African LanguagesHausa

Yaya sabuwar dokar haraji ta shafe al’uma? Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani

Getting your Trinity Audio player ready...

Ranar 26 ga watan Yunin 2025, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan wasu dokokin kwaskware tsarin harajin kasar wadanda za su fara aiki daga daya ga watan Janairun  2026 idan Allah ya kai mu.

    Wannan matakin ya zo ne yayin da ake cigaba da mahawar kan yiwuwar dorewar tsarin samun ko kuma dai ka’idar kudin kasar da yadda ya kamata ta rage dogaro da kudaden da shigan da ake samu wajen sayar da ma’adinan man fetir.

    Wannan sabon tsarin shi ne yunkuri mafi dogon buri a tarihin matakan da ake dauka wajen kwaskware dokokin karbar harajin kasar na tsawon shekaru da dama yanzu.

    A cewar Tinubu, wadannan  sauye-sauyen za su rage yawan dogaron da ake yi da man fetir su kuma fadada yawan wuraren samun haraji ta yadda zai tabbatar da adalci wa jama’a da manyan sana’o’i.

    Gyarar fiska a Dokar Kwaskware Harajin da ke kan Albashi, Dokar Harajin Kamfanoni, Dokar Harajin karin kudi (wanda aka gyara), Dokar ka’idar kudi (wanda aka gyara) duk suna daga cikin shirin ingantawa da sabunta tsarin harajin Najeriya ta zo daidai da zamani.

    Yayin da za’a zame masu samun karamin albashi da kananan  ‘yan kasuwa, masu samun albashi mai tsoka da manyan masana’antu ko ‘yan kasuwa mai yiwiwa za su biya kudi mai yawan gaske

    Bayan sauraron mahawarorin da ake yi dangane da gyare-gyaren tsarin harajin a shafukar yanar gizo, DUBAWA ta yanke hukuncin wallafa mahimman bayanan da suka shafi batun dan taimakawa ‘yan Najeriya wajen fahimtar manufar baki daya.

    Ga biyar daga cikin abubuwan da ya kamata ku sani dangane da sabbin sauye-sauyen harajin:

    1. Gwamnati ta dauke haraji wa masu karamin albashi. 

    A karkashin sabuwar DOkar Harajin Albashi, duk wadanda ke karbar kasa da N800,000 a shekara ba zai biya haraji ba. Wadanda kuma suke samu fiye haka  za’ sa sanya musu harajin a kan yawan kudin da ya gota mizanin daga kashi 15 cikin 100 har zuwa kashi 25 wa wadanda suke samun sama da naira miliyan 50 kowace shekara.  

    Tallafin rage haraji kan jimilar albashi wanda aka fi sani da Consolidated Relief Allowance (CRA) a turance, wanda rangwame ne da gwamanti ta rika bayarwa ga ma’aikata dan rage yawan albashin da da za su biya yanzu an kashe shi. Da ma ma’aikaci kan iya cire wani kaso na albashi misali N200,000 ko kuma kashi daya na jimilar albashi, hade da kashi 20 cikin 100 na albashin kafin ya kidaya kudin da za’a cire harabi a kai, wanda ta yin hakan nan da nan ya kan rage yawan harajin da ma’aikat za su biya.

    IA maimakon haka yanzu an gabatar dai da tsarin da ya ke la’akari da matsugunnen mutane, wanda zai sa wadanda ke hayar gidajensu su cire kashi 20 cikin 100 na kudin hayar shekara wanda zai iya kaiwa n naira 500,000, amma zai iya kasancewa kasa da haka. Wannan sauyin na da burin tabbatar da daidaito da kuma mayar da hankali kan abubuwan da al’umma ke bukata a zahiri kamar gida/matsugunnai.

    1.  Kudin sallama, kudaden da ake samu daga yanar gizo-gizo, ka’idojin zama dan kasa

    A karkashin sabuwar dokar, kudaden sallamar da ake bai wa ma’aikata sadda suka rasa aikinsu, ko kuma yayin da ake gudanar da sauye-sauye a wurin aikin da wadanda suka yi ritaya su ma duk za’a sauwake mu su harajin.

    A baya kudaden da suka kai naira miliyan 10 ne kadai ake cire mu su harajin ma’ana duk wani kudin da ya wuce hakan za’a cire haraji a kai.

    Da wannan sauyin a  kara mizanin zuwa  to Naira miliyan 50, wannan zai bai wa wadanda suka saba samun kudaden sallama mai yawa damar ajiye kaso mai tsako wa kansu a maimakon biyan haraji. Wannan zai kuma bai wa wadanda suka rasa aikin yi damar gyara makomarsu a tsanake.

    Bacin haka, kudaden da ake samuwa daga kafofin sadarwa irinsu YouTude, TikTok da sauran kafofin sada zumunta su ma za’a fara sa haraji a kan su. Haka nan suma kudaden kryto, da tallafi, da kudaden da ake samu daga kyauta idan an yi nasara a gasa ko kuma wata lamba ta yabo, duk za’a sanya haraji a cikinsu.

    A baya duk wadannan hanyoyin samun kudi ba’a yi la’akari da su cikin dokokin Harajin Najeriya ba bare a sanya ido a kansu. Yanzu da wannan sabon tsarin, infuluwensas, masu kirkiro shirye-shirye, da wadanda ke aiki a yanar gizo-gizo kadai, wadanda kuma duk ta wurin suke samun albashinsu su ma tilas su biya haraji kan albashinsu.

    Daga karshe, ka’idojin zama dan kasa su ma na gyara su, ma’ana, ‘yan Najeriyan da ke da kwakwarar dangantaka da iyalansu a kasar ma na iya biyan haraji a matsayin ‘yan kasa ko da kuwa suna zama a kasashen ketare. Haka nan kuma bakin da ke aiki suna samun kudi a Najeriya su ma za’a cire haraji kan kudin da suka samu a kasar.

    1. Kananan ‘yan kasuwa ba za su biya haraji ba amma manyan kamfanoni za su biya da yawa 

    Wadannan sabbin sauye-sauyen ma sun shafi ‘yan kasuwa, domin akwai wadanda suka sami sauki da wadanda kuma aka kara mu su nauyi.

    Kananan kamfanoni wadanda ke samun jimilar kudaden shiga kasa da miliyan 100 da kadarori kasa da naira miliyan 250 ba za su biya harajin da ake cirewa kan ribar da kamfani ya yi a cikin shekara ba, da  kudin da suka samu bayan sun sayar da kadarori wato capital gains tax a turance sai kuma harajin da ake sa wa a ribar kamfanoni da nufin sanya kudin wajen gudanar da ayyukan bunkasa cigaban kasa wanda aka fi sani da development levy a turance. 

    Manyan kamfanoni kuwa za su fiskanci matakai masu tsauri a ciki har da  kashi 15 cikin 100 na mafi karancin harajin da kasashen duniya suka amince da shi wato 15% global minimum tax wanda ke la’akari da ka’idojin kasa da kasa. Wannan na nufin manyan kamfanonin da ke aiki a Najeriya ba za su iya kai ribar da suka samu kasashen waje su kaucewa biyan haraji a Najeriya kamar yadda suka saba ba.

    Sabbin dokokin sun ma shafi sassan man fetir, hakar ma’adinai da wasannin bidiyo da komfuta dan gudanar da komai a bayyana an tabbatar da gaskiya kuma kowa ya dauki nauyin da ya rataya a wuyarsa wajen yadda kamfanoni ke bayyana ribar da suka samu da ma dai yadda suke biyan haraji. Alal misali, kamfanoni man fetir da gas yanzu dole sai sun bayar da cikakken bayani kan yawan man da suka sarrafa cikin wani rahoto, kuma irin wannan rahoton ya na kare magudi wajen gabatar da alkaluman yadda ya kamata. Haka nan kuma, kamfanonin hakar ma’adinai dole su fadi ainihin darajar ma’adinai su kuma biya harajinsu daidai yadda ya kamata.

    Masana’antun wasannnin bidiyo da komfuta da na caca duk sun habbaka a yanar gizo-gizo kuma yanzu za su fiskanci sa ido mai tsauri dan tabbatar da cewa masu irin kamfanonin na da lasisin da ya kamata sa’annan sun kuma biya yawan harajin da ya dace a kan kudin da aka ci da ribar da aka samu.

    Haka nan kuma, Yankunan Ciniki Kyauta wadanda ake kira Free Trade Zones  da turanci ko kuma FTZs, –  wadanda wurare ne da ake iya gudanar da kasuwanci ba tare an biya ciakken kudin kwastam da haraji ba, da nufin bai wa jama’a karfin gwiwar fitar da kayayyaki, – yanzu dole sai sun cimma wadansu mahimman ka’idoji kafin a cigaba da yi musu rangwamen da suke samu a harajin. Wato ke nan yanzu ya zama tilas kamfanonin da ke aiki a yankunan su bayar da hujjojin cewa lallai abubuwan da suke sarrafawa fitar da su suke yi  kuma ba wai abubuwan da za su amfani kasuwannin cikin gida ba ne sun jin dadin rangwaman da aka yi mu su a kan harajin. 

    1.  VAT zai cigaba da kasancewa kashi 7.5 cikin 100, amma an kara yawan wasu mahimman abubuwan da za’a daukewa VAT din .

    Harajin da ake karawa kan kayayyaki wanda ake kira VAT zai cigaba da kasancewa kan kashi bakwai da rabi cikin 100 duk da  irin  tayin  da aka yi na karawa. To sai dai jerin abubuwan da ba’a sanyawa haraji ko wadanda aka dauke mu su ya  karu inda aka hada abubuwan da ake bukata na rayuwar yau da kullun irin su abinci, kayayyakin kiwon lafiya da ilimi.  

    Gwamnatin ta ce an yi wannan gyaran ne da nufin kare masu karafin karfi a Najeriya daga hauhawar farashin kayayyakin yau da kullun. 

    Dole ‘yan kasuwa yanzu su bi dokoki masu tsari na rubuta takardun kudi ko da kuwa wanda ake yi a yanar gizo ne saboda a rage zamba cikin aminci a kuma inganta yadda ake yin harkokin karbar kudaden VAT din a bayyane.

    1. Tsarin gudanar da ayyukan karbar haraji a Najeriya na bukatar gagarumin sauyi. 

    Za’a maye gurbin Hukumar Tara Kudaden Shiga ta kasa (FIRS) da Ma’aikatar Tara Kudaden Shigar Najeriya (NRS) wata sabuwar hukuma wadda za’a ba ta ikon karbar haraji da ma sauran kudaden da ba haraji ba.

    Haka nan kuma an kirkiro wata hukumar karbar kudaden shigar ta hadin gwiwa wadda za ta hada duka ayyukan kudin tarayya da jihohi da na kananan hukumomi domin hana karbar haraji sau da yawa.

    Haka nan kuma an kafa ofishi na musamman wanda zai rika sa ido kan yadda ake gudanar da duk wani aiki da ya shafi haraji wanda aka fi sani da Tax Ombudsman da turanci, tare  da kotun daukaka kara dan sake karfafa hanyoyin kare masu biyan haraji cikin adalci.

    Ofishin na Tax Ombudsman zai kasance ofishi mai zaman kan shi wanda zai rika gudanar da bincike kan korafe-korafen da masu biyan haraji za su gabatar. Zai kuma kasance mai shiga tsakanin ‘yan kasa da hukumar karbar kudaden shigan ta yadda zai taimaka wajen shawo kan matsaloli. 

    Shi kuma kotun daukaka karar wato Tax Appeal Tribunal, a waje guda kuma an kara fadada shi ta yadda zai iya kula da korafe-korafen da ke da dangantaka da hajari cikin sauki, ta yadda za’a iya shawo kan matsaloli ba tare da zuwa babban kotu ba.

    An tsara wadannan cibiyoyin ne dan su kara karfafa tsarin harajin Najeriya su ba shi nagarta da inganci ta yadda zai biya bukatun al’umma.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button
    Translate »