African LanguagesHausa

Hoton bidiyon rikicin ENDSARS ne ake amfani da shi a sunan an kai hari kan motocin Tinubu yayin da ya ke gangamin zabe a jihar Osun

Zargi: Wani bidiyon da jama’a su ka yi ta yadawa na zargin wai wasu sun kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyya mai mulk na APC wato Bola Ahmed Tinubu yayin da ya ke yakin neman zabe a jihar Osun

Hoton bidiyon rikicin ENDSARS ne ake amfani da shi a sunan an kai hari kan motocin Tinubu yayin da ya ke gangamin zabe a jihar Osun

DUBAWA ta gano cewa bidiyon ya fara bulla a shekarar 2020 ne sadda aka yi zanga-zanfar #ENDSARS a jihar Osun, kuma ba shi da wata alaka da ziyarar gangamin da Tinubu ke yi a jihar

Cikakken labari

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu,  ya je yakin neman zabe a Osogbo babban birnin jihar Osun ranar 12 ga watan Yuli dan nuna goyon bayansa ga dan takarar gwamna a jihar, wato gwamna mai ci Adegboyega Oyetola.

Oyetola na neman samun damar yin tazarce a zaben 16 ga watan Yuli.

Jim kadan bayan gangamin, wani bidiyo ya bulla a shafukan soshiyal mediya da zargin wai wasu matasa sun kai hari kan dan takarar da tawagarsa.

Sai dai bayan da muka karanta irin tsokacin da aka yi mun ga ra’ayoyi mabanbanta. A yayin da wasu su ka yi amanna da bidiyon wasu sun yi watsi da shi.

Yayin da zaben na jihar Osun ke karatowa, DUBAWA ta ga yana da mahimmanci a tantance gaskiyar wannan batun domin irin shi ne ke janyo fargaba da ma tashin hankali tsakanin masu zabe

Tantancewa

Binciken kalmomin da muka fara da shi bai nuna mana wani rahoto dangane da batun a kafofin yada labarai masu nagarta ba.

Daga nan DUBAWA ta gudanar da binciken kan bidiyon daki-daki a manhajar gano asalin bidiyoyi ta InVid. Sakamakon binciken ya nuna cewa bidiyon ya bulla a karon farko ne ranar 17 ga watan Oktoba 2020 lokacin gagarumar zanga-zangar nan ta #EndSARS.

An wallafa bidiyon sau da yawa a yanar gizo-gizo. Kafofin yada labarai irin su Channels TV, TVC da AIT Online suna amfani da kanu kamar haka: “‘Yan daba sun kai hari kan gwamnan Osun Gboyega Oyetola yayin da da yake jawabi ga masu zanga-zangar #EndSARS a tashar Olaiya a Osogbo.”

Su ma jaridu masu nagarta irin su Premium Times, Cable, Vanguard da Tribune sun wallafa rahotanni dangane da harin ‘yan daba a kan gwamnan na Osun a 2020.

A lokacin da aka kai wannan harin an sami labarin cewa biyu daga cikin maharan sun hallaka.

Mun tuntubi mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben na Tinubu, Mr Bayo Onanuga sai dai ba dauki wayoyinmu ba kuma bai amsa sakonnin text din da mu ka aika masa a WhatsApp dangane da batun ba.

A Karshe

Bidiyon da ke zargin wai matasa sun kai wa Tinubu hari lokacin gangamin zabe a jihar Osun ba gaskiya ba ne. DUBAWA ta gano cewa a shekarar 2020 ne aka dauki bidiyon lokacin zanga-zangar #EndSARS

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »