African LanguagesHausa

Da Gaske ne wani Kansila ya raba babura da abinci da kudade a jihar Sokoto?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wasu shafukan Facebook sun yi da’awar cewa, Kansila a jihar Sokoto ya raba babura, kayan abinci da kudade.

Da Gaske ne wani Kansila ya raba babura da abinci da kudade a jihar Sokoto?

Hukunci: Yawanci Karya ce, Dubawa ta gano cewa kayan abincin wani dan kasuwa ne ya sauke farashinsa, sai kuma shugaban matasan APC a Sokoto ya raba kudade, yayin da Kansila ya raba babura kawai.

Cikakken Bayani

Mukamin Kansila shi ne mukami na kasa a tsarin mukaman siyasa wadanda al’umma ke zabe a Najeriya, kuma aikin Kansila ya takaita ne kawai wajen gudanar da mazaba daya a cikin karamar hukuma. Haka kuma yana gudanar da aikin shi ne a karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar. 

Tun a ranar Jumu’a, 7 ga watan Marin na 2025 wani labari ya karade shafukan sada zumunta na Facebook da X dake cewa, wani kansila a jihar Sokoto, ya rabawa al’ummarsa kayan abinci da babura da kudade.

Labarin wanda aka rika wallafawa tare da hotuna, ya nuna buhunnan abinci da babura ajiye a lokacin da ake shirin raba wa ga mutane.

Da Gaske ne wani Kansila ya raba babura da abinci da kudade a jihar Sokoto?

Hoton da aka zakulo a Facebook

Sai dai mutane da dama na yin mamakin wannan labarin, har wasu ke yin tambaya cikin nishadi cewa “Dan Crypto ne ko NGO yake aiki?”

Ganin yadda mutane ke nuna shakku akan wannan labari, ya sanya Dubawa yin bincike domin tabbatar da sahihancinsa.

Tantancewa

Binciken da Dubawa ta yi a shafin nema na google ta gano cewa babu wata sahihiyar kafar yada labarai da ta ruwaito labarin da ake yadawa.

Sai dai da muka yi amfani da shafin nema na Facebook, mun gano shafin gidan talabijin na Alu TV; gidan talabijin mai zaman kansa a jihar Sokoto wanda ya yada aikin rabon tallafin kai tsaye a shafin.

A bayanin da aka wallafa, rabon tallafin an yi shi ne kashi hudu kuma dukkaninsu gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ne ya jagorance bayar da su. 

Na farko rabon tallafin kudi ga mata, matasa da mabukata wanda Alhaji Nasiru Italy, shugaban matasan APC na jihar Sokoto, sai kaddamar da siyar da tallafin kayan abinci da wani dan kasuwa Alhaji Salmanu Dan-Malam Makerar Assada zai yi, na uku kuwa shne rabon kayan abinci ga masu lalura ta musamman da ma’aikatar kuma da masu bukata ta musamman ta yi, sai na karshen shine gabatar da kyautar babura ga magoya bayan jam’iyyar APC wanda Alhaji Abu Mairodu jigo a jam’iyyar ya samar.

Binciken Dubawa ya gano cewa Alhaji Abu Mairodu shine Kansilar mazabar Gagi ‘B’ dake cikin karamar hukuma Sakkwato ta Kudu.

Wani dan jarida ma’aikacin Vision FM Sokoto da ke aika rahoto daga gidan gwamnatin jihar Sokoto, Bello Abdullahi ya tabbatar wa Dubawa cewa ya halarci wannan taron na rabon kayan tallafin kuma Alhaji Abubakar Mai Rodu, ya bayar da kyautar babura ne kawai ga magoya bayan jam’iyyar APC a jihar ta Sokoto.

A Karshe

Yawanci Karya ce, Dubawa ta gano cewa kayan abinci da aka nuna wani dan kasuwa ne ya sauke farashinsa, sai kuma shugaban matasan APC a jihar Sokoto ya raba kudade, yayin da Kansila ya raba babura kawai, dukaninsu Gwamna Ahmad Aliyu ne ya kaddamar da su.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »