African LanguagesHausa

Bidiyon wasu mazaje da ke fada da adda ba ‘yan Najeriya ba ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani bidiyo  video  wanda ya nuna wasu mazaje guda biyu da aka yi zargin al’ummar Igbo ne suna fada kan hada-hadar kwayoyi a Indiya.

Bidiyon wasu mazaje da ke fada da adda ba ‘yan Najeriya ba ne

Hukunci: Yaudara ce! Shedu da aka tattara na kafafan yada labarai a watan Mayu sun nunar da cewa bidiyon ba shi da wata alaka da huldar kwayoyi a Indiya, lamarin ya faru ne a Jamhuryar Dominican. Haka kuma babu wata sheda da ta nunar da cewa  mazajen da ke fadan ‘yan Najeriya ne.

Cikakken Sakon

Wani mai amfani da shafin Facebook Aare Saka, ya yada wani bidiyo da ya nuna wasu mutane biyu suna fada dauke da addina a hannunsu, wadanda aka ce al’ummar Igbo ne ke fada kan hada-hadar kwayoyi a Indiya.

A bidiyon an rubuta “Clement Okafor da Kenneth Chukwudi, na amfani da addina suna sassara kansu a kokari na mamaye hada-hadar kwayoyi a Indiya,  duba abin mamaki yadda Okafor ya dauko hannunsa da aka sare!”

A bidiyon ya nuna yadda mazajen biyu ke fada ta hanyar amfani da addina a wani gidan mai gefen hanya, bayan fadan ne sai aka ga daya daga cikinsu ya tafi ya dauko wani abu mai kama da hannunsa da aka sare yayin fadan.

Za a iya ganin wata wallafar irin wannan kamar anan (here) da nan (here).

A baya-bayan nan, nuna banbancin kabila da yarfe na karya abune da za ka gani ana hirarsu musamman a shafukan sada zumunta ta intanet wannan yasa DUBAWA ta ga dacewar gano gaskiyar da’awar. 

Tantancewa

DUBAWA ta sanya wannan bidiyo a manhajar Google mai gano asalin bidiyo sai ta lura da cewa an wallafa wannan bidoyo a karo daban-daban.

Daya daga cikin rahotannin report an yi shi ne da harshen Spaniyanci da jaridar  LA VERDAD ta wallafa a ranar 15 ga Mayu,2024 a labarin da aka fassara na cewa “abokai na fada da adduna saboda wata mace; daya daga cikinsu ya rasa hannunsa (bidiyo)’inda aka hadar da bidiyon mai da’awar.

A cewar rahoton lamarin ya faru ne a Dominican Republic. Lamarin ya faru a gaban gidan mai inda aka fafata tsakanin mazaje biyu a kan mace, rahoton ya kara da cewa daya daga cikin masu fadan an sare masa hannu inda aka garzaya da shi asibiti yayin da dayan ya hau babur ya tsere daga inda lamarin ya faru.

A wannan rana jaridar New York Post ma ta ba da rahoto kan labarin.

A wata kafar yada labaran PAGINA CENTRAL ta ba da labarin a ranar 16 ga watan Mayu,2024 inda tace fadan an yi shine tsakanin Nelvin Felix da Kelvin Melquiades Trinidad an kuma yi fadan ne a kan titin Consuelo, a lardin San Pedro de Macorís a jamhuriyar ta Dominican Republic.

Ga ma wasu rahotannin irinsa anan (here) da ma nan (here).

A Karshe

DUBAWA a bincikenta ta gano cewa bidiyon yaudara ce aka shirya. Lamarin fada ne aka yi tsakanin mutane biyu a Dominican Republic akan mace, sabanin yadda mai da’awar yace kan hada-hadar miyagun kwayoyi ce a Indiya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »