African LanguagesHausa

Mata ke rike da rabin sararin sama, amma bayanai marasa gaskiya kan banbancin jinsi na mayar da su baya

Ina yawan shiga tattaunawa dangane da hakkokin mata da mutane, musamman kafin in gama kulla dangantaka da su. Ta yin haka ne na lura cewa tattaunawa ce mai kayatarwa kuma hanya ce ta gane irin ra’ayoyi, alkibla da akidun mutane.

Wata ranar Laraba da yamma a watan Mayun 2023, na gayyaci wasu mutane gida ne kuma kamar yadda na saba, muka fara tattauna batutuwan da suka shafi hakkokin mata. Wasu daga cikinsu na da ra’ayin cewa maza sun fi basira, kuma maza na iya musu dabara su yaudare su cikin sauki. Sun ma hada da misalin tauraron kwallon kafar PSG, Achraf Hakimi, wanda aka yi zargin ya yi wa matarsa wayo ya yi rajistar duka kaddarorinsa a sunar mahaifiyarsa ba da saninta ba, abun da kuma ya bar ta haka nan bayan da aurensu ya mutu.

Wata daya kafin nan, DUBAWA Ghana ta duba labarin inda ta tantance cewa wannan batun ma karya ne.  Sai dai, a ranar da tattauna da wadannan bakin na wa na gode wa Allah cewa ina aiki a wurin da ake tantance gaskiyar labarai. Nan da nan na nuna musu binciken da DUBAWA ta yi a kan batun na kuma kara da nuna musu yadda bayanan karya wadanda ke la’akari da jinsi ke kara haddasa rashin daidaito.

However, the day of the conversation with my guests was one of the times I was grateful to work with a fact-checking organisation. I quickly shared DUBAWA’s fact-check on the subject with them about how gendered disinformation can be used to justify gender bias and inequality.

Gendered disinformation, ko kuma labaran karya wadanda ke la’akari da jinsi, hanya ce ta cin zarafin mata inda mutane ke amfani da labaran karya ko na yaudara su yada batutuwan da ke sa fifiko a banbanci  jinsi ta yadda mata za su noke su gaza yanke irin shawarwarin da ya kamata a ce sun yanke dan tabbatar da cigaba a rayuwarsu, kuma hakan ya kan rage mu su kima a idon jama’a ya kuma hana su shiga a dama da su a harkokin da suka shafe al’umma.

Irin wannan nau’in na bayanai marasa gaskiya shi ne mafi hadari, domin ya fin yin munnunar tasiri a kan rayuwar mata da ‘yan mata, kuma wannan a labaran yau da kullun ake samu kadai ba, har ma da fannonin kiwon lafiya, labarin wasanni da sauransu.

Misali, a halin da ake ciki yanzu akwai ‘yan matan da aka hana karbar allurar rigafinhuman papillomavirus vaccine (HBV) wanda ke kare mata daga kamuwa da cutar daji, saboda wadansu labaran karyar da aka fada wa iyayensu.

Wannan kwayar cutar ta human papillomavirus, bisa bayanan Majalisar Dinkin Duniya, ita ce ke da alhakin kashi 70 cikin 100 na cutur dajin da ke kama mata a al’aurarsu, ita ce nau’in cutar dajin da aka fi gani a mata a mataki na uku, har wa yau a jerin nau’o’in cutar da suka shi kashe mata ita ce na biyu musamman tsakanin matan da ke da shekaru 25 zuwa 44.

Domin shawo kan wannan matsalar a Najeriya, gwamnati ta samar da allurar rigakafin na HPV cikin jerin alluran da ta ke yi dan kai ga ‘yan matan da ake hasashen sun kai miliyan bakwai a kasar yanzu. Wannan allurar ana baiwa ‘yan matan da ke da shekaru daga 9 zuwa 14.

Ko da shi ke akwai shugaban makarantar da ya kwatanta wa DUBAWA yadda wasu iyaye suka gargade su a kan bai wa yaransu allurar wadda a cewarsu “guba” ce. Mambobin wani shafin Facebook, wanda aka fi sani da “Once a mom,, always a mum initiative,” su ma sun yi zargin cewa allurar na iya hana haihuwa dan haka kada iyaye su bari a yi wa ‘ya’yansu.

Sai dai tattaunawar da DUBAWA ta yi da kwararrun likitoci ya bayyana cewa babu wata dangantaka tsakanin allurar rigakafin da mutuwa ko rashin haihuwa.

Haka nan kuma adadin matan da ke shiga siyasa a Najeriya bai kai matsakaicin adadin matan da ke shiga siyasa a duniya ba, saboda mata na yawan fada wa cikin tarkon bayanan karya ko na yaudara da zarar suka shiga takara

Wata kasida da Ms Oloyede Oluyemi daga Hukumar Kididdiga ta Kasa a Abuja ta gabatar ya nuna cewa kashi 6.7 cikin 100 na mata ke shiga siyasa ko ma samun mukamai na siyasa, wannan ko kusa bai yi da adadin sauran kasashen duniya ba inda ake samun kashi 22.5 cikin 100. A sauran kasashen Afirka ma a kan sami kashi 23.4 cikin 100, sa’annan a Afirka ta yamma inda Najeriyar ta ke alkaluma na nuna kashi 15 cikin 100.

Har ila yau, sadda Gimbiya (Princess) Abiodun Oyefusi ta tsaya takarar gwamnar jihar Legas a karkashin inuwar jam’iyyar LP a shekarar 2023, an yi rahotao na musamman aka ce tana shan tabar shisha. Amma shi ma wannan labarin daga baya DUBAWA Ta gano cewa hotunan da aka yi amfani da su an gyara su dan yaudara.

Mata ke da rabin sararin samaniya

A tsukin shekarun da suka gabata, dole sai da mata suka rika nuna cewa su ma suna da daraji kuma ana iya su tare da maza kafada da kafada. Wannan duk da cewa mata sun kunshi rabin al’ummar duniya kuma suna bayar da gudunmawa sosai ga bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya.

Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa na kiyasin cewa darajar aikin kula da yara da aikin gidan da mata ke yi kyauta ya kai kashi 9 cikin 100 na abun da kasashen duniya ke samu kowace shekara wato GDP, adadin da ake kiyasin ya kai dalar Amurka triliyan 11, kuma a cikin wannan adadi mata sun dauki kashi 6.6 ke nan kowace sa’a mata na aiki na tsawon sa’o’i 16 ba tare da samun ko sisi ba.

Bacin haka, matan Afirka sun fi yawan matan da ke sana’o’i a duniya baki daya, inda kashi 25.9 na mata ke kirkirowa ko kuma ma kula da sana’a a yankin kudu da saharan Afirka.

A fannin noma, mata ne ke da kashi 50 cikin 100 na wadanda ke aikin noma a yankin kudu da saharar Afirka, abun da alkaluma ya nuna cewa ya karu da kashi 45 cikin 100 daga shekarar 1980. Matsakaicin adadin na reto ne tsakanin kadan a saman 40 a kudancin Afirka, zuwa kadan a saman kashi 50 a yankin gabashin Afirka.

Duk da haka, muddin aka cigaba da yada labaran karya, batutuwan da ke fifita maza ne za su cigaba da bunkasa, tare da harkokin kiwon lafiyar da za su yi tasiri mai muni a kan mata, ta yadda samar da rayuwar da fi dacewa da su a al’umma zai kasance babban kalubale.

Goyi bayan yaki da bayanan karya da yaudara masu la’akari da banbancin jinsi.

A bururrukanta na samar da cigaba mai dorewa mai lamba biyar, Majalisar Dinkin Duniya ta nunar cewa daidaita tsakanin Jinsi hakkin dan adam ne, wanda ke da mahimmanci ga zaman lafiya, bunkasa da ma dorewar duniya baki daya.

Dan haka, saboda ranar Mata ta Kasa da Kasa, ku dafa mana baya wajen jaddada mahimmancin daidaita tsakanin jinsi, da kuma yaki da bayanan yaudara. Ka da ku taimaka wajen yada bayanan karya dangane da bambancin jinsi, a maimakon haka, ku rike yada labaran da DUBAWA ta tantance.

Bacin haka, ku karanta wadannan labaran na mata ku kuma raba su da ‘yan uwa da abokan arziki dan fadakar da su.

Kawar da ra’ayin cewa gwajin pap smear (wanda ke gwaji kan yiwuwar kamuwa da cutar daji a al’aura da mahaifa) ana yinsa ne kawai wa matan da ke kwana da maza da yawa.

Asalin hoton: YouTube

Pap smear, ko abin da ake kira gwajin Pap, ko kuma Papanicolaou test, gwaji ne wanda ya kunshi binciken yiwuwar kamuwa da cutar dajin da ke kama mahaifa ko kuma wani sauyi a kwayoyin halittar da ke gabobin cikin al’aura dan tantance ko za su iya kai ga kamuwa da cutar daji. Sai dai akwai rade-radin cewa irin wannan gwajin na matan da su iya kamun kai ne kadau. Kuna iya samun karin bayani dangane da wannan batun a nan.

Shin wadanan mata na zanga-zanga ne don adawa da shirin maza na auren mace guda a Finland kamar yadda ake fadi?

Asalin hoton: Google

Akwai wani bayani da ake yi a kai-a kai na cewa mata a kasar Finland sun yi zanga-zanga da riga dan nuna adawa da mazan da ke auren mace guda daya duk da yawan al’ummar da ake samu. A gaskiya maya sun yi zanga-zanga amma saboda yadda ake mayar da jikinsu tamkar wata alama ce ta jima’i kawai, yayin da suke neman a mutunta musu ‘yancin da suke da shi na kare kansu. Kuna iya karanta cikakken labarin a nan.

Sanya gishiri a cikin fitsari ba shi da wani tushe a kimiyya idan ana batun gwajin ko mace na da ciki

Asalin hoton: Women Health Centres

Wani mai amfani da shafin Instagram ya yi zargin cewa ana iya sa gishiri a fitsarin mace dan gane ko tana da ciki. To sai dai babu wata hujja ta kimiyya da ta nuna cewa fitsari na iya sauyawa idan aka sa gishiri dan ya nuna ko mace na da ciki. Amfani da na’urar gwajin da aka saba, ya fi bayar da sakamakon da ake bukata. Kuna iya samun karin bayani nan.

Kwararru sun ce turara al’aurar da mata ke yi na da hatsarin gaske ga lafiyarsu

Asalin hoton: Rebirth Massage
Wani mai amfani da shafin Facbook ya ce idan aka tafasa ganyayyaki masu kamshi da shiri ana iya amfani da su wajen warkar da warin al’aura, ciwon wata-wata na mata da sauransu. Sai dai babu wata hujja ta kimiya da ta tabbatar da hakan. Likitocin mata ba su ma yadda da turara al’aurar ba kuma shi ma wannan labarin kuna iya karantawa a nan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button