|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Umar ma’aikaci ne a wani kanti da ke jihar Kanon Najeriya, inda kop’ina ke cike da kayayyakin da suka sha rana suka kuma yi kura. Bayan da ya kammala makarantar sakandare, aiki da ya kasance kadai a gabansa ke nan. Duk da haka, da kyar ya ke iya samun na sa wa a bakin salati sakamakon tsadar abinci a dalilin hauhawar farashin kayayyakin masarufi, wanda har ya wuce kashir 34.19% banda tashin farashin man fetir da ma dai sauran matsalolin da suka jibanci tattalin arzikin kasar.
A cikin watan Agusta, matsalar tattalin arzikin ta kai kololuwarta har ma ta yi sanadin zanga-zangar da aka yi wa tashen dakatar da gurbataccen shugabanci ko kuma #EndBadGovernance. Kamar dai jama’a da yawa, shi ma Umar ya zaci wata dama ce ta bayyana ga ‘yan Najeriyar su bykaci sauyi mai mahimmanci. “Ni ma ina so in bayyana abubuwan da ke ci mani tuwo a kwarya,” ya bayyana.
Kwanaki hudu da fara zanga-zangar wadda aka fara ranar daya ga watan Agusta, wani abun da ba’a taba tsammani ba ya bayyana – tutocin Rasha suka bayyana a hannuwan masu zanga-zanga a biranen Kano, Jos da Kaduna duka a yankin arewacin Najeriya.
Umar, na daya daga cikin wadanda suka rika daga tutocin, “Na daga tutar,” ya bayyana. A cewarsa wani abokin shi ne ya gayyace shi zuwa wani taro a Hotoro, a Kano, inda aka raba mu su totucin aka ce alama ce ta walwala.
Abokin na sa, wanda aka kama saboda daga tutar, ya dage cewa lallai a wancan lokacin matakin da ya fi dacewa ke nan. Ganin tutocin Rasha lokacin zanga-zanga a yankin yammacin Afirka ba sabon abu ba ne, amma ba’a taba gani ba a Najeriya sai sa’annan. Watanni kadan gabannin juyin mulki a kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, tutocin makamantan wannan sun bayyana kan tituna.
Hoton Umar a gaban shagon da ya saba aiki
Duk da haka, wanda ya fi cin gajiyar wannan lamarin shi ne Sani Abbas, wani infuluwensa dan Kano wanda ke da mabiya sama da 100,000 a shafinsa na TikTok.
“Lokacin zanga-zangar, na sami kudi sosai,” Abbas ya bayyana. Ya fadawa jama’a cewa wata kungiya mai tasha a shafin Telegram da sunan “Africa Initiative” ta biya shi kudi sosai. Shafi Telegram shafi ne da ake amfani da shi sosai a Najeriya inda kusan kashi 54 cikin 100 na al’ummar kasar ke amfani da shi musamman wadanda ke tsakanin shekaru 16 -64 a cewar wani bincike, wanda ma ya nuna cewa daga tsakiyar shekarar 2022, shafin ya taka rawar gani sosai wajen yada tsarawa da yada bayanai musamman a lokutan da ake zanga-zanga.
Abbas ya yada bidiyoyin da ke kira ga Rasha da ta sanya baki kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.
“Mun wallafa hotuna da bidiyoyi dangane da zanga-zanga a tashar sa’annan muka tsinci irin bayanan da za su dauki hankali muka wallafa musamman a shafukan TikTok da Instagram.”
Ya kuma kara da cewa sauran infuluwensas irinsa ma sun sami irin bayanan da ua kamata su wallafa a shafukansu wadanda suka hada da “Putin idan ka yarda ka zo ka ceci Najeriya,” “dakarun sojoji ne amsar Najeriya” sa’annan kuma suka bukace su da su yada irin wadannan labaran a sauran shafukan soshiyal mediya suna amfani da kalmomi kamar #zangazanga da #putin.
Mun bi diddigin shafukan da wadannan bayanan a TikTok kuma bayanan da muka gani sun zo daidai da abubuwan da Sani ya bayyana mana. Mun mayar da hankali ne kan bidiyoyin da aka wallafa a tsakanin ranakun 5 da 11 ga watan Agusta. Tsakanin wannan lokacin kuma mun ga shafuka 38 wadanda suka yada bayanan da ke tura manufofin da ke goyon bayan Rasha da ma juyin mulki. kuna iya ganin shafukan a nan
A wani bangare na shafin Sani a TikTok dauke da bayanan da ke goyon bayan Rasha lokacin zanga-zangar.
Nazarin tashar “Africa Initiative” a Telegram
Lallai shafin Telegram ya zama dandalin yada bayanai marasa gaskiya a Afirka, kuma ba safai ake sanya ido kan abubuwan da ake wallafawa ba shi ya sa yawancin labaran ke yaduwa cikin gaggawa kuma ba wanda ke iya shawo kan su. Tashoshi irin su “African Initiative” sun dade suna yada bayanai irin wadanda ke goyon bayan manufofin Rasha suna kuma kira da a dauki matakin soja kuma wadannan abubuwan babu shakka su ne ke tasiri a kan bayyanar tutocin Rasha a duk sadda ake zanga-zanga. Wannan rashin sanya idon ne ya sa Telegram ya zama babban makami wajen bayyana batutuwa marasa gaskiya musamman wadanda ke tasiri a dandalin kasa da kasa, kuma wannan ya kan shafi siyasa da ma halayyar jama’a wajen yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi siyasa a nahiyar.
Ta yin amfani da Tgstat, wata manhajar Telegram na yin nazari, mun iya samun tashar “Africa Initiative” inda muka gano cewa ya na kwatanta kansa a matsayin “Kamfanin Rasha na dillancin bayanan da ke tashe a nahiyar Afirka.” Tashar na bayanai a harsuna da dama wadanda suka hada da Arabi, Faransanci, Turanci, Portuganci da Spanianci. Haka nan kuma ta na cike da bayanai kan dangantakar Afirka da Rasha tare da goyon baya da yabawa labaran da ke alfahari da juyin mulkin da aka yi a kasahsen Nijar, Burkina Faso da Mali. Tashar na kuma bayyana babban shafinta da wannan adireshin: afrinz.ru.
A Hoton tashar African Initiative a shafin Telegram
Nazarin da muka yi a Tgstat ya bayyana mana cewa an kirkiro tashar a shafin ne a watan Oktoban 2023, kuma a wancan lokacin ya na da mabiya 200. Sai dai zuwa karshen watan Yunin 2024m watanni biyu kafin a fara zanga-zanga a Najeriya, tashar ta samu habbaka sisai inda ta sami mabiya sama da dubu 50. Wannan habakar ta cigaba da kasancewa cikin watannin Yuli da Agusta har zuwa watan Satumba.
Wannan teburin na nuna yadda ‘African Initiative’ ke jan hankalin masu amfani da shafin Telegram zuwa tashar ta. Yawanci ya kan yi amfani da ambatan sauran tashoshi watakila masu alkibla irin na su, yawan wadanda akan ambata a wallafe-wallafen tare da ma yawan mutanen da suka fara bin su a kowane wata na bayyane.
Haka nan kuma wasu bayanan na daban sun nuna cewa a cikin watannin Yuni, da Yuli da Agusta, tashar ta sami karin mabiya sa’annan ta fadada nisan wuraren da dama ta kan sami mabuyan. Sai dai wannan habakar ta ragu sosai cikin watannin Satumba da Oktoba bayan da aka kammala zanga-zanga.
The Wannan hoton na nuna irin karuwan da aka samu lokacin zanga-zangar da kuma yadda ya kasance bayan da aka kammala.
Yawan matsakaicin huldodin da akan samu shi ma ya karu sosai tsakanin watan Yuli da Agusta sadda aka yi zanga-zangar.
Wannan hoton na nuna karuwar da aka samu wajen huldodin irin wanda ba’a cika gani a shafin African Initiative din a tasharsu ta Telegram ba, lokacin da aka gudanar da zanga-zangar.
Sunayen shafukan da ya ke ambatowa wadanda aka fi sani da mentions sun nuna cewa shafin na da alaka da sauran shafukan da ke bin manufofin Rasha a Afirka. Alal misali Hukumar Kula da Harkokin Cikin Gida na Amurka ta bayyana shafukan ‘Smile & Wave’ da ‘Africa Korps’ a matsayin manyan tashoshin Telegram da ke yada ‘munanan’ bayanai irin masu haddasa husumi a nahiyar Afirka.
The Wannan hoton na sama na nuna yadda tashar Africa initiative a Telegram ya kasance daya daga cikin matakan Rasha na yada bayanan da ba daidai ba.
An gano cewa tashar Africa Initiative na yawan wallafa abubuwa dangane da zanga-zanga a lokacin da tutocin Rasha suka bayyana. Akwai sadda ma a cikin daya daga cikin bayanan da aka wallafa a shafin suka yi da’awar cewa “wani binciken da suka gudanar, sun gano wadanda ke bayan zanga-zangar da aka yi a Najeriya, da nufin cewa shugabannin kasashen yamma ne. Labarin ma har ya kara da zargin cewa talauci da matsalolin siyasa duk sun kasance makamai ne a hannun kasashen yamma “wadanda suka kawo mulkin dimokiradiyya.” A wani labarin da suka wallafa ranar bakwai ga watan Agustan 2024, sun kira boren da ake yi “zanga-zangar nuna adawa da gwamnati.”
Hoton wani labari daga tashar dangane da zanga-zangar inda aka kira masu boren “masu adawa da gwamnati.”
Haka nan kuma, a cikin wani labarin shi ma Africa Initiative sun yi amfani da wani mai shafin TikTok wanda ba’a ambaci sunansa ba, wajen wallafa hotunan da bidiyoyin Rasha a shafin X, yayin da shi ma wani “mazauni” wanda ya yi bayanin cewa “zanga-zangar ba ta da wata alaka da Rasha, kuma tutocin da aka yi a gida da ma muradin Rashar da al’ummar ke yi na zuwa ne kawai dan mutane sun gaji da abin da su ke gani kullun.”
Har wa yau a cikin wani labarin na daban, Africa Initiative ta sake karfafa bayanin ta da wani mai amfani da TikTok wanda shi ma ba’a bayyana sunansa ba amma sun ce d son ransa ne ya ke yada bidiyoyi da hotunan Rasha ba wanda ya sa shi. Shi ma sun ce “mazauni” ne.
“Babu wata alamar cewa masu zanga-zangar na da alaka da kungiyoyin da ke da muradin Rasha. Da kansu suka yi tutocin a gida, kuma ba wanda ke cusa mu su ra’ayi da kansu ne suke muradin Rasha.” Suna bayani dangane da bullar tutocin Rasha wajen boren.
Wannan hoton na sama na nuna wabi bayani daga shafin Africa Initiative dangane da zanga-zangar inda suka bayar da hujja da wani “mai amfani da TikTok” da wani “mazauni” suke da’awar cewa muradi ne na al’umma ba wai ana cusa musa ra’ayi ba.
Wajen lokacin da masu boren suka rika daga tutocin Rasha, an gano shafin Rutube na Rasha — wanda ke kama da shafin YouTube din da aka fi sani — cike da bidiyoyin zanga-zangar.
Ga hoton tashar ta Africa Initiative a Rutube channel, makare da bidiyoyin zanga-zangar hade da wasu kuma da aka sami daga shafin TikTok.
Domin samun fahimta mai zurfi kan irin tattaunawar da ake yi cikin tashoshin, mun sauke bayanan chat da multimedia wadanda aka wallafa a nan. Sakamakon bincikenmu ya nuna mana cewa tashar na yada bayanan da ke la’akari da manufofin Rasha dangane da zanga-zangar da ake yi a Najeriya tun ma kafin batun ya bazu a yanar gizo-gizo.
Misali, an wallafa wannan bayanin da ke kasa ranar hudu ga watan Agusta ne, wuni guda kafin tutocin suka fara bayyana kan titunan yankin arewacin Najeriya.
Wannan bayanin da aka dauko daga shafin na nuna hotuna da dama na zanga-zanga a Najeriya musamman inda aka rika daga tutar Rasha.
Hoton bidiyoyi daga tashar Telegram wadanda ke nuna zanga-zanga kamar dai yadda aka gani a shafukan TikTok.
Rawar da Telegram ya taka wajen yada bayanan da ba daidai ba na cigaba da karuwa, musamman a kasashen Afirka, inda ba safai ne kwararru ke sa ido kan sahihancin bayanan da ake wallafawa ba. Irin wannan muhallin zai iya habbaka tare da tallafin shafuka irin su ‘Africa Initiative’ idan har suka yi amfani da irin daburun da suka yi nasara a rikice-rikicen wasu yankunan. A kasahen Mali, da Burkina Faso, alal misali, haka nan aka yi amfani da Telegram wajen yada manufofin Rasha da bukatar mulkin soji yayin da ake nuna Rasha a matsayin kawa wajen yaki da manufofin kasashen yamma, kamar dai yadda ma’aikatar cikin gida na Amurka ta bayyana.
Rashin sanya idon Telegram, da mahimmancin da ya ke baiwa ‘yancin kare sirrin masu amfani da shafin, da ma dai irin goyon bayan da ya ke bai wa manyan tashoshi duk su ne suka ba shi damar kasancewa dandalin yada bayanan da ba daidai ba. Hasali ma wadannan abubuwan ne ke wai wa shafuka irin su ‘Africa Initiative’ damar yada bayanan da ke goyon bayan Rasha, kamar yadda ma’aikatar kula da harkokin cikin gidan Amurka ta lura a kasashen Mali da Burkina Faso. Turjiyar da dandalin ke nunawa wajen bin dokoki na kara sa sarkakiya a yunkurin da ake yi wajen san ya ido da ma dai yin la’akari da irin bayanan da ake wallafawa.
Ranar 25 ga watan Agusta, makwanni biyu bayan da aka kammala zanga-zanga a Najeriya, Pavel Durov, shugaban Telegram, ya shiga hannun ‘yan sanda a tashsr jirgin saman Paris bisa zarginsa da hannu cikin haramtattun ayyuka irin wadanda suka hada da safarar miyagun kwayoyi, zamba cikin aminci, yada hotunan batanci na kananan yara duk a kan shafin na Telegram. Cibiyar Nazari na Afirka ta ce bayan juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso a watan Oktoban 2022, shafukan wasu kungiyoyin da Telegram sun yi hasashen cewa hakan ne zai kasance makomar Nijar nan ba da dadewa ba. Makomar da a yanzu haka aka cimma.
“Hadakar kungiyoyin da ke yada bayanan da ba daidai ba masu alaka da Wagner Group sun yi yunkurin yada jita-jita har sau biyu dangane da juyin mulkin Nijar, har ma da abun da ya yi kama da wata makarkashiyar da aka kulla a kan yanar gizo-gizo wanda ya zo daidai da wata tafiyar da shugaba Bazoum ya yi zuwa kasar waje a watan Fabrairun 2023,” a cewar cibiyar.
Telegram, wanda ake amfani da shi sosai a Najeriya, ya taka rawar gani sosai wajen yada bayanan da ba daidai ba lokacin da aka yi fama da zanga-zanga. Sai dai bayan da aka tuntubi shafin dan tsokaci dangane da rashin sanya idon, babu wanda ya amsa har zuwa lokacin da aka wallafa wannan labarin.
Kwararru sun riga sun bayyana irin hadarin da ke tattare da rashin sanya ido a Telegram, wanda ya ke haddasa yaduwar bayanai masu hadari. Yayin da zai yi wahala a ce an tantance kowanne labari, akwai hujjojin da ke nuna cewa da gangar ne aka yi amfani da Telegram wajen yada bayanan domin suna dan yada farfagandarsu lokacin zanga-zangar wanda ma har ya kai ga aka kama wasu. Akwai abubuwa da dama da shafin ya kunsa wadanda sukan taimaka wajen yada bayanai cikin gaggawa, wanda kuma ya ta’azzara lamarin har ya kai ga kama kananan yara da dama.
Duk da cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ba ta amsa tambayar da muka yi mu ta dangane da irin shirin da ta yi dan tinkarar batun ba, rahotanni na nuna cewa ta na fiskantar kalubale sosai wajen tantance bayanan da ba daidai ba a shafukan irin su Telegram.
Fifikon da Telegram ke bayar wa wajen kare masu amfani da ita ne babban abun da ke kasancewa karfen kafa ga jami’an tsaron. Bacin haka, rundunar ‘Yan sandan ta NPF ba ta wadata na kayayyakin aiki da ma irin kayayakkin gudanar da binciken kwa-kwaf, wanda kuma ya ke kara wahalar gudanar da bincike irin wannan. Hakazalika rashin kwararrun ma’aikata ma na hana su gudanar da aikin yadda ya kamata.
To amma ainihi su wane ne suka kirkiro Africa Initiative?
Ta yin amfani da manhajar Who.is, bayanan da muka samu sun nuna mana cewa a watan Satumban 2023 aka kirkiro shafin na African Initiative, karkashin wata kungiya mai suna “Initsiativa 23,” wanda idan aka fassara da turanci ya ke nufin “Initiative 23” .
Hoton da ke nuna shafin the African Initiative wanda aka kirkiro wanda kuma ke karkashin jagorancin Initiative-23., da Kureyev Artem Sergeyevich, wadda ke zaman kungiyar leken leken asirin Rasha.
Binciken da muka yi a Google wajen gano ma’anar “Initsiativa 23” ya bayyana mana wani rahoto wanda sashen kula da harkokin wajen Amurka ya wallafa inda ya bayyana Artem Sergeyevich Kureyev a matsayin babban editan shafin a yankin Afirka. Haka nan kuma shi ne babban darektan “Initsiativa 23,” kungiyar da ta yi rajistar Africa Initiative a karkashin ta. Wannan rahoton dai ya kara da cewa kungiyar na da rajista da kuma babban ofishi a birnin Mosko. Bacin haka ya na da rassa ko kuma kananan ofisoshi a birnin Ouagadougou na Burkina Daso da Bamako a Maki inda ya kan gudanar da bukukuwa da taruka. Sun ma kwatanta Kureyev a matsayin ma’aikacin FSB ko kuma hukumar leken asirin Rasha.
Shafin na, “African Initiative”na kwatanta kansa a matsayin kamfanin dillancin labaran Rasha mai burin fadada fahimtar juna tsakanin Rasha da Afirka.
“Mu na fadakar da masu sauraronmu a Tasha dangane da irin damammakin da ‘yan Rasha ke da shi a Afirka, dangane da al’ummomin da nahiyar ta kunsa, da ma irin mulkin mallakar da aka yi kasashen Afirka da yadda suka shafe shekaru suna fama da illolinsa, sa’anan da batun ayyukan da sojojinmu ke yi, da ‘yan kasuwa da likotoci da ‘yan jarida duka a nahiyar.”
Tun bayan da zanga-zangar ta gudana, daga turorcin Rashar da aka yi ya yi sanadin mahawarori masu zurfi dangane da mulkin dimokiradiyyar Najeriya. Jamiu Folarin wani malami a sashen Mass Communication da ke jami’ar Crescent a Najeriya ya yi gargadin cea daga tutar Rasha na da babban hatsari ga ikon cin gashin kan Najeriya. “Abun kamar kasashen ketare na tasiri ne a tsarin mulkin dimokiradiyyar Najeriya, wanda zai iya haddasa rashin daidaito,” a cewarsa.
Damuwar da Mr Folarin ke da shi ya wuce abin da ya faru a zanga-zanga. Ya yi misali da kusancin da Najeriya ke da shi da Nijar, inda rikici irin wannan ya kai ga juyin mulki. “Mai yiwuwa ‘yan Nijar din da ke rayuwa a yankin arewacin Najeriya ne suka yi tasiri a kan ‘yan uwansu,” ya kara da cewa hakan na haddasa fargabar cewa kimar Rasha da tasirinta na kuruwa a yankin Afirka kuma hakan na iya haddasa rikici a yankin.
Yadda wadansu bangarorin ke ganin labarin
Wannan bayanin dai ya gamsar da wasu daga cikin wadanda suka ji. A Jos, Mustapha wani tsohon mai sayar da kabeji shi ma ya daga tutar wanda a tunaninsa alama ce ta nuna karfi.
“Mallam Tafida ya fada mana cewa daga tutar na nufin juyin mulki,” a cewar Mustapha. Ganin yadda ya ke cikin kunci bayan da ya rasa sana’arsa sakamakon hauhawar farashin kayayyakin masarufi, labarin samun sauyi ne ya ja ra’ayinsa. A cewarsa ma ya tuna sadda ya taba ganin shugaban kasa a gaban wata tuta makamanciyar irin wannan wanda ya kara karfafa ra’ayinsa kan cewa alama ce ta karfi da iko, ba wai tasirin kasashen ketare ba..
Tutar da aka kewaye da ja, wanda ke kusa da Tinubu ne Mustapha ke nufi.
To amma abun da ya ke a zahiri ya banbanta. Malam Tafida, dan kasuwa a Abuja ne ya yi ta raba tutocin Rasha a Jos sai dai bayan da rikicin ya barke a na nemi shi an rasa.
Hotunan guda biyu du a wuri daya aka dauka, wato a birnin Jos, a Old Airport Road inda aka yi amfani da tutocin Rashar har ma rikicin ya yi zafi. An dauki hoton farkon ne sadda ake cikin yin zanga-zangar yayin da na biyun shi kuma aka dauka bayan da aka kamala.
Da zanga-zangar ta bazu, Saleh, wani mai amfani da TikTok daga Kaduna, a fili ya fito ya bayyana cewa ya na goyon bayan juyin mulki, duk da cewa an kama wasu daga cikin abokanansa wadanda suka yi amfani da tutocin Rashar.
“Mun nemi kananan yara ne suka rika daga tutocin,” Saleh ya bayyana, ya na karin bayani kan yadda ya rika rabawa kananan yaran da suka rika jin yunwa burodi a Zaria, musamman a Kwangila, dan dai jan ra’ayinsu su shiga zanga-zangar a dama da su. Yawancin wadannan yaran ba su ma san abun da tutar ke nufi ba, su dai kawai suna neman abin sa wa a baki ne. Mun kai ziyara wurin inda muka zanta da wasu daga cikin yaran da suka tabbatar mana cewa sun shiga an dama da su. Tun watan Agusta aka kama yaran kuma ba su suka je kotu ba sai watan Nuwanba, inda suka bayyana a gajiye kuma cikin matsananciyar yunwa. Yayin da ake shari’ar, wasu daga cikinsu sai da suka suma saboda tsananin gajiya, abun da ya kara tabbatar da jita-jitar cewa an rika wulakanta su sadda su ke kulle.
A sunan martanin da aka maida ga kiraye-kirayen al’umma da kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil adama, shuga Bola Tinubu ya umurci da aka sako yaran kanana guda 29 wadanda suke fiskantar hukuncin kissa sakamakon rawar da ake zargin sun taka lokacin zanga-zangar.
To amma yanzu mai zai faru da manhajar Telegram ita da ta jagoranci wannan batun? Domin tinkarar matsalolin da ke kalubalantar yunkurin aiwatar da dokar miyagun laifukan yanar gizo a Najeriya musamman wajen rawar da kafofi irinsu Telegram ke takawa a yada bayanan da ba daidai ba, dole ne a fahimci wadansu muhimman matsalolin da suka shafi dokoki da fasaha. Barrister Saminu Mohammed ya yi bayanin cewa dabarun sakaya bayanai na Telegram masu karfi sosai da kuma rashin sa ido kan abubuwan da ake wallafawa a shafinsu ne ke kasancewa babban kalubale ga mahukunta wajen sa ido su gano ayyukan da ake aiwatarwa tare da mugun nufi. Haka nan kuma, tashoshin dandalin na wajen Najeriya ne dan haka a wasu lokutan dokokin Najeriya ba za su iya aiki a kansu ba.
“Makasudin dokar yaki da aikata miyagun laifuka a yanar gizo shi ne kariya da kuma hukunta duk wadanda aka kama da aikata miyagun laifukan, a ciki har da yada bayanan da ba daidai ba. To sai dai dokar ba ta iya aiki yadda ya kamata mmusamman a kan dandalolin da suka dauki matakan kariya na musamman da kuma wadanda tashoshinsu ke bin dokokin ketare. Akwai bukatar hadin kai a matakin kasa da kasa domin sake inganta dokokin da suka shafi yanar gizon ta yadda za su shawo kan irin wadannan matsalolin na wannan zamanin sadarwar,” a cewar Baristan.
Wannan daya daga cikin hotunan da aka dauka a Kwangila a zaria ke nan yayin da kananan yaran ke karbar kudi nera hamsin hamsin dan su je su aikata abin da aka sa su yi.
Da muka tuntubi ‘yan sanda su yi mana bayani dangane da tsare yawan, Muyiwa Adejobi, mai magana da yawun ‘yansandan na NPF, ya tabbatar cewa lallai, “masu shirya” zanga-zangar ne suka bukaci yaran su rika daukar tutocin.
“Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi gargadi kan amfani da tutocin ketare lokacin zanga-zangar da ma kiraye-kirayen juyin mulki, abin da muka kira cin amanar kasa, bisa tanadin dokokin Najeriya,” ya ce.
Da aka tambaye shi ko an kama wasu daga cikin wadanda suka rika amfani da tutocin, mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce “Mun kama fiye da 90 a cikin wadana daka gansu da tutocin.”
Har yanzu dai ba’a kai ga kama wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar ba. Akalla bayanin da jami’an tsaro daga sojoji da ‘yan sanda da sauransu suka bayar ke nan sadda suka yi wata sanarwa ta hadin gwiwa suna zargin wasu wadanda suka dauki nauyin rikicin amma ba’a san ko su wane ne ba da yunkurin hambarar da gwamnati ba tare da bayar da hujjoji ba.
“Har yanzu ba mu san wadanda suka dauki nauyin wannan shirin ba,” jami’an tsaro suka bayyana sadda suka gana da manema labarai. Sai dai, sun tantance cewa wadanda ke yunkurin kalubalantar gwamnati za su gamu da mummunar makoma.
Lauya, Saminu Mohammed ya bayyana sarkakiyar da lamarin ke da shi. Yayin da daga tuta kamar yadda suka yi keta doka ne musamman a zanga-zanga irin wannan – inda mahalarta ke kira da a yi juyin mulki — cin amana ce bisa tanadin dokokin Najeriyaa
Sashi na 410 na dokar Najeriya na la’akari da abubuwan da za su iya kasancewa kalubale ga shugaban kasa wajen gudanar da ayyukansa a matsayin cin amanar kasa wanda ke dauke da hukuncin kisa. Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan Mansir Hassan ya yi bayani dangane da lamarin Kaduna: ya ce mutane 39 aka kama a Kaduna, a ciki har da telan da “ya rika dinka tutocin da aka yi amfani da su.” an kwace tutocin Rasha kusan 40 da na China guda daya, ya bayyana.
Yayin da a jihar Kano, mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce a nan ne aka kama mafi yawan mutanen. Hasali ma sai da hedikwatar ‘yan sandan ta mayar da kotun majistiret din can, kuma a nan ne ma ake gudanar da shari’ar. Haka nan ma ko a Kanon an cafke telolin da suka rike dinka “tutocin Rashar.”
Ya kuma kara da cewa ana cigaba da gudanar da binciken gano wadanda suka “dauki nauyinsu.”
“A hedikwatar ‘yan sandan Kano yanzu, kuna iya ganin wadanda aka kama suna fiskantar shari’a. Dan haka ba ajiye su mu ke yi na wani tsawon lokaci ba,” ya tabbatar
Maxime Koami Domegni, kwararriya kan bunkasa kafofin yada labarai kuma Editan GIJN na yankin Afirkar da ke amfani da harshen faransanci, ya dade yana labarai dangane harkokin Rasha da juyin mulki a Afirka. Ya nuna cewa matsaloli kamar dadewa a kujerar mulki da ma rike iko ko ta halin kaka da rashin tsaro duk sun taru sun kara karfin tasirin kasashen waje a kan nahiyar Afirka.
“Sabbin mahukuntan, su kan zo da alkawura da harkokin da suka shafi kishin kasa ko kuma kishin Afirka, a matsayin wadanda za su ceci mutane. Ko da shi ke, mun fara ganin abubuwan da ke faruwa a zahiri, domin da kyar ake gane cigaba na gari, sa’anan kuma muryoyin da ke bayanin ya kamata ana yawan danne su ko kuma a tilasta kusu gudun hijira.”
Da aka tambaye shi kan wadanda ke daukar nauyin ire-iren wadannan abubuwan, Mr. Domegni ya ce zai yi wahala a gano wadanda ke da hannu idan ba wai bincike mai zurfi ne aka gudanar ba. “Ya na iya yiwuwa cewa wadanda ke da abin samu ne daga rikicin suke sa hannu wajen baza tutocin a Najeriya, hatta jami’an diflomasiyyan Rasha da sauran kasashen da ta ke ma’amala da su a yankin.”
Ya kuma kara da cewa zai ma iya kasancewa ‘yan kasar ne kawai suke gudanar da zanga-zangar ba lallai wai akwai wanda ke daukar nauyinsu ba, illa dai suna jin dadin bayanin cewa kulla kawance da Rasha zai fi inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
“Abu daya ne tabbas: shekaru biyu ko uku da suka gabata, kasashen yammacin Afirka kalulan ne za su iya danganta kansu da tutar Rasha, amma yanzu muna ganin masu zanga-zanga a kasashen Mali, Nijar, Burkina Faso, da ma wasu wurare suna nuna tutocin a kai-a kai.”
An yi rade-radin cewa za’a sake gudanar da wata zanga-zangar ranar daya ga watan Oktoba, ranar samun ‘yancin kan Najeriya, sai dai ranar ta zo ta tafi ba tare da an yi ba, harkokin da aka yi ma ba su kai yawan wadanda aka yi a watan Agusta.
Bacin hakan, ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ya karyata zargin cewa ta na da hannu, cikin wata sanarwa a shafinsu, inda ta yi bayani kamar haka, “Gwamnatin tarayyar Rasha, da duk jami’anta, ba su da hannu cikin wadannan harkokin kuma ko daya ba mu shirya su ba,” lokacin wani bayanin da suka yi a talibijin.





