Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Gwamnan jihar Adamawa ya sauke Atiku Abubakar daga sarautar Wazirin Adamawa

Hukunci: Yaudara ce! Gwamnan jihar Adamawa bai sauke Atiku ba, kamar yadda sakataren yada labarai na gwamnan ya bayyana.
Cikakken Bayani
Ana ci gaba da cece-kuce tun bayan da gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya sanya hannu kan dokar masarautun jihar, wacce ta ba da ikon ƙirƙirar sabbin gundumomi 84.
Yayin da ake ci gaba da muhawara, wani labarin dake cewa gwamnan ya sauke Atiku Abubakar, madugun adawa a Najeriya daga saurautar Wazirin Adamawa ya karade shafukan sada zumunta har ma da wasu jaridun da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, kamar yadda muka zakulo a nan, da nan da kuma nan.
Zuwa ranar Jumu’a 21 ga watan Fabrairun 2025, labarin da aka wallafa a shafin Media Adverts mutane kusan 500 ne suka yi tsokaci akai yayinda mutane 71 suka yada labarin.
Kasancewa Atiku Abubakar sanannen mutum kuma dan siyasa a Najeriya, labarin sauke shi daga sarauta zai yi matukar shafuwar kimarsa, akan haka ne Dubawa ta yi bincike kan wannan labarin domin tantance sahihancinsa.
Tantancewa
A farkon watan Janairun 2025, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya nada sarakuna a sabbin masarautun da ya kafa da suka hada da Sarkin Fufore, Sarkin Huba, Sarkin Michika, Sarkin Madagali, Sarkin Gombi, Sarkin Maiha da Sarkin Yungur.
A cewar DW Hausa, wasu sun danganta lamarin da siyasa saboda kalaman da ake zargin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yi a lokacin gangamin yakin neman zabe a shekara ta 2019 cewa “za mu fasa kwarya”.
A nata ɓangare gwamnatin jihar Adamawan ta ce abin da majalisar ta yi na ƙirƙirar sabbin masarautun zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tsarin shugabanci da al’adun gargajiya a faɗin jihar.
Dubawa ta gano cewa a cikin wani jawabi ne da gwamnan ya yi a wurin bukin nadin sabon Sarkin Madagali da aka yi a ranar Laraba 19 ga watan Fabrairun 2025, aka zakulo wannan jawabin da ake yaɗawa.
Dangane da labarin cewa an sauke Atiku a matsayin Wazirin Adamawa, sakataren yada labarai na gwamnatin jihar Adamawa, Humwashi Wonosikou ya musanta labarin, yana mai cewa an yi wa kalaman gwamnan mummunar fahimta, cewar da ake yu Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sauke dukkanin Hakimai da masu rike da sarautu ciki har da Wazirin Adamawa Atiku Abubakar.
A cewarsa, Gwamnan ya umurci Hakimai dake masarautun da abin ya shafa da su je su yi mubayi’a ga sabbin sarakunan da aka nada, domin a sake nada su.
Haka kuma gwamnan ya umurci duk sarakunan da hakimai da su nemi amincewar gwamnatin jiha kafin aiwatar da wasu sabbin nadin sarautun na gargajiya.
Dubawa ta tuntubi wani dan jarida a jihar Adamawa, Umar Ibrahim wanda ya yi karin haske abinda gwamnan ke nufi, a cewarsa umurnin ya shafe hakimai ne kawai ba da sarakuna masu daraja ta daya ba.
“sabanin yadda mutane suka rika yadawa gwamnan yana magana ne kawai da hakimai wadanda suka yi nadin sarautu a karkashinsu” Inji dan jaridan.
A Karshe
Yaudara ce. Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Adamawa ya yi karin haske kan kalaman gwamnan da aka fahimta ba dai-dai ba, kuma wani dan jarida ya tabbatar wa Dubawa cewa umurnin gwamnan ya shafi hakimai ne kawai.