African LanguagesHausa

Yaya gaskiyar batun cewa yawan shan magungunan sanya tazarar haihuwa na janyo ƙarin mahaifa ko kuma fibroids

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: wani mai amfani da shafin X @Ne0_officiall  na da’awar cewa yawan shan magungunan takaitawa ko kuma sa tazarar haihuwa na iya sanadin cutar fibroids ko kuma karin da ke fitowa a mahaifa.

Yaya gaskiyar batun cewa yawan shan magungunan sanya tazarar haihuwa na janyo ƙarin mahaifa ko kuma fibroids

Hukunci: Babu isashen hujja! Babu isashen hujjar da ke da alaka da binciken kimiyyar da ya goyi bayan wannan da’awar. Kadan daga cikin binciken da muka gani na da’awar cewa kwayoyin na iya kara hadarin samun cutar, yayin da wasu kuma suka ce magungunan na iya rage hadarin kamuwa da cutar.

Cikakken bayani

Ƙarin mahaifa babban abun damuwa ne a fannin kiwon lafiya musamman tsakanin mata a Najeriya. Bincike na nuna yadda ake samun bayyanar cutar a yankunan Najeriya daban-daban,  inda ake samun kashi show varying prevalence rates across 14.2% cikin 100 a yankin Ogoni, jihar Rivers, Kashi 6.83% a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, da kuma mafi yawa kashi 48 cikin 100 tsakanin matan da ba su san namiji ba birnin Ibadan

Binciken  na kuma nuna cewa an fi samun fibroids din ne tsakanin matan da ke da shekaru 26 zuwa 45, kuma yanayin ma ya kan karu yayin da shekaru suka karu. Bacin yawan wadannan alkaluman, bayanan da ba daidai ba dangane da abin da ke janyi shi da ma abubuwan da ke kara hadarin kamuwa da shi na cigaba da yaduwa a kafofin sada zumunta na soshiyal mediya.

Kwanan nan wani mai amfani da shafin X, @Neo_officiall, ya yi zargin cewa yawan amfani da magungunan da ake sha dan sa tazarar haihuwa na iya janyo karin cikin. 

Tun 2 ga watan Maris , 2025 aka wallafa bayanin kuma mutane 139,500 views, sun yi ma’amala da shi sa’annan an tsokaci  63, an raba shi sau 245 reposts, an kuma adana sau 122.

Ganin yadda cutar ta yi kamari a tsakanin mata da ma yadda labarin ya bazu da sauri ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin gudanar da wannan binciken.

Tantancewa

Ƙarin mahaifa tsuro ne wadanda ke fitowa a mahaifar mace amma kuma yawanci ba su da wani lahani kamar cutar daji. Girmansu ya banbanta kuma sinadaran jikin mutun na tasiri a kan su. Wadannan sinadaren, musamman wadanda ake kira da turanci  estrogen and progesterone sun fi tasiri. Sai dai yayin da tsuron ke kasancewa wani abun da aka saba gani, ba’a san ko ainihin abin da ke janyo shi ba.

Ba dukansu ne ke zuwa da  alamu ba, amma idan har suka zo da su, kadan daga cikinsu sun hada da jini mai yawan gaske a lokacin haila, ciwon baya, yawan zuwa fitsari, da jin zafi sadda ake jima’i. Yawanci akan same shi ne a matan da suka kai shekarun haihuwa.

Bincike na nuna cewa karin kan girma ne sosai a duk sadda sinadaran jikin mutun suka karu (misali sadda ake dauke da juna biyu) sa’annan sukan kuma ragu sadda sinadaran suka ragu (Kamar lokacin da mace ta kai shekarun daina haihuwa baki daya)

 Binciken kimiya ko kuma na asibiti na cigaba da binciken musababbabin cutar da ma magungunan da za su fi aiki. Sai dai har yanzu abin da aka kai ga ganowa shi ne sinadaran nan biyu wadanda aka ambato da farko ne ke janyo shi. Magungunan takaita haihuwa na kunshe da duka sinadaran biyu.

Bisa bayanan shafin kiwon lafiya na Mayo Clinic, akwai abubuwa da dama da za su iya kara hadarin kamuwa da cutar. Wadannan sun hada da kiba, girman jiki, tarihin cutar a iyali, rashin haihuwa, samun jinin wata-wata da wuri (Ko kuma daukar ciki da wuri) da kuma daina haihuwa a makare.

Wani  binciken  da aka yi a 2021 na cewa shan magungunan na iya kara hadarin kamuwa da cutar ko kuma ma su kara girmar wadanda suka riga suka fito, musamman saboda yawan sinadaran estrogen da cikin jikin mutun wadanda aka gano cewa karin kan bukace su wajen kara girma.

To sai dai, akwai binciken da ke nuna cewa idan har aka dade ana amfani da magungunan ana iya rage hadarin kamuwa da cutar.

Ra’ayin kwararru

A cewar Yan Katsnelson, kwararre wajen cire karin, “ba’a kai ga tantance taka mai-mai abin da k janyo fibroids din ba.” Ko da shi ke masu binike sun gano cewa ya na da alaka da wasu daga cikin sinadaran da ke cikin jikin mutun wadanda yawansu ko karancinsu ke tasiri a kai. Shi ya sa ma babu wata dabara ta bai daya na samun kariya ko kuma ma amfani da magungunan tazarar hauhuwar domin kowa na da salon da ya karbe shi.

A wasu lokutan magungunan sanya tazarar haihuwar da ke dauke da wadannan sinadaran kan taimaka wajen daidaita kwanakin hailar mace, su kuma kare hawa da saukan sinadaran, a cewar Katsnelsin. Amma sai dai karuwar wadansu sinadaran na daban su kuma na iya kara mu su girma.

“Ya kamata kowace mace ta tattauna irin zabin da take da shi na magungunan sanya tazarar haihuwa da likita, musamman idan har an tabbatar cewa ta na da karin,”  a cewar Katsnelson.

Wani likitan kyma, Doctor Stan, ya ce cewa shan magungunan lna janyo karin ba daidai ba ne kuma ma babu wata hujjar da ta goyi bayan hakan a kimiyance. Fibroids na zuwa ne saboda dalilai da dama musamman sauyin wasu sinadarai a jikin mutun kuma danganta shi da shan magungunan da ke sa tazarar haihuwa ba abu ne da aka tabbatar ba.

A Karshe

Da’awar cewa shan magungunan da ke sanya tazarar haihuwa na wani tsawon lokaci na janyo fobroids yaudara ce kawai. Babu wata hujja ta kimiya da ta goyi bayan wannann da’awar. Kwararru na cewa idan har mutun na fargabar shan magungunan tazarar haihuwar saboda hadarin kamuwa da fibroids din, ya tuntubi likita dan samun bayanan da suka dace.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »