Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu hotuna da bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna jirgin mahajjatan kasar Mauritaniya ya yi hadari kan hanyar zuwa Saudiyya

Hukunci: Karya ce. Babu wani jirgi da ya yi hadari, hukumomin kasar sun musanta labarin.
Cikakken Bayani
A ranar Talata 27 ga watan Mayun 2025, wani labari mai dauke da tashin hankali ya karade shafukan sada zumunta, yayin da kasashe duniya ke shirin kammala jigilar alhazzai zuwa kasa mai tsarki domin su yi ibadar aikin hajji, wanda rukuni ne a cikin shika-shikan musulunci guda biyar.
Labarin da wani Muhammad Usman ya wallafa a shafinsa na Facebook na cewa maniyyata aikin hajji su 220 daga kasar Mauritania sun rasa rayukansu sanadiyar hadarin jirgi, kan hanyar zuwa kasar Saudiyya domin yin ibadar hajjin 2025.
Mutane da dama sun rika yada hotuna tare da da’awar cewa jirgin mahajjatan ne ya fadi kuma yake ci da wuta, kamar yadda Dubawa ta zakulo (nan, da nan, da nan, da kuma nan).
Hakama wani bidiyo da wani @SoftWarNews ya wallafa a shafin X da ya nuna lokacin da mahajjata ke kururuwa yayin da jirgin zai yi hatsari.
Zuwa ranar 28 ga watan Mayun 2025, labarin da aka wallafa a Facebook an yada shi (share) sau 51 inda mutum 76 suka yi sharhi (comments).
Ganin yadda labarin ya dauki hankali tare da jefa al’ummar musulmi cikin jimamai, ya sa DUBAWA ta yi bincike domin tabbatar da gaskiyar labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken wasu kalmomin da suka shafi labarin a shafin nema na ‘Google Search’ inda muka lura da cewa babu wata kafar yada labarai mai inganci da ta ruwaito wannan labarin, sai dai mun lura da labarin ya bazu sosai a shafukan sada zumunta.
Mun bincika a shafin yanar gizo na kamfanin jirgin sama na Mauritania, kasancewar bayanai da ke cikin shafin a harshen larabci ne, mun garzaya shafin sada zumunta na Facebook wanda aka dora a matsayin likau a cikin shafin.
DUBAWA ta lura da wata sanarwa da kamfanin sufurin jirage Mauritania Airlines ya wallafa a shafin cikin harshen larabci kuma mun yi kokarin fassara bayanin ta hanyar amfani da manhajar fassara ta ‘Google Translate’.
A cikin sanarwar, kamfanin Mauritania Airlines ya musanta labarin cewa jirgin mahajjatan kasar ya yi hadari.
“Dukkan alhazan kasar Mauritaniya sun isa kasa mai tsarki cikin aminci, kamar yadda aka tsara a ranakun 23, 24 da 25 ga Mayu 2025, a cewar kamfanin.
Daraktan aikin Hajji a ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta kasar Mauritaniya, El Waly Taha, ya musanta labarin hadarin jirgin.
A Karshe
An yi jigilar mahajjatan kasar Mauritaniya sun isa Saudiyya lafiya ba tare da wata matsala ba, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.