|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bayanin da aka wallafa a Facebook na da’awar cewa NNPC ya sanar da wani sabon wurin sayen man fetur din a kan farashin N200

Hukunci: Yaudara ce! Sabanin wannan da’awar, mai magana da yawun NNPC ya yi karyata wannan zargin. Bacin haka ma babu wata kafar yada labarai mai nagartar da ta wallafa wannan labarin.
Cikakken bayani
Ba da dadewan nan ba ne kamfanin an fetur na NNPC a Najeriya ta sanar cewa za ta iya tabbatar da dorewar samar da man fetur a kan kari kuma cikin wadata a duk fadin Najeriya, tare da bayyana damuwarta kan matsalar kudi.
Yayin da ake cikin haka ne kuma, Najeriya ta sake fadawa wani sabon yanayin na rikicin karancin man fetur, inda har ma tashoshin man fetur suka ruge kofofinsu ga masu motoci da ma sauran ma’aikatan da ke bukatar man fetur din a kan farashi mai
Ranar biyar ga watan Satumba, wani shafin da ake amfani da Facebook, Kegit.ng Hausa ya wallafa wani labarin da ke cewa NNPC, wato kamfanin man kasa, ya fara sayar da man a kan farashin N200 kowane lita yayin da sauran masu sayar da man ke kokuwar sa shi a kan farashin da zai sami karbuwa a wajen masu sayen man.
A cewar bayanin, “NNPC ya bayyana sabon tashar da ya ke sayar da man a kan farashin N200.”
Ya zuwa ranar Asabar 14 ga watan Satumba, labarin ya sami ziyara sama da 5, 000, an yi tsokaci sama da dubu daya sa’annan an sake rabawa sau 123.
Da DUBAWA ta yi kokarin tantance sahihancin sakon, ta lura cewa akwai wadanda suka yi amanna, yayin da wasu kuma suka yi shakkar afkuwar hakan.
Da ya ke mayar da martani, Joekings Vibes, cewa ya yi: “Ina jinjinawa NNPC da ya dauki wannan babban matakin.”
Shi kuma da ya ke bayyana takaicinsa, DC Nation, cewa ya yi: “Najeriya kasa ce da ke bukatar kubuta daga hannun miyagi.”
Wani shi ma mai amfani da shafin, Oluseyi Ayoola, ya kara da cewa: “Ku tantance irin man da ake saidawa, ka da ku ce mai kawai. CNG ba man da aka saba amfani da shi yau da kullun din da yawancinmu suka fi sani ba ne.”
“Wannan shafin na Legit, bai cika daukan labaran gaskiya ba,” a cewar Udo Kwu
DUBAWA, ta lura da mahawarar da ake yi kan wannan da’awar kuma ta yanke shawarar gano gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta duba binciken kasuwanni da nazarin kafofin yada labarai dangane da batun. Muna iya tabbatar mu ku cewa tun uku ga watan Satumba, farashin man fetur ke kan N879 zuwa sama kan kowace lita.
Jaridun Premium Times da Vanguard duk sun rawaito wannan larin farashin da aka samu.
Haka nan kuma mun tuntubi Femi Shoneye, Babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, wanda ya fadawa DUBAWA cewa ta yi watsi da wannan da’awar domin karya ce kawai.
Ya ce: “Wannan ba gaskiya ba ne. Kasuwanni ne ke tabbatar da farashin man fetur ba NNPC ko gwamnati ba. Kasuwa ce wadda hada-hadar kasuwani ne ke tasiri kan farashin da ake saida man.”
“Darajar musayar kudi ma na taka muhimmiyar rawa. A NNPC muna iya kokarin mu wajen ganin cewa Najeriya ta sami farashi mai adalci, kuma muna tattaunawa da Dangote dangane da farashin,” ya bayyana.
Bacin haka ma babu wata kafar yada labarai mai sahihancin da ta wallafa labari kan ragi a farashin man fetur.
A Karshe
Binciken DUBAWA na nuna cewa NNPC bai rage farashin man fetur zuwa N200 kowace lita ba kuma ma bai sanar wa jama’a cewa ya bude wata tashar da za’a iya zuwa a sayi man ba dan haka, wannan da’awar yaudara ce kawai.




