African LanguagesHausa

Gaskiya ne! Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta kammala karatu kan kudirin doka da zai hana Sarkin Musulmi damar yin nadi

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X Imran Muhammad, (claimed) yayi da’awar cewa Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta kammala karatu na daya da na biyu kan kudirin doka da ya nemi a cire karfin iko da Sarkin Musulmi ke da shi wajen nada masu zabar sarki da hakimai ba tare da amincewar gwamna ba.

Gaskiya ne! Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta kammala karatu kan kudirin doka da zai hana Sarkin Musulmi damar yin nadi

Hukunci: Gaskiya ne. Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta kammala karatu na daya da na biyu kan kwaskwarima ga tsarin sarautar ta sarkin Musulmi, idan kudirin ya zama doka to babu shakka za a zarewa Sarkin Musulmi karfin iko na nada masu zaben sarki da hakimai ba tare da amincewar gwamna ba.

Cikakken Sakon

Kudirin dokar kwaskwarima ga dokar da ta tanadi masarautar Sokoto, wannan kudiri ya zama babban abin muhawara ganin yadda wannan sarauta ke da muhimmanci a batun masarautu a arewacin Najeriya.  Wani aikin majalisar cikin jihohin arewacin na Najeriya me burin sauyawa da sake tabbatar da mulki irin na sarauta.

Ga misali irin wannan aiki na majalisa a (Kano State’s legislature) a baya-bayan nan ya rushe sabbin masarautu hudu da aka kirkira a 2019 inda aka mayar da babbar masarauta guda. Wadannan masarautu an samar da su a 2019 karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya rage karfin iko na Sarki Muhammadu Sunusi na biyu. Wannan sauyi an kalle shi a mahanga ta siyasa saboda yadda Sarki Sunusi ke cacccakar gwamnati.

Wannan ya sanya an sauke shi  (Sanusi’s dethronement in March 2020.) Sai dai kuma wannan gwamnati ta yanzu karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi watsi da wancan gyara inda ta sake dawo da sarki mai daraja ta daya kuma babban sarkin Kano.

Ana tsaka da haka ne sai kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC da wasu fitattun ‘yan Najeriya suka ja hankali (has raised alarms ) kan kudirin dokar da zai kwaskwarima ga masarautar ta Sokoto inda ake ganin watakila Gwamna Ahmed Aliyu na so ne ya rage darajar sarautar dama watakila ya cire Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III daga kujerarsa. MURIC tayi gargadin cewa wannan yunkuri na iya girgiza yankin dama rage kimar al’ada dama  muhimmancin da wannan sarauta ke da shi a mahanga ta addini.

A wani fannin kuma mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ba da shawara  (advised) cewa gwamnatin ta Sokoto ta ba da kariya ga masarautar ta Sokoto, inda ya nuna muhimmancinta dama irin barazanar da ke tattare da sauken sarkin Musulman.

Shima tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar  ya nun a rashin jin dadinsa (expressed concerns) kan yadda gwamnatocin jiha ke tsoma baki kan harkokin sarauta. Anan sai Atiku ya nemi a yi gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda za a ba da kariya ga masarautun, inda yace suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Da yake mayar da martani kan kalaman na mataimakin shugaban Najeriya Gwamna Ahmed Aliyu  ta bakin sakataren yada labaransa, yayi watsi da da’awar (refuted claims) cewa gwamnatinsa na shiri na cire sarkin Musulmin kamar yadda mataimakin shugaban kasa ke daawa inda yace ya kamata mataimakin shugaban ya rika gudanar da bincike kafin ya furta kalami.Ya jaddada cewa kudirin dokar ba shi da aniya ta rage kimar Sarkin Musulmin amma yana da buri ne na inganta gwamnati da ma samar da dorewar masarautun gargajiyar.

A ranar 25 ga watan Yuni 2024 wani mai amfani da shafin X Imran Muhammad, yayi da’awa (claimed) ya ba da labarin “DA DUMIDUMI: Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta yi karatu na daya da na biyu kan kudirin dokar masarautar Sokoto, idan aka amince da kudirin dokar ya zama doka zai sanya a tube karfin iko da Sarkin Musulmi ke da shi na nada masu zaben sarki da hakimai ba tare da amincewar gwamna ba, baya ga sauran batutuwa.”

Wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla sama da 265,000 (views,) da wadanda suka sake wallafawa 433 (reposts,) da masu kafa hujja  167 (quotes) da nuna sha’awa 1,352 (likes,)  da masu ajiya 131 (bookmarks.) 

Don haka  DUBAWA ya ga muhimmanci na gudanar da bincike kan wannan da’awa.

Tantancewa

Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta kammala karatun kudirin doka na daya da na biyu , wannan shine abin da manyan fitattun kafafan yada labarai irinsu Punch, Tribune, da Vanguard suka wallafa a dangane da kudirin dokar masarautar ta Sokoto kuma asalin yadda aka samo labarin ya fito ne daga wata murya ta atoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Sokoto Nasir Binji.

 A wani sakon da aka nada, bayan zaman majalisar zartarwa a ranar 6 ga watan Yuni 2024, Binji yayi bayani dalla-dalla, ya bayyana cewa kwaskwarimar (amendment ) za ta ba da damar dauke ikon nada masu zaben sarki da hakimai daga hannun Sarkin Musulmi zuwa gwamnan Sokoto sai dai shi Sarkin Musulmi zai ba da shawara kan wadanda za a zaba.

Har ila yau wani sako na manema labarai  (a press release) da ya fita daga shafin sakataren gwamnatin jihar ta Sokoto ya sake tabbatar da haka.

Bayanin ya kara da cewa kudirin da aka samar na da burine ya kara alakanta yadda ake nadin da yadda ake gudanar da harkokin gwamnati ta jihar, ya sake jaddada cewa gwamna shike da iko na nadi a matakin karshe ba Sarkin Musulmi ba.

Akwai dai tarin bayanai da suka tabbata daga rahotannin jaridu wadanda suka bibiyi yadda aka gabatar da kudirin dokar. Rahotannin sun yi bayanai da sharhi daga bayanan da suka fito daga jami’ai na gwamnati wadanda suka jaddada bayanan da suka fita daga Nasir Binji da jawaban da suka fita daga sakon da ake ba wa manema labarai. 

A yadda bayanan muryar suka nunar da ma rahoton da ake bawa manema labarai  sun nunar da cewa kudirin dokar an bayyana shi a matsayin kudirin dokar “kananan hukumomi da masarautu” sabanin kudirin dokar “masarautar Sokoto da za a kwaskware.”

A ranar 6 ga watan Yuni, 2024 Nasir Binji Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihjar ta Sokoto yayi bayani cewa gwamnatin jihar ta Sokoto ta gabatar da kudiri na yin gyara (proposed amending) ga “sashi na 76 na dokar da ta shafi masarautu” ta yadda za ta dace yadda ake gudanar da harkoki na jiha. Wannan bayanan an jiyo shi na magana a jawabi ga manema labarai ( audio clip of him addressing journalists) bayan zaman majalisar zartarwa a wannan rana.Ko da yake wasu jaridun sun bayyana kudirin a matsayin “Kudirin dokar gyara masarautar Sokoto,” amma a zahiri ba haka abin yake ba. 

Saboda haka yadda aka rika bayyana kudirin akwai kuskure amma yadda a majalisar aka gabatar shine daidai.

A Karshe

 Da’awar da ake da ta shafi masarautar ta Sokoto haka take a kan daidai, idan kuma aka amince da ita babu shakka za ta ragewa Sarkin Musulmi karfin iko ta kuma sa gwamnati sai ta amince kafin nada wasu manyan mukamai a masarautar. Kudirin dokar ya wuce karatu na daya da na biyu a majalisar dokokin jihar, abin da ke nuna ana samun ci gaba a kokarin majalisar  na tabbatuwar wannan doka.

An fitar da rahoton  karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 da shirin kwararru na Kwame KariKari  da hadin gwiwar  Garkuwa FM, don dabbaka “gaskiya”a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »