African LanguagesHausa

Laberiya ta samu kujera a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Getting your Trinity Audio player ready...

Lokaci ne na farinciki da jin dadi a wannan kasa bayan da aka bayyana wannan sakamako. Shekaru 60 baya da Laberiya ta taba zama mamba wacce ba ta dindin-ba a Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar In 1961, karkshin mulkin tsohon shugaban kasar Laberiya Williams V. S. Tubman wanda yanzu ya rigamu gidan gaskiya a karon farko an zabi Laberiya ta samu kujera a Kwamistin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya.

Mambobin gwamnati da suka hadar da Shugaba Joseph Nyuma Boakai da matarsa, 

(gathered in the conference room of the Ministry of Foreign Affairs) sun hadu don kallon yadda aka kada kuri’a a zaben da ya wakana a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke Amurka.

Wannan taro har ila yau ya hadar da mataimakin shugaban kasa Jeremiah Koung da masu goyon bayan Tempore a majalisar dattawa da Madam Nyonblee Karnga-Lawrence da mambobi na majalisar wakilai da shugabannin ma’aikatu da hukumomi na gwamnati.

Duk wanda ka gani yana sanya da karamar farar riga dauke da tambarin kasar ta Laberiya da rubutu da ke nuna bukatar Laberiya ta samu kujera a kwamitin na MDD “Liberia 4 UNSC.” 

A ranar uku ga watan na Yuni (June 3, 2025), Laberiya ta kasance cikin kasashe biyar da aka zaba a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a karo na biyu tun bayan da aka ganta na karshe a 1961.

Wannan zabe da ake yi duk shekara ta hanyar kada kuri’ar sirri , wadanda za su yi takara ana zabo su ne daga shiya-shiya don neman kujera kuma kasar da ke takara sai ta samu kaso biyu bisa uku na kuri’un 193 da mambobi za su kada a babban taron kafin kaiwa ga nasara.

Idan aka duba wadannan sharuda na nuni da cewa Laberiya na neman kuri’a 129 ne amma abin mamaki sai gashi ta samu rinjaye sosai inda ta samu kuri’u 181 abin da ya haure abin da ma take bukata a zaben.

Hanyar da Laberiya ta kai ga nasarar samun kujerar UNSCS

A karshen watan Satumba (late September), Shugaba Joseph Nyuma Boakai ya kaddamar da kamfe na neman samun kujerar mamba wacce ba ta din-din-din ba a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Lokacin da yake gabatar da jawabinsa yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York, shugaban na Laberiya ya bayyana cewa kasar Laberiya na da karfin fada aji a nahiyar Afurka don haka ta cancanci samun kujerar a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC).

Bayan gabatar da wannan bukata ce sai Shugaba Joseph Nyuma Boakai ya kafa kwamiti na kasa (Steering Committee) wanda ya hadar da ministan shari’a da ministan tsaro da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro da shugabannin matasa dana dalibai, wadanda aka dorawa alhakin ganin sun tabbatar da ganin kasar ta kai ga cimma samun wannan kujera.

Tun bayan kaddamar da wannan fafutuka ce dai ma’aikatar harkokin wajen Laberiya bata zauna ba har sai da ta tabbatar da ganin wannan kasa ta samu wannan kujera.

Ministar harkokin wajen Laberiya, Madam Sara Beysolow Nyanti, ta yi fafutukar ganin ta samu hadin kai na kasashen Afurka don ganin ta cimma nasara, ta ziyarci kasashe da dama na Afurka kai har ma da Mali and Saudi Arabia.  

Me ake nufi da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC)?

The United Nations Security Council (UNSC) Shine kwamiti mafi girma a Majalisar Dinkin Duniya mai fada aji kan sha’anin da ya shafi tabbatar da samun zaman lafiya da tsaro a fadin duniya.

Wannan kwamiti na da mambobi 15 ma’ana daga kasashe 15. Biyar daga cikinsu suna da kujera ta din-din-din da suka hadar da Amurka da kasar Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya su ake kira da P5, sannan akwai wasu wadanda ba mambobi na din-din-din ba su 10.

 Amurka da kasar Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya kowannensu na iya hawa kujerar naki na hana gudanar da wata matsaya. 

Su kuwa wadannan mambobi 10 ana kiransu mambobi ba na din-din-din ba, ana zabarsu ne bayan kowadane shekaru biyu, ba kuma a jere ba, kuma basu da karfi na hana aiwatar da wata matsaya.

Mambobi biyar din wadanda ba na din-din-din ba da aka zaba sabbi sune Bahrain da Kwalambiya da Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango da Latvia da Laberiya, sune za su hade da Denmark da Girka da Pakistan da Panama da Somaliya inda za su zama su 10 cif kenan. 

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da ayyukansa ne ya dakile duk wata barazana ga tsaron kasa da kasa da shiga tsakani da sanya takunkumi da amfani da karfin soja ta hanyar tura dakarun wanzar da zaman lafiya inda ake fama da wata tarzoma.

Me hakan ke nufi ga Laberiya?

Biyo bayan zabar Laberiya a Kwamitin na UNSC, Shugaba Boakai ya jinjina nasarar da kasar ta samu a matsayin bude sabon babi ga Laberiya, za ta shiga a dama da ita kan abubuwan da suka shafi duniya, sadaukarwa ga irin juriya ta al’ummar wannan kasa da hangen da suke da shi a tsakanin kasa da kasa.

Da yake jawabi ga al’ummar kasa (Addressing) bayan samun wannan nasara ta zabar kasar Shugaban na Laberiya yace,”Wannan girmamawa ce da mutuntawa ga kasarmu mai shekaru 178, zabinmu ya nuna irin juriyar Afurka, murna ce ta sake tabbatar da ‘yancin ‘yan Laberiya wadanda suka yi aiki tukuru don samun ‘yanci da gwamnati mai cin  gashin kanta da samun hadin kan al’ummar duniya.”

Shugaba Boakai ya kuma mika godiya da jin dadinsa ga mamabobi na Majalisar Dinkin Duniya ganin yadda suka nuna aminta da cewa Laberiya za ta iya taka rawa a wannan kujera ta Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Da ya juya baya ya halarto sama da shekaru 14 da yakin basasa kasar ta koma tafarkin Dimukuradiyya  Shugaba Joseph Nyuma Boakai, yace wannan ya tabbatar wa kasar cewa an amince da kokarin da ta sa gaba na samun zaman lafiya da sulhuntawa da hadin kai tsakanin kasa da kasa. 

Shugaba Boakai yace, “Sabanin wa’adinmu na wucin gadi a 1961 zabinmu a wannan rana ya ba da sheda cewa ta dukufa a hanyar samar da zaman lafiya da daidaito.” Ya kara da cewa “wannan ya sake tabbatar da cewa Laberiya abar dogaro ce kuma tana da muryar da zaa saurara a mataki na duniya.”

Me Laberiya za ta amfana da samun wannan matsayi?

A matsainta na mamba a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta samu wata kima ta musamman da fada aji a harkoki tsakanin kasa da kasa. Ta samu wata dama ta ba da tata gudunmawa a tsare-tsare na duniya da samun ta cewa kan abin da ya shafi samun zaman lafiya da tsaro da ma harkoki na shugabanci a tsakanin kasa da kasa. 

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya shi ke kula da harkokin aikin wanzar da zaman lafiya a duniya da sa ido kan harkokin siyasa wanda mambobi na da ta cewa. Samun mambar har ila yau zai ba  kasar dama ta tsayawa tsakanin kasa da kasa ta yi mu’amala a tsakaninta da sauran kasashe.

A matsayinta na zama mamba a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Laberiya na da dama ta shiga tattaunawa tsakanin kasa da kasa da warware wasu matsaloli na suka shafi duniya da dabbaka hadin kai tsakanin kasashe.

Ya ‘yan Laberiya ke kallon wannan nasara?

Tun bayan bayyanar sakamakon nasarar da ta kai Laberiya ga samun wannan kujera a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya , al’ummar wannan kasa sun gaza boye irin murnar da suka shiga ciki inda suke ta mika sakon murna ga junansu.

Wannan labari ya samu kambamawa daga bangaren kafafan yada labarai wanda ya zama babban labari a manyan jaridu na kasar, ya zama abun tattaunawa a tsakanin masana a lunguna da sakuna na babban birnin kasar da wajensa.

Liberia wins UN Security Council seat

Wasu daga cikin manyan shafuka na jaridun kasar ta Laberiya

Tsohon shugaban kasar Laberiya George Weah ya rubuta a shafinsa na facebook official Facebook inda ya taya murna ga gwamnatin Laberiya inda yace wannan nasara a wannan lokaci ta kafa tarihi babba ga wannan kasa. 

Tsohon shugaban yace “Lokacin da muka fara wannan tafiya nasarar ta bayyana: Ta karbar gurbin da ya dace da Laberiya a mataki na duniya a kokari na dabbaka zaman lafiya da kwanciyar hankali a idanun duniya. Yanzu da aka cimma wannan nasara na nufin mu ci gaba da aiki tukuru don kasar mu. Ina kira ga kafatanin al’ummar Laberiya su yi amfani da wanan nasara da aka samu mu yi aiki tare don ci gaban kasarmu Laberiya.”

Alexander Cummings, Wanda yayi takarar shugaban kasa a Laberiya sau biyu yace wannan abin alfahari ne da ya kafa tarihi a Laberiya.

Shugaba a jam’iyyar ta Alternative National Congress (ANC) yace a yanzu fiye da kowane lokaci Laberiya ta samu dama ta jagoranci samar da zaman lafiya da tsaro da ci gaba ba kawai ga Laberiya ba har da Afurka da fadin duniya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »