka, mai rubutattun wakoki Fela nPGM(@neo_pelz_) wani mai tsokaci shi kuwa cewa ya yi: Kamata ya yi babban banki wato CBN ta kare sabbin takardun kudin. “Ya kamata a sanya wa wadannan kudaden tambarin cewa na gwaji ne idan ba haka mutane za su fara sace su kwanannan,” ya bayyana.
Wadannan ra’ayoyin mabanbanta kumamasu karo da juna ne suka sa DUBAWA ta yanke shawarar tantancewa dan bai wa al’umma bayanai masu nagarta dangane da sabbin takardun kudin musamman idan har an riga an fitar da su.
Tantancewa
Domin tantance bidiyon da ma ainihin inda aka nade shi, DUBAWA ta yi amfani da manhajar InVid wadda ke taimakawa wajen tantance bidiyoyi ta yin nazarin abin da ke ciki da bayar da bayani dalla-dalla dangane da wuraren da aka yi amfani hotuna makamantan shi baya a cikin duniyar gizon baki daya. Da ya fara nazarin bidiyon mai tsawon dakiku goma sai ya dakata ba tare da ya gano wani abu mai kama da shi ba.
Sai dai da muka dauki hoton kudin sai mu ka gano cewa ba nera ba ne illa takarsun kudin turai wato euro. Bacin haka, kasancewar takardar kudin da su ke zargin Nera 10 ce ya nuna cewa da walakin goro a miya domin cikin takardun kudin da CBN ta bayyana babu nera 10. Sanarwar ta ce N100, N200, N500 da N1000. Takardun kudin N100 da N200 ne kadai ake gani daga cikin tarin kudin da ke bidiyon domin hotun bidiyon ba shi da kyau sosai. Dan haka sai mu ka duba salon zanen kudaden muka kwatanta su da kudaden sauran kasashen duniya, inda a nan ne muka gano cewa takardun kudin euro ne ba nera ba kamar yadda ake zargi
Babban bankin na sa ran fitar da sabbin takardun kudin a watan Disemba ne dan haka ba a kai ga fitar da kudin ba. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce za’a kaddamar da sabbin takardun kudin ranar 15 ga watan Disembar 2022.
A Karshe
Binciken bidiyon da muka yi bai nuna mana cewa akwai wani bidiyon da ke dauke da irin hotunan da aka gani a cikin bidiyon ba. Ko da shi ke nazarin da muka yi ya nuna mana cewa takardun kudin cikin bidiyon ba nera ba ne illa takardun kudin euro wanda ake amfani da shi a yawancin kasashen Turai. Dan haka wannan zargin karya ne.