African LanguagesHausa

Jimilar abin da Najeriya ke samu kowace shekara kan kowane mutun daya: Warware gaskiya tsakanin da’awowin da Adesina da Onanuga suka yi

Getting your Trinity Audio player ready...

Cikakken bayani

Wata  takaddamar da ta afku kwanan nan tsakanin Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa da Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya kasa ta Afirka wato AfDB, ya mayar da hankulan jama’a kan batun tarihin tattalin arzikin Najeriya da yadda ake fassara alkaluman da ke kwatanta jimlar abin da kasa ke samu kowace shekara a kan kowane mutum wato GDP per capita. Mr Adesina ya ce abun da Najeriya ke samu kan kowane mutun GDP per capita a shekarar 1960 na zaman $1,847, abun da a cewarsa ya wuce abun da ake samu yanzu. Ya kuma kara da cewa darajar abin da mai matsakaicin karfi ke samu yanzu shi ma ya ragu sosai

Ko da shi ke Mr Onanuga, ya kalubalanci wannan da’awar inda ya hakikance kan cewa GDP ko kuma abin da kasa ta samu a shekarar 1960 kan kowani mutun daya bai kai haka ba, ya ce darajar kudin ta fi kusa da dalar Amurka 93 kuma abin da kowani mutun daya ke samu a Najeriya ya karu sosai a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.

Duk da cewa duk yunkurin da muka yi na tuntubar Mr Adesina dan jin majiyar da ya ke dogora da ita ya ci tura, wannan takaddamar na nuna mahimmancin fahimtar ainihin yadda ake auna GDP da ma yadda ya kamata a fassara ire-iren wadannan alkaluman ba tare da yin kuskure ba.

Fahimtar jimilar abin da kasa ke samu kan kowani mutun daya ko kuma GDP Per Capita

GDP per capita wani ma’auni ne da ke gwada tattalin arzikin kasa wanda ake samu bayan an raba yawan abin da kasa ke samu kafin haraji da yawan al’ummar kasar. A nan ana nufin cewa GDP shi ne darajar duk wasu kayayyaki da hada-hadar da ke samar da kudi a cikin kasa kowace shekara.  

Wannan lissafin na nuna matsakaicin karfin tattalin arzikin kowani mutun daya kuma ana amfani da shi wajen kintatar yanayin rayuwa da arziki. Alal misali, idan har kasa ta na da GDP na dalar Amurka biliyan 500 kuma yawan al’ummarta miliyan 50 ke nan kowani mutun daya zai sami dalar Amurka dubu 10 ke nan. Yayin da wannan kwatancen da na yi ya yi kamar abun ba wahala wata sa’a lissafa GDP ya fi haka sarkakiya kuma ya danganci salon da aka yi amfani da shi wajen aunawa.

Masana tattalin arziki na amfani da hanyoyi daban-daban wajen lissafa GDP dan gano abubuwa iri-iri. Akwai wanda ke kidayar darajar abun da kasa ke samu daga kayayyaki da hada-hadar kudi kadai ba tare da yin la’akari da hauhawar farashin kayayyaki ba. Wannan na iya yaudarar jama’a musamman idan ana kwatanta alkaluman da na shekarun baya saboda hauhawar farashin na iya karawa GDP daraja ba tare da nuna cewa tsadar farashin kayayyaki ne kawai ba wai darajar kayayyakin da ake sarrafawa ne ta karu ba.

A waje guda kuma, GDP na ainihi kan iya yin la’akari da tsadar farashin kayayyakin ya gyara lissafin dan samar da alkaluman da ke nuna ainihin abin da al’umma ke samu ya kuma gano ko rayuwarsu na dada inganta. Misali idan GDP ya karu da kashi biyar cikin dari sa’annan kuma tsadar farashin kayayyaki ya karu da kashi 4 cikin 100 ke nan ainihin abin da kasa ta samu ya karu da kashi daya cikin 100 ne kadai.

GDPn da ya yi la’akari da daidaiton da ke tsakanin darajar takardun kudi da farashin rayuwa ko kuma PPP kamar yadda aka fi sani da turanci, kan lura da banbancin da ke tsakanin farashi ko kuma tsadar rayuwar da ke tsakanin kasashe. Irin wannan na da mahimmanci sosai musamman idan aka kwatanta da kasashen kasa da kasa domin takardun dala ko pam na iya sayen kayayyaki da yawa a wata kasar fiye da wata kasar,  dan haka PPP ya fi bayar da ma’auni mafi ma’anan na ainihin karfin kudaden shiga a kasashen duniya.

Dogaro da GDP kan kowani mutun daya kadai na iya janyo kura-kurai sosai. Wata kasar na iya bayyana kamar tana da arziki saboda hauhawar farashin kayayyaki da ma rashin daidaito a darajar takardun kudinta, to amma idan har aka gyara yadda ya kamata, yanayin tattalin arzikin kasar kan kasance daban.

GDP kan kowani mutun daya a Najeriya: takaitaccen tarihi

A lokacin da Najeriya ta sami ‘yancin kai a shekarar 1960, ana kiyasin darajar GDP dinta a kan $4.2 billion da al’ummar da ke da yawamn miliyan 44.9 million. Idan aka raba wannan da yawan al’umma ke nan kowane mutun day na zaman $93.54 ke nan, abun da ya gaskata bayanin Mr Onanuga. A shekarun 1960, yawanci Najeriya ta fi dogaro ne da noma, da masana’antu kalilan tare da ababen more rayuwa wadanda su ma ba su da wani yawan gaske. A lokacin ne tattalin arzikin kasar ta kara bunkasa, kuma tsarin albashi ba shi da wani yawan gaske idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya.

Gano man fetur da hakon shi daga karshen shekarun 1950 zuwa farkon shekarun 1960 ne ya bude sabon babi. Kudaden shigan da aka rika samu daga man fetur sun kara habbaka kudaden shigan kasar baki sadda aka yi yayen bunkasar man fetir a shekarun 1970, wanda ya yi sanadin kara yawan ababen mire rayuwa, gina birane da kuma yunkurin samar da sabbin hanyoyi na habbaka tattalin arziki. 

Ya zuwa sheakrar 1980, abin da Najeriya ke samu kowace shekara a kan kowani mutun daya ya wuce $880. Bayan da aka sake daidaita GDP din da ya yi la’akari da fadadae da aka samu a fannin tattalin arziki, alkaluman da aka samu daga bankin duniya sun bayana cewa adadin ya kai kolouwarsa ne a kan kimanin $2,585.7 a shekarar 2015. 

A ‘yan shekarun nan, Najeriya ta fiskanci kalubalen tattakin arzikin da suka hada har da karyewar darajar takardun kudi, rashin daidaitton farashin man fetur da kuma karuwar yawan al’umma duk wadanda suka taru suka raunata darajae GDP a kan kowani mutun daya. A shekarar 2023, an yi kiyasin GDPn Najeriya a kan kusan $363.85 billion, da al’ummar da ke da yawan kusan miliyan 226.2, abun da ya sa GDP kan kowani mutun daya a kan kimanin  $1,596.6. Yayin da wannan ya yi kasa da adadin da aka samu ko a shekarar 2015 sadda ya kai kololuwarsa, wannan na wakiltar karuwa na kusan ninki sau 17 daga abin da adadin ya kasance a shekarar 1960.

Daidaita tsakanin alkaluma a zahiri da hasashen jama’a

GDP kan kowani mutun daya abu ne da akan nema a duk sadda ake kokarin bayyana matsakaicin abin da ake samu daga tattalin arzikin kasa dan kwatanta shi da abin da sauran kasashe sa’o’i ke samu na wani tsawon lokaci. Karuwar da Najeriya ta samu daga kusan dalar Amurka 93 a shekarar 1960 zuwa $1600 a shekarar 2023 ya nuna cewa lallai an sami karuwa sosai. Wannan zai taimakawa masu kirkiro manufofi wajen nazari da kuma gano salon yanayin abubuwan da ke tashe ta yadda za su iya tantance tasirin manufofin tattalin arziki da sauran manufofin ketare da ka iya yin tasiri kan su.

To sai dai tantance GDP a haka na da na shi gazawar. Ba lallai ne ya yi la’akari da yawan albashin da mutane ke samu a kasa ba. Najeriya na da rashin daidaito na albashi, da abin da ake kira Gini coefficient da turanci  abun da ke nufin rashin daidaito na kudaden shigan al’umma  35.1 a shekarar 2022, wanna na nuna cewa arzikin bai rabu daidai ba, Bacin haka akwai banbanci sosai tsakanin wadanda ke rayuwa a birane irin su Legas da wadanda ke karkara. Wannan na nufin cewa yawancin al’ummar ba su ci gajiyar karuwar da aka samu a alkaluman GDP din ba.

Haka nan kuma, adadin GDP kan kowani mutun daya bai cika la’akari da fannonin da ba su tasiri kai tsaye a kan tattalin arzikin kasa ba wadanda suka hada da kiwon lafiya, ilimi, tsabtataccen ruwan sha, da muhalli mai inganci. Alal misali  Ma’aunin Tantance Cigaban Dan Adam Najeirya ya kasance a mataki na 163 cikin kasashe 191  a shekarar 2022, wannan na nufin habbaka ko karuwar GDP kawai ba ya nufin cewa rayuwar dan adam zai ingantu. 

Tashi da saukar takardun kudi da farashin kayayyakin masarufi na iya rage darajar GDP. Ganin yadda GDP na Najeriya ya kai kololuwarsa a sheakarar 2015 na nuna cewa takardun kudin Najeriya ya kasance da daraja sosai wanda ya rika taimaka wa jama’a su yi sayayya,  kafin aka rage mu su karfi. 

Bayanai masu karo da junan da Adesina da Onanuga suka yi na iya kasancewa banbancin da ke tsakanin majiyoyin da suka yi amfani da su ne, da ma’aunan da aka yi amfani da su wajen samun bayanan ko kuma rashin fahimtar wasu daga cikin kalaman da aka yi amfani da su. Bayanan da aka samu daga tarihi na nuna cewa GDPn Najeriya a shekarar 1960 bai kai dalar Amurka 100 kan kowani mutun daya ba, amma wannan adadin ya karu a cikin shekarun da suka biyo baya.

Sai dai fahimtar da ake wa koma bayan tattalin arziki a GDP bayan habbakar da ya yi a shekarar 2015, karuwar yawan al’umma, rashin da talauci da rashin daidaito, abin da ke nufin cewa habbakar da aka samu bai yi tasiri a kan rayuwar al’umma ba duk da irin karuwar da ake shaida cewa ya faru.

Kwarraru sun sa baki

Victor Aluyi, kwararre kan tattalin arziki kuma daya daga cikin wadanda suka mallaki kamfanin shawarwari kan zuba jari a matakin kasa da kasa na Aztran Global Investment, ya jaddada mahimmancin tantance ainihin ma’aunan da ke nuna tattalin arziki a zahiri, musamman halin da mai matsakaicin karfi ke da shi. A cewarsa hauhawar farashin kayayyakin da aka yi fama da shi cikin shekaru bakwan da suka gabata ya yi tasiri sosai kan ‘yan Najeriya wajen samun halin biyan kudaden haya, motar haya da kayayyakin masarufi.

Mr Aluyi ya kuma yi la’akari da mahimmancin sake duba ainihin ma’aunan da ke nuna cigaban dan adam, wadanda suka hada har da ilimi, da lafiya da ma darajar mafi karancin albashin da suke karba. A cewarsa, “Idan muka dubi mafi karancin albashin da mu ke da shi yanzu, kimanin N70,000 ne. A ‘yan shekarun da suka gabata ya na kan N30,000. To sai dai idan muka canza shi zuwa dalar Amurka, mafi karancin albashi na N30,000 zai yi kamar ya fi daraja a kan N70,000.” Ya ce wannan na nuna bukatar yin la’akari da wasu mahimman abubuwan da suka hada da abubuwan da mutane za su iya saye da albashin da suke samu a maimakon alkaluman kadai.

Joseph Ajibola, farfesa na harkokin kudi da tattalin arziki a jami’ar Caleb da ke Legas ya ce dogaro da alkaluman da su wakiltar abin da ake fama da shi a zahiri a rayuwar yau da kullun tamkar rashin adalci ne wajen rabon arzikin kasa, wannan na zaman yadda ake kwatanta rashin adalcin tsarin biyan jama’a. Ya ce “idan har GDP kan kowani mutun daya ya kan kai kan kashi 10 cikin 100 ne kawai wadanda yawanci suke rike da manyan mukaman iko tare da barin sauran kashi 90 cikin darin da suka rage cikin talauci, duk wani adadin da ake la’akari da shi  ba shi da wani tasiri.

Mr Ajibola ya ce, “Shin rayuwar ‘yan Najeriya yanzu ya fi wanda suka yi a shekarar 1960 idan har muka yi nazarin shi a kan mizanin cigaban dan adam? Amsar ita ce a’a.” Ya amince cewa yayin da cigabar da aka samu a fannin fasaha ya bayar da damar samun bayanai da sauran harkoki, zakarar gwajin dafi shi ne kwatanta halin da mutane ke da shi a daa din da yanzu. “Wanda ke samun fam daya zai iya sayen mota da gida a wancan lokacin yanzu ko har nawa mutun ya ke bukata kafin ya sayi mota da gida? Irin tambayoyin da ya kamata a rika yi ke nan.”

Ajibla ya yi kira ga gwamnati da ta samar da manufofi da shirye-shiryen da za su taimakawa talakawan Najeriya wajen yaye talauci. Ya ce cigaba mai mahimmanci tilas ne ya yi la’akari da halin da jama’a ke ciki a zahiri. “Idan har tattalin arzikin bai biya bukatun tattalin arzikin da mutane da ke da shi ba, akwai matsala ke nan wajen manufofin da ake samarwa jama’a, ya ce”

A Karshe

Bacin mahimmancin da GDP ke da shi,shi kadai ba zai iya bayar da cikakken bayani kan sarkakiyar da ke tattare da matsalolin kasar da suka hada da rashin daidaito na albashi, talauci, da kalubalen da ke tattare da cigaban dan adma. Yayin da alkaluman da ake da su kan GDPn Nigeria, kamar yadda Mr Adesina ke da’aawa ba shi da isashen hujja, bayanin shi kan koma bayan tattalin arzikin Najeriya ba daidai ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »