African LanguagesHausa

BINCIKE: Yadda masu shafukan X suka rika amfani da fasahar AI a yada labaran karya kan yakin Isra’ila da Iran

Getting your Trinity Audio player ready...

Yaki tsakanin Isra’ila da Iran ya barke inda ya jawo kai hare-hare tsakanin kasashen biyu, hakan ya jawo lalata dukiyoyi da sanya mutane da dama kauracewa muhallansu. 

A ranar 13 ga watan Yuni, 2025, Isra’ila ta kaddamar da hare-hare (launched) da ta kira shi da sunan zaki mai tasowa (Rising Lion) inda ta nufi wurare 100 a Iran. Harin da ke zama na bazata da wasu hare-haren Isra’ila ta nufi sansanin sojan Iran da wurin aikin makamin nukiliyar kasar da wajen hada makamai masu linzami da wasu cibiyoyi na soja hare-haren da suka yi sanadi na rayukan wasu manyan dakarun da masana kimiya a kasar ta Iran. 

A hare-haren da ke zama na ramuwar gayya (counterstrike), Iran ta harba makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuka wadanda suka afka birnin Tel Aviv da Jerusalam da babban asibitin Beersheba inda Isra’ila ta bayyana cewa kimanin mutane 240 ne suka samu raunika baya ga kadarori da aka lalata.

A lokacin da kasashen biyu ke ci gaba da barin wuta kan juna, labarun karya a shafin X sun yawaita wanda ke nuna yadda Iran ta kai tarin farmaki a kan Isra’ila.

DUBAWA ta gano tarin shafuka na X da ke yada labarai wadanda ba haka suke ba, inda a hannu guda ake dauko hotuna da bidiyo da ake hadawa da fasahar ta AI don isar da sakonni da ke nuna yadda Iran din ta kaiwa Isra’ila hare-hare. 

A wannan rahoto DUBAWA ta nazarci wasu shafuka masu yada labaran karya, don ganin abin da suke yadawa da tasirinsu.

Shafukan bogi na yada labaran AI da ke zama na yaudara

A shafin na  X, DUBAWA ta gano wasu shafuka da ke zama nabogi wadanda suka bayyana kansu a matsayin na hukumomi inda suke amfani da damar wajen yada labarai da hotuna da bidiyo wadanda ke zama na bogi ne da ke nuna yadda Iran ke barin wuta a Isra’ila, daga cikin irin wadannan shafuka akwai “Iran Update” (@hehe_samir), wanda ke da tarin mabiya  227,000. 

Duk da cewa an nuna shafin na bogi ne, da dama mutane sun rika martani wanda ke nuna cewa sun aminta da abin ake wallafawa, abin da ke nuni da cewa akwai karanci na ilimin tantance abubuwa na gaskiya a shafukan sada zumunta, a ko da yaushe abubuwan da mai wannan shafin kan yada labarai ne na karya da aka tsara su don a yaudari al’umma kan hare-haren Iran kan Isra’ila. 

A ranar 18 ga watan Yuni,2025, an yada wani bidiyo (video) da ya nuna babbar motar yaki dauke da manyan makamai da mai da’awar ke cewa shirye-shirye ne na kaiwa Isra’ila hari. 

A cewar mai da’awar “Shiryawa don kai hari a daren nan”, wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla sama da mutum dubu 2 da mutane dubu 19 da suka nuna sha’awarsu da mutane 3000 da suka sake yada bidiyon da 348 masu kafa hujja da shi da 1,900 da suka nuna alama ta cewa za su sake dawowa kan bidiyon a nan gaba.

Ganin yadda aka samu mabanbantan martani a sashin tsokaci inda wasu mutanen ke aza ayar tambaya kan fasahar sadarwa ta Grok wacce taki amincewa cewa wannan bidiyo kirkirarsa aka yi da fasahar ta AI, DUBAWA ta tura bidiyon ga Cantilux don tantancewa, inda sakamakon ya nunar da cewa akwai alamu da ke nuna cewa bidiyon kirkirarsa aka yi ganin yadda wasu alamu da ke nuna cewa an kirkiri bidiyon ne kamar yadda motsi yake wanda ya saba da zahiri alama da ke nuna cewa an kirkiri bidiyon da fasahar AI.

ANALYSIS: X users' deployment of AI to spread false information about the Israel-Iran war Hoton sakamako da aka samu daga Cantilux

A wani bidiyon kuma a wannan shafi a ranar 19 ga watan Yuni,2025 an sake yada wani bidiyon (video) mai tsawon dakika 38 inda ya nuna wani daki da ke zama na gwaje-gwajen kimiya, mai da’awar na cewa wannan bidiyo da ya nuna masanan kimiya sanya da riguna irin na masu bincike suna aiki ne kan makamai masu linzami da zaa yi amfani da su wajen kai farmaki ga Isra’ila.

Da muke gabatar da bincike kan wannan bidiyo mun samu wani bidiyon da shima aka yada shi a shafin TikTok Amir Khan. A bayanan da aka tattara a dangane da wannan shafi yana yada bayanai ne na abubuwan da aka kirkira da fasahar AI wadanda ke zama bidiyo ko hotuna. Wannan bidiyo da aka samar da manufar karya ta nuna yadda Iran ke shiri na yaki, an yada shi a ranar 16 ga watan Yuni,2025 kafin a yada shi a shafin na X.

A tsakiyar watan Yuni, wannan shafi ya sake yada wani bidiyon video, wanda ya samu masu kallo (views,) 529,000 da masu nuna sha’awarsu 15,800 (likes) da wadnda suka sake yadawa su 2,100, wannan bidiyo ya nuna yadda aka samu tashin bama-bamai da ya kona wani gini yayin da hayaki ya tashi sama ya turnike, da aka turawa Cantilux wannan bidiyo ya nuna alamu masu yawa da suka ce bidiyon kirkirarsa aka yi da AI.

Haka kuma DUBAWA ta nazarci asalin bidiyon a wani shafi na TikTok (everythingai97), wanda ke nuna bidiyon da aka hada da fasahar ta AI, wanda sabanin abin da aka wallafa a shafin na X, an wallafa wannan bidiyo a shafin na TikTok tun a watan Mayu, kafin ma yakin ya kazanta tsakanin wadannan kasashe da ake fafata wuta.

ANALYSIS: X users' deployment of AI to spread false information about the Israel-Iran war Hoton sakamako da aka samu daga Cantilux

Wani bidiyon video da wannan shafi ya yada kan yadda aka yi raga-raga da wani yankin na Isra’ila shine dai aka yada a shafin na AI TikTok kamar yadda ake gani anan here.

Da aka zurfafa bincike, DUBAWA ta kara gano wani shafin mai suna (@patriticHun1) a shafin na X wanda ke nuna bayanai wadanda na yaudara ne kan yadda Iran ke lugudan wuta a kan kasar ta Isra’ila wanda shima yana da irin wadancan hotuna da aka wallafa a shafin da aka nazarta a baya, kawo lokacin fitar da wannan rahoto wannan shafi na da mabiya  84,300 (Followers).

.A ranar 14 ga watan Yuni,2025, shafin na @patriticHun1 ya yada wadannan bidiyo guda biyu (here da here) ind suka nuna yadda harin yayi raga-raga da wasu manyan gine-gine duk dai cikin harin na Iran kan Isra’ila. Binciken da muka yi a shafin na google ya tabbatar da cewa wannan bidiyo kirkirarsa aka yi. Wallafar abu guda a ranakun 26 ga watan Mayu da ranar 14 ga Yuli,2025, wannan ya nunar da banbanci ma na lokaci kan abin da mai shafin na X ya wallafa.

Wani shafin ma da ke zama na mai yin kutse,“Iran News daily commentary” (@DailyIranNews) shima ya shiga yakin ta hanyar yada sakonni masu tarin yawa duk da cewa alamu na nuna cewa abubuwan da yake wallafawa basu yi kama da na gaskiya ba.

DUBAWA ta lura cewa wannan shafi na da mabiya sama da 157,000 shi kuma yana bin 3,031, ya dai nuna cewa zamankansa yake don kada a ga cewa gwamnatin Iran ke tafiyar da shi ko ita ke da cewa akansa.

A ranar 17 ga watan Yuni,2025  (@DailyIranNews) ya yada wani hoto da ke nuna wani abu na ci da wuta inda aka sa taken labarin da cewa “Tel Aviv ta kama da wuta”. Wannan hoto ya samu wadanda suka kalla a shafin na X 110,000 inda mutane ke tsokaci bisa amannar cewa hari ne aka kai kan Isra’ila.

Sai dai da aka sanya hoton a Google don gano asalinsa sai ga wani rahoto (report) kan farmaki da aka kai birnin Kyiv na kasar Ukraine wanda ya nuna hoto iri daya da wancan, sannan wata wallafa a shafin X ta sake tabbatar da cewa hoton na da alaka ne da Ukraine.

A wannan rana dai shafin ya sake yada wani hoton (image) da taken “ A hukumance Iran ta kaddamar da hari da ke zama sabo a zagaye na uku (Operation True Promise 3) ana ruwan makaman roka a Tel Aviv da Haifa.”

Sakamakon bincike kan wannan hoto ya nunar da cewa makaman roka ne ake gwajinsu karkashin jagorancin Kim Jong Un a watan Mayu, watanni kafin a fara yakin na Iran da Isra’ila, Wasu kafafan yada labaran kuma sun saki wannan labari kamar a wadannan wurare (here da here).

Shafin X na hudu daga Iran (“From Iran,”) an samar da shi a 2023, yana da mabiya 120,000 wanda ake zargin baya bin wani shafi, shima yana yada labarunsa wadanda basu da inganci a kokari na yada farfaganda kan yakin na Iran, wasu daga cikin abubuwan da shafin kan yada shafin na X ya aza alamar tambaya a kansu kamar yadda za a gani a wadannan wurare (here and here).

Duk wadannan shafukan da wasunsu na yada labarai ne na karya, mutane na daukarsu suna tsokaci suna kara bazuwa daga dubbai zuwa miliyoyi, ganin yadda suke son kara samun masu danna shafukan da sake yada abin da suke wallafawa.

Har ila yau, akwai karin wasu hotunan da bidiyo na fasahar ta AI da ake iya gani a wadannan wurare (here da here da here da here).

Karin wasu karairayin

A lokacin da muke gudanar da bincike, daya daga cikin shafukan da DUBAWA ke bibiya mun lura an sanya masa iyaka, akwai abin da ba a yarda a gani ba, Shima an ga irin wadannan labarai a kansa, dukkanin shafukan hudu suna dauke da tutar kasar Iran a jikinsu.

ANALYSIS: X users' deployment of AI to spread false information about the Israel-Iran war Hoto da ya nuna shafukan guda hudu wadanda DUBAWA tayi bincike a kansu ya zuwa lokacin hada rahoton, hotunan an dauko daga shafin X 

Duk da cewa shafin na X ya sanya alama da ke cewa labaran na karya ne ko yaudara, wadannan shafukan sun ci gaba da yada irin wadannan labarai saboda suna kayatar da masu nuna sha’awa da wadanda ke sake yada irin wannan labarai na yaudara.

Baya ga amfani da AI wadannan shafukan sun ci gaba da yada wasu bayanan da suka sha banban ma da halin da ake ciki a kasar, a wani hoto (image) da aka yada an nunar da yadda aka kama wasu mutane hudu idanunsu rufe kamar dai an tsara za a aiwatar masu da hukuncin kisa, sai aka alakanta hoton da cewa wasu mambobi ne Mossad hukumar leken asirin Isra’ila wadanda aka kama su a Iran bisa zargin zuwa shiga aikin leken asiri. Bayan tantancewa sai aka gano cewa hoton daga wani bangare ne na fim (scene) da aka yi a 1968 ( American Western film Hang’ Em High).

Wani hoton  (image ) shima an yada shi inda aka nuna yadda aka kama wasu masu leken asirin, DUBAWA ta lura cewa babu alaka da halin da ake ciki a dangane da hoton, a shekarar 2016 Iran ta kama sojojin ruwan Amurka kamar yadda sahihan kafafan yada labarai suka ba da rahotanni kamar yadda yake anan (here da here da here).

ANALYSIS: X users' deployment of AI to spread false information about the Israel-Iran war Hoto mara alaka da aka yi amfani da shi don nuna yadda Iran ta kama masu leken asiri daga Isra’ila, inda aka samo hoton shafin X

A wata wallafar ta yaudara (post), mai amfani da shafin ya yada bidiyo da yayi zargin cewa sojoji suka yi taho mu gama da Yahuwa ‘yan kama wuri zauna, inda mazaunan ke kokarin kare sojojin masu kisan yara a birnin Tel Aviv.

“Duk saboda ku ne; wa ya ce ku kai wa Iran hari.”

Sabanin abin da ake fadi gudanar da bincike mai zurfi a Google ya nunar da rahoto da aka tantance (fact-check) a watan Nuwamba 2024, inda yayi da’awar cewa ‘yansandan Isra’ila ne suka tunkari aikin kashe gobara a kudancin titin Ayalon lokacin zanga-zanga da ta barke bayan korar minista Yoav Galant.

Hadarin labaran da ba na gaskiya ba lokacin yaki

A cewar Kunle Adebajo, kwararen masani kan irin labaran da ake jirkitawa bisa wata manufa, kasashe a lokuta da dama suna amfani da labaran da ba na gaskiya ba don neman tallafin  kasashe su goya masu baya a kokarin da suke na kawar da abokan gaba,

Ya kara da cewa “A lokutan yaki bangarorin kan yi amfani da labaran da ba haka suke ba don jan ra’ayin magoya baya da al’ummar gari ko ‘yankasa don su mara baya da ba da tallafi ko ma su ja hankalin abokan hulda na kasa da kasa.” 

Yada irin labaran da ba na gaskiya ba na taimakon masu fadan a nuna suna nasara ya karfafa gwiwar ci gaba da fadan ta hanyar jawo abokansu na kasa da kasa su tallafi kokarinsu da jan hankalin ‘yankasa, su ba da gudunmawa a yakin da ake yi.

Silas Jonathan, manaja kuma kwararen mai bincike kan fasahar sadarwa da kirkirarriyar basirar a cibiyar tattara bayanai da sharhi a kansu ta (Digital Technology, Artificial Intelligence, and Information Disorder Analysis Centre (DIADAC) yace yada labaran da ba haka suke ba, na iya jawo kai ramuwar gayya da jawo rashin samun nutsuwa a cikin al’umma. Ya kara da cewa irin wannan tasirin zai iya ci gaba a zukatan al’umma ko da ma bayan an kammala yakin. 

Ya kammala da cewa “Labaran da ba haka suke ba na iya jawo tsana a tsakanin al’umma, ya sanya mutane su ci gaba da zama da kulli a zukatansu ko da ma bayan yakin ne.” 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »