African LanguagesHausa

Shin da gaske ne ruwan roba na dauke da kananan kwayoyin robar a cikinsa?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wata mai amfani da shafin Instagram tayi da’awa (claims) cewa ruwan roba na kunshe da kananan kwayoyin roba da idanu baya iya ganinsu. 

Shin da gaske ne ruwan roba na dauke da kananan kwayoyin robar a cikinsa?

Hukunci: Gaskiya ne, bincike da dama da aka yi ya tabbatar da cewa ruwan gora ko na roba na dauke da kananan kwayoyin roba da idanu ba zai iya ganinsu ba sai an yi amfani da na’urar microscope. 

Cikakken Bayanin

Microplastics (MPs) wadannan kananan kwayoyin roba, kanana ne sosai kasa da   millimetres biyar. Ana samunsu su daga manyan kwayoyin roba da aka dagargaza ko daga burbushi na robar wadanda ke zama kanana kwarai. 

Masu aikin bincike a ma’aikatar kare muhalli ta Amurka (United States Environmental Protection Agency (EPA) researchers ) sun fassara wadannan kananan kwayoyin roba na (MPs) da cewa kwayoyin halitta ne kanana matuka gaya wadanda girmansu ke tsakanin milimeter (mm) 5 zuwa nanometer (nm) 1. Wadannan kananan kwayoyin roba na MP ana samunsu a cikin abinci ko lemon sha da jikin halittar dan Adam da dabbobi.

Wata mai amfani da shafin Instagram@redapple.life, ta yada (shared) wani bidiyo na  Dr William Lim a kafar yada labaran podcast ta (Mel Robbins Podcast) inda yake da’awar cewa ruwan cikin roba ko ruwan gora na dauke da kananan kwayoyin roba da suke narkewa daga cikin robar su shige cikin ruwan. Mista Lim a bidiyon ya rubuta cewa “Za ka sake tunani akan ruwan cikin roba ko gora bayan kallon wannan bidiyo.” inda ya kafa hujja da wani bincike a kasar Italiya da ya gano kananan kwayoyin roba a cikin jinin mutane.

A cikin bayanan ta nunar da cewa “Ba kawai tsadar ruwan shan na roba ba, ko gora, har ma da irin illa da yake wa jikin dan Adam! Bayan wadannan kananan kwayoyin roba da yawa wadannan ruwa na roba suna kuma dauke da abin da masana kimiya ke kira ORP (oxidative reduction potential) wanda ke iya bude kofa ta haifar ko ta’azarar samun wasu cutika. ”

Sai ta ba da shawarar cewa mutane su guji shan ruwan na roba su zuba jari a tsarin samar da ruwa tsaftatacce a gidajensu, wannan ruwan ne ba shi da sinadaran na ORP (da zai kawar da illar ga jikin dan Adam).

Ganin yadda wannan batu ya shafi lafiyar al’umma, ya sanya DUBAWA ganin bukatar gudanar da bincike.

Tantancewa

Ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi mun gudanar da bincike kan nazarin da Dr.Lim ya bayyana cewa ya gano akwai kwayoyin roba a jikin na dan Adam. Ga dai inda bincikenmu ya kaimu ga wannan makala  da aka wallafa a New England Journal of Medicine (British Heart Foundation da kafa hujja da lokacin nazarin 2024 study

Binciken ya gano ( Polyethylene da polyvinyl chloride da wasu bakin kananan halittu na robar a jikin mara lafiyar. Kuma binciken Radiography da aka yi ya gano cewa wadannan abubuwa da aka gano sun hadar da sinadarin Chlorine.

Binciken ya gano cewa marasa lafiya da aka gano hanyoyin jininsu na dauke da wadannan kwayoyin robobin na (MNPs) suna da saurin kamuwa da cutika da suka shafi zuciya da cutar shanyewar barin jiki koma su mutu bayan watanni 34 da samun cutar idan aka kwatanta da wadanda basa dauke da kwayoyin robar a jininsu. A makalar ta (article by Harvard Health Publishing) ita ma ta kafa hujja da wancan nazari. 

 Mun kuma gano wata makalar da aka rubuta (article by the National Institute of Health) kan robobin da ake samu a cikin ruwan roba.  An kafa hujja da wancan nazari da aka wallafa a ranar 8 ga watan Janairu,2024 a binciken National Academy of Sciences (PNANS). Wannan bincike (This research) ya gano cewa a duk lita guda ta ruwa akwai kananan ‘yanrobobin 240,000. Ya kara da cewa kaso 90% na wadannan ‘yanrobobin kanana masu kankanta ne sosai da ake kiransu nanoplastics. Suma a makalar da suka rubuta  CNN da VeryWell Health sun kafa hujja da wannan nazari.

Wani nazari ma na (“Microplastic particles in human blood and their association with coagulation markers”) ya gano yadda ake samun ‘yanrobobin a cikin jikin dan Adam na da alaka da salon rayuwar mutum da sauyawar sababi na cutukan (PT, APTT, FIB, D-dimer, da FDP wadanda ake amfani da su wajen gwajin yadda jini ke daskarewa ko ma ya toshe hanyoyin da jinin ke bi).

Daga cikin samfur na robobin gwajin jinin da aka dauka daga mutane guda 36 don wannan nazari 32 duk an samu jininsu na kunshe da kwayoyin robobin na MPs. 

Haka kuma a wani binciken (2023 pilot investigation) da aka gudanar kan jijiyoyin jini na wasu mutane ya tabbatar da gano kwayoyin robar na MPs a cikin hanyoyin jinin. Kazalika wani nazarin a 2018 (study) an gano kwayoyin robar da kananansu sosai kaso 93% a robobin ruwa kala daban-daban su 11 da aka dauko daga kasashe 9.

A Karshe

Da’awar cewa ruwan roba na dauke da wasu kwayoyin roba kanana cikinsa gaskiya ce. Nazarce-nazarce da dama da aka gudanar ya tabbatar da cewa ana samun ruwan na roba da wadannan kananan robobi da ido baya iya ganinsu ya danganta da yawansu a kowane ruwan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »