African LanguagesHausa

Shin da gaske ne mataimakin shugaban Najeriya ya tashi daga gidansa bayan gano an makala masa na’urar CCTV

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X, Biafra_Daily Mirror (@biafra_daily), yayi da’awa  claimed cewa mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya tashi daga gidansa da gwamnati ta bashi na kudi naira miliyan dubu 21 saboda ya gano cewa an makala na’urar CCTV ba tare da saninsa ba.

Shin da gaske ne mataimakin shugaban Najeriya ya tashi daga gidansa bayan gano an makala masa na’urar CCTV

Hukunci: Yaudara ce. Babu wata sheda da ta nuna cewa mataimakin shugaban kasa Shettima ya shiga sabon gidan mataimakin shugaban kasa da aka gyara ballantana a yi maganar cewa ya sake ficewa saboda ya gano an sanya masa na’urar sirri ta CCTV. Rahotanni sun tabbatar da cewa bai ma shiga gidan ba, sannan babu wata sahihiyar kafa da ta tabbatar da wannan labari da ake yadawa.

Cikakken Sako

Gabanin zaben 2027 akwai rade-radi da ke nuna cewa an samu baraka tsakanin Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima

Bayan da gwamnonin APC suka ayyana Tinubu a matsayin dantakararsu na shugaban kasa, rashin bayyana Shettima ya nunar da cewa an shiga yanayi na kila-wakala (he may ko may not be) ko zai yi tafiyar da mataimakinsa ko akasin haka.

Wannan fargaba da ake da ita ta bayyana karara lokacin da aka yi babban taron APC a yankin Arewa maso Gabshin Najeriya taron da aka shiga rudani a yayinsa (summit turned chaotic ) bayan da mataimakin shugaba na shiya daga wannan yanki Mustapha Salihu ya bayyana cewa Tinubu shine dantakarar jam’iyar ba tare da ya hada shi da Shettima ba.

Ana tsaka da wannan fargaba ta siyasa sai wani mai amfani da shafin X Biafra_Daily (@biafra_daily), a ranar 20 ga watan Yuni,2025 ya fitar da wata wallafa posted da hoton mataimakin shugaban kasa  kamar yadda ake gani anan( here) tare da sabon ginin gidan a bayan hoton. A wannan hoto an nunar da tambarin tashar Channels TV ga taken da ke makale a jikin hoton na cewa “ya koma gidansa mallakin kansa bayan da ya gano cewa an makala masa na’urar CCTV ba tare da saninsa ba.”

Sai kuma ya rubuta, “Suna yaudarar kansu.”

Ya zuwa ranar 20 ga watan Yuni,2025 , wannan wallafa ta samu wadanda suka kalleta sama da mutum 200,000 (views), sai masu nuna sha’awa kusan 2,000 (likes) da masu yadawa 100 (shares). Mutane da dama sun shiga tsokaci kan batun wasu na nuna amincewa da abin da aka fada da dama na tsokaci kan mukadan kudade miliyan dubu 21 da aka kashe a kan gidan.

Olufemi Ayodele (@phemidawhiz) ya rubuta cewa, “ me yasa suke sa ido kan yunkurin mataimakin shugaban kasa?”.

Mohammed (@Jammil_Naxx) ya rubuta ne cewa“ wannan abu ne na ci gaba.” 

Flow (@FrankNwadi5) ya rubuta nasa tsokaci da cewa, “miliyan dubu 21 ta tafi an binne ta, sai hakuri Najeriya.”  

Erika (@Smarterikana) ya rubuta cewa, “Yada labaran karya ba zai taimaki wannan fafutuka ba ta neman ‘yanci.”

An yada irin wannan da’awa kamar a nan (here) ta kuma yadu a shafin TikTok da Facebook. Wani mai amfani da shafin na TikTok, @tamarapreyenews, ya yada wannan wallafa the claim ( here) da ta samu masu nuna sha’awa, 4,900 (likes) da masu sake yadawa, 474 (shares), da masu tsokaci 750 (comments). 

Duba da yadda lamarin siyasa ke bukatar taka tsantsan hakan ya sanya DUBAWA ta ga ya dace ta gudanar da bincike kan wannan da’awa.

 Tantancewa

Domin tantance wannan da’awa DUBAWA tayi amfani da wasu kalmomi da wasu jimloli a harshen Inglishi don bincike kamar (“ CCTV a gidan Shettima” “VP Shettima ya fita daga gidansa,” da  “Mataimakin shugaban kasa ya kauracewa gidansa.”

Mun gano babu wata kafa ta cikin gida ko ta kasa da kasa wacce ta ba da labarin cewa mataimakin shugaban kasa ya gano wata na’urar nadar bayanai ta CCTV da aka sanya ba tare da saninsa ba ko kuma ya fice daga gidansa saboda ya gano su. 

Batun hoton tambarin gidan talabijin na Channels TV. 

Domin zurfafa bincike kan hoton da aka yada, DUBAWA ta yi amfani da hanyar binciken gano asalin hoto ta google , sai muka gano wani hoto ne da gidan talabijin din yayi amfani da shi a yada shirye-shiryensa (a broadcast aired by Channels Television) a ranar 7 ga watan Yuli,2024, inda ta dauko rahoto a ranar da aka kaddamar da sabon gidan mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da aka gyara a Abuja. Wasu karin kafafan yada labarai da suka yi rahoton a wannan rana sun hadar da AIT da The Guardian da Premium Times.

A tarihance mataimakin shugaban Najeriya na zaune ne a Akinola Aguda House da ke a fadar shugaban kasa Presidential Complex da ke a Three Arms Zone  Abuja.

A shekarar 2010 gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara aikin katafaren gidan mataimakin shugaban Najeriya da fari an bayyana aikin gyaran zai lakume naira miliyan dubu 7, wannan aiki ya fuskanci watsi da shi da aringizo na kudade da ake ta bayyanawa za a yi amfani da su don wannan aiki.

A cewar rahotanni masu inganci na Premium Times da BusinessDay, an sauya kudin wannan kwantiragi zuwa miliyan dubu 21-22 ya zuwa shekarar 2024.  Wannan gini an kammala tare da kaddamar da shi (commissioned on June 7, 2024.) An rika tunani cewa mataimakin shugaban kasa ba tare da bata lokaci ba zai tare a wannan gida bayan kaddamarwar. 

Sai dai har zuwa watan Fabarairu na 2025 rahotanni (reports) sun nunar da cewa gidan ba a shiga ba, abin da ya jawo tarin tambayoyi da jawo jita-jita a shafukan sada zumunta.

Mun lura cewa ba wannan shine karon farko ba da aka yada irin wannan labari, a watan Maris,2025 wani mai amfani da shafin Facebook Idris Ahmed yayi zargi (alleged) cewa mataimakin shugaban kasa da gangan yaki komawa bisa zargin yadda aka yi ginin an makala wasu na’urori da za a yi amfani da su wajen nadar wasu abubuwa da yake yi. 

Wannan zargin ma ya dora ne a kan wancan, shima dai yana zargi ne cewa an dasa na’urar CCTV a sirrance sai kuma yace Shettima ya shiga gidan sai kuma daga bisani ya fice ya koma gida mallakarsa bayan ya gano abubuwan da aka makala a gidan.

Sai dai bincike da DUBAWA ta gudanar ta gaza gano wata sheda da za ta tabbatar da hakan.

Sabanin abin da ake fadi a watan Fabrairu,2025 rahoto da aka fitar na Daily Trust ya nunar da cewa an samu tsaiko ne a wajen tarewar wasu dalilai na tsaro kasancewar gidan na daga gefe ne ba wai domin an sanya masa na’urar nadar bayanai ba.

Da aka ci gaba da bincike a shafin X na mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Stanley Nkwocha, ya nunar babu inda ya fitar da wata sanarwa ko takardar manema labarai da ta nuna cewa mataimakin shugaban ya fita daga muhallinsa saboda wasu na’urori da aka makala ba tare da saninsa ba.

DUBAWA ta sake nazartar shafin X da aka yi wannan wallafa @biafra_daily, abin da ta lura da shi shine wannan shafi na da alaka da masu fafutukar aware daga Najeriya Biafran separatist sentiments suna yada labarai na nuna kiyayya ga gwamnati da hadin kan kasa, abubuwan da shafin yafi yadawa sun fi alaka da kokarin yada labarai na bangaranci da yada labarai da za su kawo rarrabuwar kai na siyasa da nuna banbancin kabila.

Musamman DUBAWA ta lura (cited) da wani labarin da wannan shafi na  @biafra_daily ya wallafa  posts inda ake nufar wasu hukumomi na kasa abin da zai kawo fargaba da tsoro a tsakanin al’umma a yankin da dama ke fama da rikici.

Wannan tsari na yada labaran da ba haka suke ba, ya kara haskakawa a gane cewa babu sahihanci a abubuwan da mai da’awar ke yadawa.

A Karshe

Da’awa da ke nuna cewa mataimakin shugaban kasa Shettima ya tashi daga gidan da gwamnati ta bashi na kudi miliyan dubu 21 saboda an gano makalallun na’urar CCTV yaudara ce. Shedu da suke a kasa sun tabbatar da cewa har yanzu ma mataimakin shugaban bai tare a gidan ba tun bayan da aka kaddamar da shi a watan Yuni,2024. Hakazalika babu wani rahoto sahihi ko wata sanarwa da ta nuna cewa an sanya na’urar nadar bayanai ba tare da sanin mataimakin shugaban ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »