African LanguagesHausa

Da gaske ne 9 ga watan Yuli,2025 ita ce rana mafi gajarta?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa ranar 9 ga watan Yuli,2025 itace ranar da zagaya rana da duniya ke yi a kullum ta zamo mafi sauri a tarihin duniya.

Da gaske ne 9 ga watan Yuli,2025 ita ce rana mafi gajarta?

Hukunci: YAUDARA CE, rahoto da ake da shi kawo yanzu ya nunar da cewa ranar 5 ga watan Yuli,2024  itace mafi sauri da aka ga duniya ta zagaya rana, inda duniyar ta zagaya da ragin 1.66 milisakan. Rahotanni da aka tattara daga hukumar kasa da kasa mai kula da yadda duniya ke  zagaya ranar da sauran bayanai da aka tattara ya nunar da cewa a ranar 9 ga watan Yuli, 2025  ta zagaya da ragin 1.37 milisakan wanda ya zama kasa da sa’oi 24.

Cikakken Sako

A ranar 9 ga watan Yuli, 2025 wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Project Nightfall ya wallafa (posted) cewa duniya za ta zagaya cikin sauri sabanin sa’oi 24 da aka saba gani an samu raguwa da milisakan 1.3 zuwa 1.6. Mai da’awar yace sauyin ya samu ne dalilin sauyin inda wata yake idan aka kwatanta daga tsakiyar duniyar.

Ya zuwa ranar 17 ga watan Yuli,2025, sama da masu amfani da shafin Facebook 62,000 sun yada wannan wallafa wacce ta samu martani 193,000 kana masu tsokaci (comments) 12,000, a  tsawon wannan lokaci.

Yayin da Project Nightfall ke nuni da cewa wannan rana na daga cikin ranakun da suka zama mafi gajarta a tarihin wannan zamani. Wasu masu amfani da shafin na Facebook sun nunar da cewa itace rana mafi gajarta.

Yayin da wannan labari ya yadu a shafukan sada zumunta da dama da DUBAWA ta lura da wasu sun nuna shakku a game da wannan batu.

Yayin da yake mayar da martani a gajeran bidiyo na (reel) Eric Deters for Kentucky and America’ a ranar 10 ga watan Yuli,2025 Michele Wright yace “Jiya [9 ga watan Yuli,2025] ita ce rana ta tara a jerin irin wadannan ranaku, ba itace mafi gajarta ba!”.

David Nunn yace, “wace asara zanyi ta lokacin bacci na? Ina yin aiki ne da dare.”

Mun kuma samu irin wannan da’awa kamar a wadannan wurare (here) da (here).

Duk da cewa za a iya ganin wannan banbanci a matsayin dan kadan, zai iya haifar da rashin fahimta na yadda dabi’ar duniya take, da fasahar zamani da tsari na duniya da yadda taurari ke kara kaina a samaniya da yadda ake ajiye ko lissafin lokaci na duniya da ba a bukatar kuskure. Tasirin wannan da’awa ga tsarin rayuwar yau da kullum ya sanya DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan bayani.  

Abubuwan da ke tasiri ga juyawar duniya

Duniya na juyawa ne a hankali (spins relatively) ta zaga rana ta yadda za a samu cikakkiyar rana cikin sa’oi 24, a wannan zagaye ake samun cikakken lokaci da akan fitar da rana da dare da ke zama bangare na rayuwar halitta kullum. 

Duk da cewa yadda duniya ke zagaya rana a kullum  (Earth’s rotation) sau tari ba a samun wata matsala, ana dan samun banbanci kadan (minor variations) a yanayin saurinta, irin wannan banbanci kan yi tasiri (affects ) wajen lissafi ma lokaci a wayoyin hannu da tsarin tsayawar duniya na GPS da yadda ake samun bayanai daga tauraron dan Adam.

Abubuwa da dama na halitta na iya jawo duniyar ta dan yi sauri na takaitaccen lokaci. 

  1. Karfin maganadisun wata 

Wata na da wani karfi(tidal forces) na iya jan abubuwa kan duniya, abin da ke tasiri kan teku da ita kanta tsandaurin kasar. Bayan tsawon lokaci irin wannan karfi na rage saurin zagayawar duniya ga rana, abin da ke kara tsayin sa’oi da rana da kimanin milisakan 1.7 a duk bayan shekaru 100. Haka kuma bigire da wata yake idan aka kwatanta da inda duniya take shima wannan na tasiri ya kawo banbanci na lokaci kalilan a wani lokaci watan na wani bigire idan aka kwatanta da inda duniya take, wannan na dan iya sawa duniya ta kara saurin zagaya rana da take yi.

Adetola Oniku, farfesa a kimiyar ilimin tarihin kasa da dabi’unta na Geophysics a jami’ar Modibbo Adama da ke Yola yace akwai karfin maganadisun wata da ke tallafar duniya ta dan karkace a yanayin zamanta, “Ba don wannan karfin maganadisun na wata ba yanayin daidaiton duniya daga samanta zuwa kasa zai iya samun kai a yanayi na rudani, ” a cewarsa.

Karfin da ke iya sanya motsin teku wanda daga wata yake, abun na zagayen ranar da duniya ke yi sannu-sannu ne da  tasirinsu ke zuwa kadan-kadan a tsawon lokaci.

  1. Rarrabuwar abubuwa masu nauyi a kan kasa

 Teku da tsandaurin kasa da kaikawon iska da suka samar da nauyi ga duniya ana samun sauye-sauye a wajensu, yadda ake samun sauyi a kan motsin teku da yanayin kai-kawon iska wannan na tasiri ga irin nauyin da ke kan duniyar.

Ga misali a irin wannan yanayi (such phenomena) misali dalar kankara inta narke za ta kara yawan ruwa a teku, wannan zai sa nauyin ruwan daga arewacin duniya zai yi kokarin dannowa tsakiya, a samu  tafiyar hawainiya a juyawar duniya wajen zaga rana a samu rana ta yi tsayi. 

Duniya na saurin juyawa ne idan nauyi ya tattaru a wurin da take juyawa dalilin tattarar kankara, haka nan sai ta koma juyawa a hankali biyo bayan janyewar nauyin idan kankarar ta tafi. Ta hanyar amfani da hoton duniya, masana kimiya sun gano (detected) taruwar kankara a yankin na Antartica tsakanin 2021 da 2023.

Is July 9, 2025, Earth’s shortest day?Yadda aka samu tarin kankara a yankin Antartica tsakanin 2002 zuwa 2023 yadda aka samo hoton: SciTech Daily.

  1. Motsi-motsin duniya da motsi na cikinta

Motsin duniya da ake samu na kawo juyi move the ground da sauye-sauye a duniyar, abin da ke kawo kananan motsi da juyawar duniya cikin sauri, misali babbar girgizar kasa da aka yi a Chile (2010) da Japan (2011)  abin da ke kawo raguwar lokaci milisakan kadan.

Zemba Audu, masanin kimiyar sauyin yanayi a jami’ar Modibbo Adama University, Yola, yace akwai abubuwa da dama da dan’Adam ke yi kamar fitar dagas da ake fitarwa daga masana’antu da sare bishiyu da sauran abubuwa da ke lalata samaniya da kawo sauyin yanayi, abin da ke kawo sauyin yanayin zafi da sanyi da yanayin ruwan sama. 

Yace irin wannan sauyin yanayi da abubuwa masu alaka da hakan kan jawo tasiri ga yadda duniyar kan juya a kowace rana. “Yanayin yadda duniyar kan juya na jawo bugawar iska yayin da take kaikawonta a samaniya, tayiwu guguwa ce ko wutar daji da sauransu, wani lokacin iskar kan tafi da sauri-sauri ko a hankali a hankali.” a cewarsa. 

Kasancewar a Najeriya ba a fuskantar girgizar kasa ko guguwar da kan zama ta bala’i, Zemba yace ana ganin tasirin sauyin yanayin ta hanyar samun kanfar ruwa da zafi mai muni da ruwan sama mai yawa da kan jawo ambaliya a kasar.

Shin 9 ga watan Yuli, itace ranar mafi kowacce gajarta a tarihi?

Shafukan facebook da dama sun yi da’awa kan irin wannan lamari, inda suka nunar da cewa itace mafi gajartar rana a tarihin wannan zamani. Masana ilimin kimiya sun tattara bayanai da suka nuna yadda duniyar ke juyawa cikin sauri tun bayan fara tattara bayanan lokaci (atomic clocks) inda ake samun bayanai daidai a shekarun 1960. Wasu kayan aikin da ake amfani da su wajen tattara bayanan sun hadar da (Very Long Baseline Interferometry (VLBI),) wanda ke amfanin da turakun neman signa ta rediyo (antena) da ke leko taurari daga nesa, wani kuma shine Satellite Laser Ranging (SLR), wadannan kayan aiki sun taimakawa masana ilimin kimiya samun bayanai da ke zama cikakku kan bayanan yadda duniya ke motsawa, wasu bayanan da aka tattara a wannan zamani sun hadar da,

  •  29, Yuni 2022: an samu raguwa da  1.59 milliseconds  wanda ya kasance kasa da yadda aka saba gani a wannan rana an samu wannan ranar da sakanni 86,398.41.
  • 26, Yuli,2022: wannan rana an samu ragi na 1.50 milliseconds, aka sami sakanni 86,398.5.
  • 5, ga Yuli 2024: A wannan rana ma an samu ragi da  1.66 milliseconds.
  • 9 ga Yuli, 2025: Wanda shine kiyasi da aka tattara na bayanan a tsarin kalanda da aka samu ragin na 1.37 milliseconds kasa da sa’oi 24.

Is July 9, 2025, Earth’s shortest day?Tsayin ranaku a 2025. Asalin inda aka samo bayanan: The Weather Network

Yawan adadi na milisakan da ake samu ya ragu a rana da take da 86,400, kan sa tsayin rana ya ragu, don haka a ranar 5 ga Yuli,2025 an samu raguwar milisakan 1.66 hakan ya sanya wannan rana ke da milisakan 86,398.34.  

Bayanai da ake da su daga cibiyar tattara bayanan yadda rana ke zagayawa a kullum International Earth Rotation and Reference Systems Services (IERS) sun nunar da cewa rana da ta zama mafi gajarta a tarihi itace 5 ga Yuli,2024, haka nan za a samu wasu ranakun da za su zama masu gajarta kamar 22 ga Yuli da 5 ga Agusta,2025.

Karshe

Sabanin bayanan da aka rika wallafawa a shafukan na facebook, ranar 5 ga watan Yuli,2024 itace mafi gajarta kamar yadda bayanan hukumar kasa da kasa da ke tattara bayanan zagayawar rana (International Earth Rotation and Reference Systems Services (IERS) suka nunar, wanda ya nunar da cewa akwai banbanci da ranar ta 9 ga Yuli,2025 da ta samu raguwar milisakan 1.37.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »