|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
A shekarar 2024, DUBAWA, shafi mafi girma da tasiri wajen tantance sahihancin bayanai a yankin Yammacin Afirka ya taka rawar gani sosai a bannin bacin karuwar da aka samu wajen bullar bayanan da ba daidai ba da ma wadanda aka shirya dan yaudarar jama’a kan batutuwa da dama.
A cikin shekarar, mun yi rahotanni da dama wadanda muka gani a cikin shafukan soshiyal mediya da waje. Mun tantance bayanan da ke da nasaba da siyasa da ma yanain zamantakewar al’ummomi dan kalubalantar ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da ma kafofin yada labarai su nuna sanin ya kamata a kasar.
Wannan rahoton na bitar manyan binciken da DUBAWA ta yi a bara.
- Abokan huldar Rasha sun yi amfani da shafunkan Telegram da TikTok wajen yada bayana da ba daidai ba da ma farfaganda lokacin zanga-zangar#EndBadGovernance a Najeriya
Daya daga cikin manyan binciken da ya fi daukar hankali shi ne labarin da muka yi kan yadda abokan huldar Rasha suka yi amfani da Telegram suka ja ra’ayin jama’a lokacin zanga-zangar nuna adawa da shugabanci mara adalci na #EndBadGovernance, inda ‘yan Najeriya da yawa suka shiga hannun mahukunta a ciki har dakananan yara 32 da wasu 87 saboda daga tutar Rasha lokacin da zanga-zangar ta yi kamari a wasu jihohin yankin arewacin kasar.
Bayan zanga-zangar, wanda adawa ne da tasirin wasu daga cikin manufofin tattalin arzikin da da gwamnatin Tinubu ya kawo, binciken DUBAWA ya bayyana cewa wata kungiya mai suna Africa Initiative, ta bayyana yadda wata kungiya mai suna the Africa Initiative, ta yi amfani da shafukan TikTok da na Telegram wajen yada bayanan da ba daidai ba. Bacin haka sun kuma samu wasu mutane marasa aikin yi wadanda suka taimaka musu wajen yada irin wadannan bayanan. Kamar yadda muka gani a rahoton ofishin kula da harkokin wajen Amurka, babban editan shafin shi ne Artem Sergeyevich Kureyev.
Sai dai an yi sa;a kananan yaran da aka kama lokacin zanga-zangar sun fita daga hannun mahukunta ranar biyar ga watan Nuwamban 2024 a wata kotun tarayya da ke Abuja.
- Wani shafin da ke yayata akidun ‘yan aware,da bayan Rasha wadanda ba daidai ba lokacin zabukan gama gari na 2023 .
Kafin zabukan 2023, inda shugaba Bola Tinubu ya kasance zakara a karkashin inuwar jam’iyyar APC, rahotanni da bincike da daman da aka yi sun gano shafuka wadanda suak yada bayanan da ke yada manufofin Rasha da goyon bayan juyin mulki wanda ya kara ta’azzara rikicin siyasar da aka yi fama da shi a lokacin zaben wanda kuma ya yi tasiri kan tsarin dimokiradiyyar yankin Sahel.
Wanna rikicin ya zo ne a daidai lokacin da aka yi yunkurin juyin mulkin da ya ci tura a kasashen Chadi, Guinea, da Gabon yayin da aka yi nasara a kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar inda har yanzu sun gaza komawa ga mulkin dimokiradiyya ko bayan shekaru uku. Binciken da aka yi dan gano abin da ke zaman makasudin wannan tashen ya nuna cewa Rasha na da hannu saboda irin tasirin da ta ke da shi a kan kasashen Afirka musamman wadanda ke da tarihin mulkin mallaka da kasashen yamman da suke da dadadden tsarin mulkin dimokiradiyya.
Shafin mujallar The IgboTimes ya yi ta wallafa warewar Biafra, da juyin mulki da ma rashin daidato a fuskar siyasa.
Ta yin amfani da manhajar leken asiri na open-source intelligence, DUBAWA ta gano cewa wani Ofoegbu Ejike ya mallaki dandalin da ke yada labaran wadanda ba daidai ba wadanda kuma ke iya tayar da rikici.
Ofoegbu Ejike, mai shafin mujallar IgboTimes Magazine. Tushen hoton: Silas Jonathan/DUBAWA
Kamar dai yadda binciken ya bayyana, Mr Ofoegbu ya taka doka tun da ya harzuka jama’a ta yin amfanin da bayanan da ke yada manufofin Rasha da neman hadasa husumi.
- Jerin bayanai marasa gaskiya wadanda suka yi ta kira da a yi juyin muli a Najeriya.
Mun kuma gudanar da bincike kan sauran kafofin sada zumunta wadanda ke janyo rudani a al’ummar Najeriya suna kira ga ‘yan kasar da su bukaci juyin mulki da da shugabancin sojoji idan har suna so a sami maslaha ga rikice-rikicen da suka addabi ‘yan kasada ma dai duk wani korafin da su ke da shi.
Lokacin da aka gudanar da zanga-zangar #EndBadGovernance mun gano cewa akwai wadanda ke daga waje da ke amfani da kafofin sada zumunta na soshiyal mediya da farfaganda wajen yada manufofinsu.
Binciken DUBAWA ya gano wani shafin X da suna Sissoko Sora Demba (@DelphineSankara) a matsayin daya daga cikin manyan shafukan da ke taka rawar gani wajen yada muggan bayanai dangane da Najeriya tare da manufofin Rasha.
Shafin ya sami mabiya sosai ya kuma yi ta yada bayanan karya dangane da matsalolin tsaron da aka rika samu da ma gazawar gwamnati. Wannan daya daga cikin matakan da aka yi amfani da su wajen ture bayanan da ake adawa da manufofin kasashen yamma a maye gurbinsu da kiraye-kirayen juyin mulki da tallafin Rasha a Afirka.
s a significant player in this disinformation landscape. The account disseminates misleading narratives about Nigeria while promoting pro-Russian sentiments.
Kwararru sun yi gargadin cewa wadannan matakan suna iya dakusar da yunkurin da Najeriya wajen tabbatar da tasirinta a yankin abin da kuma ya ke kara haddasa rikice-rikicen cikin gida da ma dai jaddada mahimmancin samar da bayanan da za su kalubalanci irin wadannan dan kare mutuncin dimokiradiyyar kasar da ‘yancin cin gashin kanta.
- Shekarar Kingibe ta farko a matsayin sanata ta gamu da kalubalen bayanai masu yaudarar jama’a.
Ireti Kingibe ta yi bukin cika shekararta ta farko a matsayin sanatan da ke wakiltar birnin tarayya da lissafa jerin ayyuka 29 da ta ke aiwatarwa wadanda suka hada da gina babbar hanya a Kpaduma, Karu da Gwagwalada, sa’annan kuma da sanya fitillun kan titi a Karamajiji, Mpape, Kwali da Jikwoyi. Bacin haka kuma akwai wani asibiti mai gadaje 50 wanda ake ginawa a Dobi da kuma wani ofishin da shi ma ake ginawa a asibitin koyarwa na jami’ar Abuja da ke Gwagwalada a matsayin wasu daga cikin nasarorinta.
Yayin da DUBAWA Ta gaza tantance wuraren da duk wadannan ayyukan da ta lissafa su ke, uku daga cikin tarar da ta ambata ne kadai aka iya tantancewa. Duk sauran illa ko yaudara ce ko kuma karya. Mun kuma gano cewa wanda ya rike mukamin kafin ita, Philip Aduda ne ya gudanar da biyar daga cikin ayyukan zuwa yanayin da suke a yanzu yayin da na karshen kuma ba’a riga ma an kaddamar da shi ba duk da cewa ita ce ta bukaci da a gudanar da shirin.
- Ambaliyar Maiduguri ko kuma#Maiduguriflood: Tasirin bayanan da ba daidai ba a kan shawo kan rikici.
Wuni hudu kafin ambaliyar ruwan 10 ga watan Satumban 2024 a Maidugurin jihar Borno, sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijani, ya kwantar da zukatun jama’a kan ambaliyar ruwan da aka yi hasashen ya na zuwa, tare da da’awar cewa gwamnatin Babagana Zulum za ta iya shawo kan matsalar ko da ta zo. To sai dai mazaunan da suka gaskata da bayanan gwamnatin sun ji jiki bayan da ambaliyar ta zo saboda wasu sun rasa rayuka da dukiya, wanda ya kai miliyoyi sa’anan da yawa sun rasa matsugunnensu a babban birnin.
Bincikenmu ya bayyana cewa shekarun da aka shafe ana badakala da kudin da ya kamata a ce an yi amfani da shi wajen hana ambaliyar daga faruwa ne ya yi sanadi, sa’annan kuma rashin gaskiyar Mr Bukar ma ya kara kai mutane ga ajalinsu da ma sa su asarar dukiya. Watanni hudu bayan nan, mazauna ba asu gyagije daga abin da ya fari ba, yawancinsu na dogaro ne da tallafi daga al’umma kuma har wa yau wannan wata alamar ce ta illolin da ke tattare da sauyin yanayi.
- Kisar gillar Okuama: Rundunar sojojin Najeriya ta bar al’umma a mawuyacin hali bayan ziyarar wanzar da zaman lafiya
Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da wani “shirin wanzar da zaman lafiya” dan gudanar da bincike kan kisan kiyashin da wadansu wadanda ba’a san ko su wane ne ba suka yi wa wasu sojoji 17 ranar 14 ga watan maris 2024 a jihar Delta. Sai dai yunkurinsu ya gamu da illolin bayanai marasa gaskiya wanda ya kara jefa al’ummar cikin rikicin da ya kai ga kashe-kashe da rashin dukiya.
Bacin da’awar da suka yi na cewa ba ramako ya kai su ba. Bincikenmu ya nuna cewa an rusa gidajen mutane da dama, da makarantu, da wasu karin wuraren da ke da mahimmanci ga rayuwar al’umma a daidai wannan lokacin/
Haka nan kuma, sojojin sun yi yunkurin dora lafin kan al’ummar inda suka yi zargin cewa al’ummar na sane da tashin hankalin da ya afki, wanda suka ce shi ne hujjarsu na yin amfani da karfi wanda ya sa al’ummar ta zama saniyar ware, sadda aka wallafa wannan rahoton. Wannan lamarin dai ya yi tasiri sosai a al’ummar Okuama, abin da ya kara sanya ido kan sanin ya kamatan sojojin Najeriya.
- Tsarin Cocin Christ Embassy ya haifar da rashin yadda dangane da da’awarsu ta warkar da mutane
Cocin Christ Embassy, Cocin da fasto Chris Oyakhilome ya kirkiro, na kokarin wanzar da wani tsarin da ke hana mutane yadda da cututtuka dan nuna imaninsu ko bangaskiyar da suke da shi. Har ma akan sa mambobi kwatanta cututtuka da sunayen da zasu nuna kamar cutar ba ta da kaifin da take da shi a zahiri.
Kafin binciken sirrin da DUBAWA ta yi, wanda ya kirkiro cocin ya ma yi zargin cewa ya tayar da akalla mutane 50 daga matattu lokacin wani bukin waraka da abubuwan al’ajibin da ya yi, inda mutane tara wadanda aka kawoa kwance a kan gadaje dan ba su iya tafiya suka sami waraka bayan da ya umurce su da su tashi daga kan gadon, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya.
Tattaunawar da aka yi da ma’aikatan coci ya nunar da tsarin koyarwarsu wanda ya jaddada mahimmancin kasancewa mai bangaskiya a maimakon amincewa da cuta. Irin shaidar da ake bayarwa da ma abubuwan da suka faru a rayuwar jama’a duk hanyoyin kasuwanci ne irin wadanda ake so a rubuta cikin littafin da ake wallafawa kowane wata mai suna “Rhapsody of Realities” wanda ke kara rufe layin da ke tsakanin bangaskiya na kawarai da bukatu na kasuwanci.
Shi ya sa ma kwararrun ma’aikatan lafiya duk sun yi shakkar tasirin addu’a kadai a kan marasa lafiya ba tare da zuwa asibiti ba, musamman wa cututtuka irinsu kansa. Ganin yadda cocin ta ki yarda ta tattauna wadannan batutuwan da manema labarai ya sanya alamar tambaya kan sahihihancin ikirarin da take yi na cewa ta warkar da marasa lafiya.
- Da’awar gwamnatin Jigawa na cewa ta dakatar da bahayar da ake yi cikin bainar jama’a ba gaskiya ba ne.
Jihar Jigawa ta gaza iya dakile bahayar da ake yi cikin bainar jama’a ya hana ta shiga rukunin jihohin da suka dakile matsalar, bisa bayanin Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, tun watan Oktoban 2022 kuma wannan laifinsu ne. Duk da cewa gwamnatin ta zuba jari sosai wajen gina wuraren bahaya tare da tallafin UNICEF. Al’ummomi da yawa ne ke bahaya a waje a jihar saboda rashin wuaren yi da ma rushewar na gargajiyar da aka gina alokacin damina. A sakamakon haka ne mazauna suka tabbatar da cewa jihar ba ta bin dokokin tsabtar kamar yadda ya kamata.
Bacin fadakarwa da ma sabbin dokokin da aka sa dan tabbatar da tsabta da bahaya a waje, yunkurin gwamnati bai haifar da da mai ido ba. Gidaje da dama har yanzu haka nan suke rayuwa ba su da shedda a gidajensu, musamman a makarantu da asibitoci inda rashin bayin ke tilastawa jama’a zuwa waje. Binciken DUBAWA ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar ta samar da ababen kawai a maimakon buga garwar cewa ta yi amma ba ta yi ba.
9. Maganin Apetamin, wanda ba’a cika sanyawa ido ba na alkawarin karawa mutane kiba a NajeriyaKalubalen sanya ido a kan sassan sassan kiwon lafiya musamman na sarrafa magunguna ya addabi Najeriya . Hukumar NAFDAC wadda ke da nauyin sanya ido kan magunguna da abinci dan tabbatar da ingancinsu ta na yin iya kokarinta wajen tabbatar da cewa sun aiwatar da dokokin yadda ya kamata amma bai yiwuwa kamar yadda ake bukata kamar yadda rahoton ya bayyana dangane da yadda ake sayar da maganin na Apetamin wanda bincike ya nuna cewa magani ne wanda ke dauke da hadarukka da yawa. Binciken DUBAWA ya nuna cewa ana iya sayen magungunan a kusan ko’ina a Najeriya duk da cewa an haba amfani da shi saboda illolin da ya ke iya janyowa.
x