|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada hoto (screenshot) na da’awar wani me amfani da shafin X wanda ke cewa fasgo na Afurka ta Kudu shi ne mafi karfi a Afurka duk da cewa kudinsa bai kai na Najeriya ba.

Hukunci: KARYA CE. Ya zuwa wannan shekara ta 2025, fasgo na Seychelles shine kan gaba a jerin fasgo mafiya karfi a tsakanin na kasashen Afurka, ana iya shiga kasashe 104 da shi ba tare da biza ba, yayin da shi na Afurka ta Kudu ana iya shiga kasashe 63 ne kawai da shi ba tare da an nemi biza ba.
Cikakken Sako
Hukumar da ke kula da shige da fice ta kasa a Najeriya ta bayyana karin kudin yin fasgo a kasar tun daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025. Fasgo mai shafi 32 wanda zai dauki tsawon shekaru biyar ana yinsa a yanzu 100,000, yayin da mai shafi 64 da zai dauki shekaru 10 ake yinsa a naira 200,000, sabanin N50,000 da N100,000, da ake kowannensu a shekarun baya.
Wannan karin kudade na zuwa ne kusan shekara guda bayan wannan hukuma ta bayyana kari (increased) daga N35,000 zuwa N50,000 ga fasgo mai shafuka 32 wanda zai dauki shekaru biyar, haka nan mai shafuka 64 da zai dauki shekaru 10 aka daga kudinsa daga N70,000 zuwa N100,000.
Da dama ‘yan Najeriya ciki har da jagoran adawa a kasar Peter Obi, ya soki (criticised) karin kudin inda yace wannan zai kara wahalar rayuwa (more burdens) ga ‘yankasar.
Mai amfani da shafin Facebook, Leonardo Medici, ya yada (shared) wannan hoto a shafin Facebook a ranar 1 ga Satumba,2025, inda ya bukaci ‘yanNajeriya da su yada wannan labari a duk inda muhawara ta taso kan batun shige da fice.
A hoton da @felixherbt ya yada a shafin na X ya nuna jerin abubuwan da ake bukata kafin mallakar fasgo na kasa da kasa a Afurka ta Kudu, mai amfani da shafin na X yace fasgo na Afurka ta Kudu shine mafi karfi a tsakanin takwarorinsa na Afurka.
Ya zuwa ranar 8 ga watan Satumba,2025, wannan wallafa ta ja hankali sau 260, akwai wadanda suka yi tsokaci 101 da wadanda suka sake yada labarin sau 21.
DUBAWA ta lura da banbance-banbance na ra’ayin al’umma a sashin tsokaci na wannan wallafa.Wasu daga cikin masu amfani da shafin Facebook sun nuna cewa suna da ja kan bayanan, yayin da wasu suka nuna amincewarsu.
Enwerem Chukwuka, a nasa martani kan wannan da’awa yace “Idan da ace ina da dama da duk wani matashi da ke son barin Najeriya sai na yi masa hanya.”
Michael Joel yace, “kasashe da suke zama matalauta suke gaba a kokari na talauta al’ummarsu.”
A nasa tsokaci Martins Makaja yace, “Afurka ta Kudu ba ita tafi karfin fasgo ba a tsakanin kasashen Afurka.”
Alexander Izu yace, “ bayanansa masu kyau ne amma fasgo na Afurka ta Kudu ba shine mafi karfi ba a Afurka Seychelles ita ke kan gaba sai Mauritius sai kuma na Afurka ta Kudu.”
Ganin yadda ake samun mabanbantan tsokaci kan wannan batu hakan ya sanya DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike kan da’awar.
Tantancewa
Jadawali da ke nuna irin karfin da fasgon kasashe ke da shi a duniya kamar yadda aka samu cikin bayanan International Air Transport Association (IATA), ya sanya (placed) Seychelles a matsayin kasa ta 20 da ke da karfin fasgo a duniya, hakan ya sanya ta zama ja gaba a Afurka.
Kasar ta yi shuhura (reputed) saboda zuwa yawon bude idanu da kyakkyawan yanayinta, don haka masu fasgo nata suna da damar shiga kasashe 104 ba tare da biza ba a fadin duniya, haka nan mai fasgo din kasar na da damar zuwa kasashe 45 da zuwansa a buga masa biza, sannan akwai kasashe 46 da sai an nemi biza an amince kafin mai fasgo din kasar ya kama hanya zuwa kasashen.
Kasar Afurka ta Kudu ita ce ta 49 a duniya tana iya samun shiga kasashe 63 ne kawai ba tare da biza ba, yayin da 88 sai ta nemi biza, jadawalin ya nunar da cewa masu fasgo na Afurka ta Kudu za su iya zuwa kasashe 47, da zarar sun isa a buga masu biza, kasar dai ita ce ta uku a Afurka (mobility score (MS) 110,) tana bin Mauritius (mobility score (MS) 104,) ita kuwa Seychelles (149 MS).
Najeriya kuwa na bukatar biza kafin shiga kasashe 144 yayin da kasashe 27 za su ba wa ‘yan Najeriya biza da zarar sun isa kasashen akasari daga Afurka ta Yamma idan aka duba Najeriyar ga batun ba da biza a lokacin da mai fasgo na kasar zai shiga wasu kasashe ita ce ta 92 a fadin duniya.
Duk da cewa a jadawalin karfin fasgo Najeriya ba ta tabuka komai ba (MS 54), bayanan da aka bayar kan Afurka ta Kudu sun zama na yaudara ga masu amfani da shafukan na sada zumunta.
DUBAWA da ta sake zurfafawa wajen binciken da’awar sai ta gano cewa Aaron Motsoaledi, ministan harkokin cikin gidan Afurka ta Kudu ya bayyana, (announced) karin kudin fasgo a ranar 9 ga watan Oktoba,2022.
ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Nuwamba, 2022 ‘yan kasar ta Afurka ta Kudu da suka kai shekaru 18 za su biya kudin mallakar fasgo daga R600 mai shafi 32, R1,200 mai shafi 48 a baya suna biyan R400 da R800 ne.
Ya zuwa ranar 7 ga watan Satumba,2025, kudin Afurka ta Kudu R600 idan aka mayar da su kudin Najeriya (convert) daidai yake da N51,600 kasancewar Rand na Afurka ta Kudu ana siyar da shi a kan N86. Wannan ya nunar da kudin da ake kashewa a mallaki fasgo na Afurka ta Kudu.
Haka kuma mafi karancin albashi a Afurka ta Kudu R28.79 duk awa daya, a cewar ma’aikatar kwadago ta kasar mafi karancin albashi (minimum wage) ya tsaya ne awa takwas a duk rana, awa 40 a duk mako, don haka ana biya duk wata R4989.88. Idan aka sauya kudin zuwa naira ya zuwa ranar 7 ga Satumba,2025 kudin a hukumance ya kama N431,481.34.
Duk da cewa akwai banbanci a bayanan da aka samu a cikin da’awar, binciken DUBAWA ya tabbatar da kudin da ake caji a Najeriya yayi tsada sosai a kan al’ummar kasar ganin irin kudin da ake bayarwa a matsayin mafi karancin albashi na N70,000 ne.
A Karshe
Bayanan da aka tattara ya nunar da cewa fasgo na Afurka ta Kudu ba shi ne mafi karfi ba, wanda yake kan gaba shine na Seychelles, wanda ake shiga kasashe 104 da shi ba tare da an nemi biza ba.





