Zargi: Wani bidiyon da ya gwado wata mata tana dukar karamiar yarinya a cikin bahon wanka har sai da ya fado har kasa ya faru a Saliyo ne

Wannan lamarin bai afku a Saliyo ba kamar yadda ake zargi, ya faru ne a wani wuri a kasar Uganda
Cikakken bayani
Wani bidiyo mai tayar da hankali da ke yawo a shafukan sada zumuntar soshiyal mediya a Saliyo ya nuna wata mata ta na dukar karamin yaro da takalmi har sai da ya fado kasa daga cikin wani bahon wankar da aka sanya shi a ciki. Wannan halin muguntar ta harzuka masu amfani da shafukan sada zumuntar sosai.
To sai dai masu amfani da soshiyal mediyar a Saliyo sun yi ta tabka mahawara dangane da inda wannan lamarin ya faru. Da yawa sun ce a cikin Saliyon wannan lamari ya faru a yayin da wasu kuma suka ce atabau ba a kasarsu ne aka aikata wannan ta’asar ba. Kadan daga cikin wadanda ke mahawarar sun tuntubi DUBAWA suna kokarin sanin ko lallai wannan lamarin a Saliyo ya afku kuma idan ba a nan ba ne to a ina ne?
Tantancewa
Domin amsa tambayar wadanda suka tuntubi DUBAWA mun bukaci sanin karin bayani daga wadanda suka tuntube da batun. Daga nan sai mu ka yi amfani da manhajar InVid wadda ke taimakawa wajen tantance abubuwan da ke dauke a cikin bidiyo da ma yin bitar hotunan dalla-dalla dan tantance mafarin su.
Da muka sanya bidiyon cikin manhajar ta nuna mana cewa matar da ke dukar sunanza Nabulime Dorothy kuma wadda ta ke duka ‘yar ta ce mai shekaru biyu na haihuwa.
Haka nan kuma mun gano cewa wannan lamarin ya afku ne a kasar Uganda kuma Hukumar Gudanar da Binciken Miyagun Ayyuka ta wallafa wannan labarin a shafin tiwita tare da yadda aka cafke ta kamar haka
“ ‘yan sandan Uganda @PoliceUG yau ta kama Nabulime Dorothy wanda aka gan ta cikin wani bidiyon da ke yawo a soshiyal mediya tana dukar diyarta mai shekaru biyu na haihuwa. Za ta bayyana a kotu ranar litinin dan amsa tuhumar da ake mata.”
Manhajar InVid ta bayyana sadda aka nadi bidiyon da ma inda aka nada. Karin binciken da muka yi a tiwita ya nuna mana cewa matar mai shekaru 22 na hauhuwa tana hannun ‘yan sanda kuma ta bayyana a gaban kotu ranar 5 ga watan Satumba dan amsa tuhumar da ake mata na cin zarafi da azabtarwa.
A Karshe
DUBAWA ta tantance bidiyon da ke yawo a soshiyal mediya na wata ‘yar yarinya mai shekaru biyu na haihuwa wadda mahaifiyarta ke dukar ta da takalmi. Binciken ya nuna cewa lamarin ya faru ne a kasar Uganda da ke yankin gabashin Afirka, ba a kasar Saliyo ba kamar yadda aka yi zargi da farko.