Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Yawan musulmai ya karu da kashi 37 a kasar Burtaniya?

Hukunci: Karya ce. Kidayar jama’a ta 2021 ta nuna cewa kashi 6 ne kawai musulmai a yankunan Ingila da Wales na kasar Burtaniya.
Cikakken Bayani
Mabiya addinin musulmi sun shiga kowane yanki na duniya, inda mafi yawan musulmin suke zaune a yankin Asiya, kasashen da suka hada da Indonesia, Pakistan, Indiya, da Bangladesh, wadanda ke da mafi yawan al’ummar musulmi a duniya.
Baya ga yankin Asiya da tekun Pasifik, akwai kuma dimbin al’ummar musulmi a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka, da kuma yankin kudu da hamadar Sahara.
A Nahiyar Turai ma, ana samun karuwar al’ummar Musulmi musamman a birane.
Wani shafin Facebook mai suna African Daily News ya wallafa wani labari dake cewa yawan musulmai a kasar Burtaniya ya karu da kashi 37, haka zalika masallatai sun karu da 1500 a kasar.
Hoton da aka zakulo a Facebook
Wannan labarin da aka wallafa ya dauki hankalin mutane da dama, inda sama da mutane 2,900 suka yi sharhi (comments) akan labarin, yayin da mutane 895 suka yada shi (share).
Wannan ne yasa Dubawa yin bincike domin tabbatar da gaskiyar wannan labarin, a kokarin da take yi na yaki da labarai na karya.
Tantancewa
Dubawa ta fara bincike a shafin nema na Google domin ganin ko akwai wata kafar yada labarai da ta ruwaito labarin, sai dai duk kalmomin da muka saka a yayin binciken, babu inda muka samu sabon labarin da ke cewa yawan musulmai ya karu a Burtaniya.
Mun kuma gano cewa kidayar jama’a ta karshe da aka yi a Burtaniya ita ce ta shekarar 2021 a yankin Ingila da kuma Wales sai 2022 da aka yi kidayar a Scotland, kamar yadda shafin Wikipedia ya nuna.
A cewar shafin majalisar musulmai na kasar Burtaniya, bayanai daga ofishin kididdiga sun nuna cewa yawan al’ummar musulmi a Ingila da Wales sun kai miliyan 3.87 a shekarar 2021 adadin da ya kai kashi 6% na yawan jama’ar yankunan milyan 59.60.
Hakan na nuna cewa yawan Musulmi ya karu da miliyan 1.16 idan aka kwatanta da shekarar 2011, inda adadin ya kai miliyan 2.71.
Majalisar ta MCB ta kara da cewa sakamakon binciken da ofishin kididdiga na kasar Burtaniya ya fitar, ya nuna cewa musulmai suna da kashi 6.5% na yawan jama’a ne kawai.
A Karshe
Karya ce. Binciken Dubawa ya gano cewa kidayar jama’a ta karshe da aka yi a shekarar 2021 ta nuna cewa kashi 6 ne kawai musulmai a yankunan Ingila da Whales na kasar Burtaniya.