Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X @TemidayoOniosun, kwananan nan ya yi da’awar cewa makarantun firamare, sakandare da jami’a duk kyauta ne idan dai na gwamnati ne.

Hukunci: Yaudara ce! Yayin da makarantun firamare, sakandare da ma wasu jami’o’in da ke karkashin gwamnati ba su bukatar kudin makaranta, akwai wadansu kudaden da tilas ne kowani dalubi ya biya kuma idan ba haka ba a hana su karbar darassi.
Cikakken bayani
Ranar 15 ga watan Satumba makarantun firamare da sakandare a Najeriya suka dawo makaranta daga dogon hutu. Bayan nan ne wasu iyaye suka shiga kafofin sada zumunta suna korafin tsadar farashin kudin makaranta, takardu da dai sauran abubuwna da ake bukata dan zuwa makarantar.
Wannan kuma ya biyo bayan korafe-korafen da dama can daliban jami’o’i su ma suka yi a kafofin sada zumunta su ma kan tsadar farashin kudin makaranta, wasu daga cikin masu amfani da shafukan ma har sun yi magana taka mai mai a kan Jami’ar Ilori wadda ita ma ta kara kudin makaranta na sabuwar shekarar ta 2025/2026 da za’a shiga yanzu.
Wannan mai amfani da shafin @theiyanuoluwa cewa ya yi, “Jami’ar Ilori ta fara zama jami’a mai zaman kanta. Kudin makarantar ya karu sosai irin na fitan hankali.”
Wani shi ma mai amfani da shafin da sunan @Uilgist cewa ya yi, “LABARI DA DUMI-DUMI! Daliban jami’ar Ilori sun fashe da kuka ganin yadda wasu tilsa su daina zuwa makaranta saboda farashin da aka kara. Daliban da ke dawowa zasu biya sama da dubu 200 ya yin da wadanda ke shekara ta karshe kuma za’a caje su su kuma sama da dubu 100.”
A wani cigaban kuma, Kungiyar dalibai na Student Union a jami’ar Benin ta fitar da sanarwar da ke karyata da’awar cewa akwai dalibai 5,000 din da ba su biya kudin makaranta ba wadanda za’a hana su rubuta jarabawa.
Yayin da ya ke tsokaci kan fannin ilimi a Najeriya, mai amfani da shafin X @TemidayoOniosun ya yi zargin cewa ilimin firamare da sakandare a makarantun gwamnati kyauta ne, ya kuma kara wa iyaye karfin gwiwa da su sa yaransu a makarantun gwamnati idan har ba za su iya biyan na kudin ba.
Wannan tsokacin na sa martani ne ga wani batun da @DebbieOA ta wallafa, wadda ta ce yawancin iyalai da kyar su ke iya biyan kudin makarantar yaransu, sa’annan dan jaddada wannan ra’ayin na ta ta yi amfani da wani labarin da ya dauki hankali na wasu wasu masu yara biyar wadanda suka gaza biya musu kudin makaranta.
Bisa la’akari da wannan batun ne, Temidayo ya yi bayanin cewa , “makarantun firamare, sakandare da jami’a duk kyauta ne a Najeriya. Duk wanda ba zai iya biyan na kudin ba ya je na gwamnati.”
To sai dai da yawa daga cikin masu amfani da shafin ba su amince da wannan tsokacin na shi ba kums su ma sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da abubuwan da suka faru da su a makarantun gwamnati.
Samun ilimin boko na cigaba da kasancewa batu mai daukar hankali tsakanin masu ruwa da tsaki a ‘yan shekarun baya-bayan nan, musamman bayan wani rahoton da ya nuna cewa a Najeriya kusan yara miliyan 18 ba su zuwa makaranta.
Ganin mahimmancin da batun ke da shi ne ya s, DUBAWA tantance wannan bayani na mai amfani da shafin X dan gano gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Binciken da muka yi da muhimman kalmomi ya bayyana mana wani rahoton da fadar shugaban kasa ta wallafa a shekarar 2023 wanda ya tabbatar mana cewa karatu kyauta ne a duka jami’o’in tarayya. A ciki ne ma gwamnatin ta bayyana cewa abin da ake kira kudin makaranta yawanci kudi ne da ba dole ne a biya ba, ita kanta jami’ar ke caja bisa la’akari da irin bukatun da za ta cimma wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, kamar kudin mafani da dakunan gwaji, yin rajista da dakunan kwana.
Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce kudaden ba dole ba ne, jami’o’in tarayyar kan kira su dole ta kuma ce tilas ne kowa ya biya wannan adadin.
Ya kamata a jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta yi magana a kan jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya ne kadai a matsayin wadanda ba’a biya, ba ta hada da makarantun da ke karkashin jihohi ba.
Bincike ya nuna cewa daliban da ke makarantun jihohi na biyan kudade daban-daban wadanda tilas ne kuma dan haka ya sabawa bayanin da aka yi na cewa kyauta ne.
Alal misali, Makarantun sakandare na gwamnatin tarayya wadanda ake kira Federal Government Colleges da turanci, bai kamata ana biya ba. AMma shi ma duk da haka a kan bukaci a biya kudin rigunan makaranta (na sabbin dalibai) litattafai da takardu, da kudaden magunguna da na wutar lantarki da sauransu. Kudin da daliban da ke yin na kwana a ire-iren wadannan makarantun ya ma karu daga N45,000 zuwa N100,000 a shekarar 2023.
A waje guda kuma, ba da dadewan nan ba ne gwamnatin Najeriya ta sanar cewa Kwalejojin Fasaha na Tarayyar da ke kasar ba kyauta ne kadai su ke ba, gwamnatin za ta ma kara da biyan duk wani karin kudin da za’a bukaci iyaye su biya. Sai dai wadanda ke yin na kwana tilas ne su kawo kayayyakin da suke bukata dan tsayawa a makarantar.
A fanin makarantun firamare kuma, binciken ya nuna cewa makarantun baki daya kyauta ne, sai dai akwai wadansu kudaden wadanad suka hada da kudin PTA, kudin bunkasa makaranta, rigunan makaranta da sauran wasu makamantan wadannan.
Wadannan kudaden ne ake kira kudin makaranta tare da wani dan wanda ake caja dan kula da abubuwan more rayuwa a makarantar. Duk wani kudin makaranta a makarantun sakandare da jami’i’o’i ne ke biya.
Yayin da makarantun tarayya na firamare da sakandare da na jami’a kyauta ne su ma akwai ‘yan wadansu kudaden da ake bukatansu su biya wadanda idan har ba su biya ma za su fiskanci matsala.
Alal misali, daliban da ke Jami’o’in Tarayya dole su biya kudin samun damar shiga kafin a amince da su a matsayin daliban makarantar. Wadanda suka gaza biya kafin ranar da aka sa, ko a kara musu yawan kudin da za su biya ko kuma su rasa gurbinsu a makarantar.
Duk da cewa idan har aka kwatanta yawan kudin makarantun jami’a a Najeriya da sa’o’insu na kasashen waje na Najeriyar ya fi rangwame, makarantun jami’a a Najeriya ba su samun irin tallafin da suke bukata.
A shekarar 2025, kasafin kudin Najeriyar da akaware wa fannin ilimi ya kasance kashi 6.4 cikin 100 na jimilar nera tiriliyan din da aka yi. Wannan na nuna cewa kudin ya ragu daga kashi 8.21 cikin 100n da aka ware a shekarar 2024.
Jami’o’in Jihohi, Makarantun Foliteknik da kwalejojin ilimi duk suna cajan kudi amma salon biyan kan banbanta wa mazauna jihohin da baki, kamar yadda muka gani a nan, nan, nan da nan.
hoton kudin makarantar da aka biya a ABSU
A Karshe
Da’awar cewa makarantun gwamnati a kowani mataki kyauta ne a Najeriya yaudara ce! An dai rage yawan kudin makaranta a na gwamnati amma duk da haka akwai wani kudin da ake karba wadanda dole ne sai an biya.