African LanguagesHausa

Sahara Reporters ta yi da’awar cewa Wike ya kauracewa taron majalisar koli wanda  karya ce

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Kafar yada labaran Sahara Reporters ta ba da bayanai (asserted) cewa  Nyesom Wike, ministan babban birnin Najeriya ya kauracewa taron majalisar koli saboda shugabancin Hukumar Zabe mai Zamankanta ta Kasa INEC.

Sahara Reporters ta yi da’awar cewa Wike ya kauracewa taron majalisar koli wanda  karya ce

    Hukunci: Karya ce! Shedu da aka tabbatar sun nunar da cewa ministoci a Najeriya ba mambobi ba ne na majalisar koli, babu kuma wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoto kan halartar ta Wike.

     Cikakken Sako

    A baya bayan nan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada (nominated) Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC), wannan ya bioyo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar Yakubu Mahmood.

    Kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, Shugaba Tinubu ana sa rai ya gabatar da sunan wanda zai karbi wannan kujera zuwa ga majalisa koli don tantancewa da amincewa.

    A lokacin da aka shiga tattaunawa don sanin makomar Amupitan a ranar 9 ga watan Oktoba,2025 kafar yada labarai a kafar sadarwar intanet ta Sahara Reporters ta yi da’awa (claimed) cewa ministan babban birnin Tarayyar Najeriya Nyesom Wike, ya kauracewa taron saboda adawa.

    A cewar rahoton, Shugaba Tinubu da Wike suna takaddama kan batun na zabin sabon shugaban hukumar ta INEC, abin da ya sake fito da yanayi na rashin fahimta da ke tsakaninsu. 

    Majalisar Koli wani zaure ne na shugabannin Najeriya wadanda ke ba da shawara ga shugaban kasa kan wasu muhimman mukamai da ba da umarni ga al’ummar kasa. 

    Ganin irin kimar shugabannin da aka bayyana su ke wajen irin wannan tattaunawa hakan ya sanya DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike kan lamarin don gudun wata matsala.

    Tantancewa

    DUBAWA ya nazarci sashi na Third Schedule (Part 1B) cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 sai ya lura cewa ministoci ba mambobi ba ne na majalisar koli ta kasa. A kundin yayi tanadi na mutanen da suke cikin wannan majalisar koli wadanda suka hadar da: (a) shugaban kasa wanda shine shugaban majalisar (b) mataimakin shugaban kasa wanda ke zama mataimakin shugaban majalisar © Dukkanin tsofaffin shugabannin kasa  da sauransu. A wannan tanadi babu inda aka bayyana sunan ministoci a ciki.

    Da wannan bayani mun ziyarci shafin  X na fadar shugaban kasa mu duba ko akwai wani bayani da aka saki kan wannan batu amma babu abin da muka gano.

    Mun kuma gudanar da bincike ta hanyar amfani da muhimman kalmomi a Google don gano ko akwai wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da wannan labari, sai dai babu wata sheda da aka samu. Babu ma wata kafa da ta ba da labarin ya halarci zaman taron ko kuma bai halarta ba.

    A Karshe

    Binciken da ta DUBAWA ta gudanar kan labarin na Sahara Reporters da ta yi da’awar cewa ministan babban birnin Najeriya Wike ya kauracewa taron majalisar koli saboda nada shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC karya ne, kuma yaudara ce don babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da wannan labari.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button
    Translate »