|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani shafin Facebook ya yi sanarwar neman ‘yan uwan wasu yara da suka yi hatsari tare da mahaifiyarsu akan hanyar Abuja.

Hukunci: Yaudara ce! Dubawa ta gano cewa tun 2020 wannan lamarin ya faru ba sabon labari ne ba.
Cikakken Bayani
Shafukan sada zumunta kamar Facebook, na taimaka wa mutane da dama wajen isar da sako ko kuma neman dauki na wani abu da suke neman taimako kamar cigiya, sanarwar tsintuwa da dai sauransu.
Duk da cewa wasu na amfani da wannan damar ta yadda ya dace, akwai lokacin da wasu ke amfani da wannan hanyar wajen yada labarun karya a cikin al’umma.
A ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu, wani shafi mai suna Jaridar Hausa a Facebook ya wallafa hoton wasu yara biyu kowanne da miki akan fuskarsa, tare da sanarwar cewa wasu yaran sun yi hadari tare da mahaifiyarsu akan hanyar Abuja kuma mahaifiyar su ta rasu.
Hoton da aka zakulo a Facebook
Mutane da dama sun yi alhinin wannan abin tare da nuna bakin cikinsu, wasu har neman karin bayani suka yi domin ganin an taimaka an gano ‘yan uwan yaran.
Kamar Labarina Series da ya yi tambaya, “Idan yan uwa ko dangin sun gani wa za su tuntuba kenan?”
Shi kuwa Nasir Almustapha Sheshe cewa ya yi “Hoton nan yau kusan Shekarar sa uku fa. Ku fara bincike kafin ku nemi suna plz”
Zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu wannan labarin da aka wallafa an yada shi fiye da sau 6,500, yayinda aka yi tsokaci sau 274.
Ganin yadda mutane ke nuna shakku akan wanna labarin a cikin akwatin sharhi, Dubawa ta yi bincike domin gano sahihancin labarin.
Tantancewa
Mataki na farko, Dubawa ta saka hoton a cikin shafin bin diddigin hotuna na Google (Google Reverse Image) inda muka gano cewa an fara wallafa hoton ne a ranar 19 ga watan Yunin 2020, hakama an yada shi a Instagram da Facebook da shafin yanar gizo na Nairaland.
Daga tattaunawar da aka rika yi a karkashin shafin @OluwaJayBoss wanda ya fara wallafa labarin, Dubawa ta gano cewa hatsarin ya faru ne kan hanyar Abuja zuwa Lokoja kuma tuni aka gano ‘yan uwansu sama da shekaru hudu da suka gabata.
Tabbacin cewa an mika ‘yaran ga ‘yan uwansu
Fassarar tattaunawar:
@yemi_sexy ke tambaya “yi hakuri idan na takura ka amma wane hali yaran suke ciki, ana kula da su?”
@echethealec ya amsa cewa “ eh, kanwar mahaifiyarsu ta ziyarci yaran, zan je karshen mako domin na duba su, nagode da tambaya.”
Kafin dubawa ta tuntube shafin domin jin majiyar wannan labarin, mun ga ya wallafa sako a cikin akwatin sharhi cewa “Aslm Agarfacemu. Anga iyayensu da jimawa Mungode.” amma duk da haka aka bar hoton ba tare da an cire ba.
Dubawa ta zanta da wani dan jarida kuma ma’aikaci a hukumar sadarwa ta Najeriya Yakubu Musa, wanda ya bayyana cewa irin wadannan shafukan suna wallafa wadannan labarun karya ne don janyo hankalin mutane su rika ziyartar shafinsu da kuma neman mabiya.
“Bugu da kari, akwai rashin kwarewa wajen aikin jarida wadda ke bada damar yin bincike da tuntuba kafin wallafa labari” a cewar Yakubu.
A karshe
Yaudara ce, lamarin ya faru sama da shekaru hudu da suka gabata kuma tuni aka hannunta yaran ga‘yan uwansu.




