African LanguagesHausa

Hotunan Masu Gudun Hijira ‘Yan Afirka Ba Daga Rikicin Rasha da Yukraniya suka fito ba

Zargi: wata kungiya a shafin facebook ta wallafa hotunan wadansu ‘yan asalin Afirka masu gudun hijira tana zargin wai an ci zarafinsu a kan iyakar kasar Poland sakamakon yakin da ke gudana tsakanin Rasha da Yukraniya. 

Bayan da Rasha ta kaddamar da hare-harenta a kan Yukraniya, milliyoyin mazauna kasar suka fara kaura zuwa kasashen da ke makotaka da su dan samun mafaka. Wannan yanayi wanda aka kwatanta shi a matsayin yaki mafi tsanani a wannan zamanin tun bayan yakin duniya na biyu, ya janyo fargaba sosai a duniya.

Sai dai lokacin da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta ce ta “damu” da rahotannin cewa ana hana ‘yan Afirkan da ke Yuraniya ketara iyakokin dan samun mafaka kamar sauran mutanen da ke kokarin tserewa daga rikicin, sai batun ya bayar da damar tsokaci iri-iri dangane da batun musamman matsalar nuna wariyar launin fata da har yanzu ake fama da ita a Turai.

Sakamakon haka ne wata kungiya mai shafi a facebook, mai suna “Biafra Defense Force” ke zargin cewa ‘yan Afirkan da ke kokarin tserewa daga Yukraniya na fiskantar cin zarafi mai tsanani a kan iyakokin kasashen da ke makotaka da kasar, musamman kasar Poland. 

Kungiyar ta wallafa labarin da wani hoton wadansu da ake zargi ‘yan Afirka ne a kan iyakar wata kasar Turai. 

 “LABARI DA DUMI-DUMI  16-03-2022 Babu wani dan Afirka mai hankali da zai goyi bayan Yukraniya. Wannan yakin da ke tsakanin Rasha da Yukraniya ne. Dubi yadda ake wulakanta ‘yan Afirka. Fararen fata na zamansu lami lafiya a Poland. Sai wasu muggan shuwagabanni na cewa “Muna tare da Yukraniya Muna tare da Yukraniya.” ‘Yan Afirka ba wanda ya damu da wanda ke da bakin fata. Ku dubi hotunan da kanku ku gani,” a cewar kadan daga cikin labarin. 

Wannan zargin ya janyo martanoni daban-daban daga wadanda hotunan suka sosa mu su rai. Wani mai amfani da shafin, Omomor Donatus ya nuna takaicin shi da shugabannin Afirka inda ya danganta labarin da rashin shugabanci nagari. 

“Ina matukar jin zafin wannan lamarin, duk wannan laifin shugabanninmu ne da dolayen matasan da ke cin raguwan da suka yar suna mara musu baya,” ya ce. 

Tunda rikicin Yukraniya ya fara, ake danganta rahotanni da dama da rikicin Yukraniya wadanda DUBAWA ta gani kuma ta tabbatar cewa wadansunsu ba gaskiya ba ne. Shi ya sa wannan zargin ke bukatar bincike. 

Tantancewa

Lokacin da DUBAWA ta sanya hotunan a manhajan Yandex dan tantance mafarinsu, sakamakon ya nuna cewa duk hotunan uku na dandalin hotuna na Getty Images – Wanda dandali ne da ke samar da hotunan labarai. Haka nan kuma, bayanan da ke kan hotunan sun tabbatar cewa ‘yan asalin Afirka ne ke cikin hotunan amma masu yunkurin gudun hijira ne wadanda mahukuntan Spain suka cafke yayin da suke kokarin ketare iyakar shiga kasar Spain daga Morocco.

“Wannan bidiyon na nuna ‘yan gudun hijira ne a wani masauki na wucin gadi da aka tanadar wa masu gudun hijira da wadanda ke neman mafaka ta siyasa (CETI) a Melilla bayan da suka haura katangar da ke raba Melillar kasar Spain daga Morocco ranar 2 ga watan Maris 2022,” a cewar bayanin da ke kan daya daga cikin hotunan bidiyon. 

“‘Yan gudun hijira kusan 1,200 suka yi kokarin shiga Spain ta Melilla daga Moroco ranar 3 ga watan Maris, 2022 wasu 380 sun samu sun ketare wuni guda bayan yunkurin adadin mutane mafi yawa da aka taba rubutawa.”

A Karshe

Duk da cewa wadanda ke cikin hotunan ‘yan Afirka ne, ba a iyakar Poland aka rike su sakamakon rikicin da ke faruwa a Yukraniya ba. Dan haka wannan zargin karya ne. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »