African LanguagesHausa

Shin sakin ruwan Lagdo Dam shi ya jawo ambaliya ta baya-bayan nan a Najeriya?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: A kwai masu amfani da shafin Facebook da dama da suka yi da’awa claimed cewa bayan bude dam din Lagdo an samu ambaliyar ruwa a wasu yankuna na Najeriya.

Shin sakin ruwan Lagdo Dam shi ya jawo ambaliya ta baya-bayan nan a Najeriya?

Hukunci: Karya ce! Bincike ya nunar da cewa bayan sakin dam din Lagdo ya sanya an samu ambaliya a wasu yankuna na Najeriya, amma abin ya faru ne a 2022 ba kwanannan lamarin ya faru ba. Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da da’awar cewa an sako dam din na Lagdo a bayan nan, inda ta tabbatar da cewa ruwan dam din bai tumbatsa ba, ba a saki ruwan ba, kuma kari a kan wannan rahotanni da sharhi sun nunar da cewa da’awar da aka yi da kuma aka nuna hoto, hoton na Kainji Dam ne ba Lagdo Dam ba. 

Cikakken Sako

Ambaliyar ruwa (Flooding) abu ne sananne a lokacin damina a Najeriya na baya-bayan nan (devastating floods) an samu ambaliyar mai muni da ta taba wasu sassa na kasar a watan Mayu da Yuni, 2025.

Yayin da Najeriya ke fama da kalubalen ambaliyar ruwa wacce ta samu (caused) dalilin sauyin yanayi da ke jawo ruwa mai yawa a wasu yankuna, gwamnatin tarayya ta yi gargadi (warnings) na yiwuwar samun ambaliya a wasu sassa 38 a jihohi 11 na kasar. Gwamnatin Tarayya tace yawan ruwan saman zai iya jawo ambaliya a watan Yuli,2025.

Ana tsaka da kalubalen sauyin yanayi da ke addabar Najeriya sai ga wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Ifite Christain na da’awar cewa a ranar 8 ga Yuli,2025, daga kasar Kamaru an sako Lagdo Dam wanda sakamakon rashin daukar mataki daga bangaren mahukunta a Najeriya an ga yadda aka yi ambaliya a wasu sassa na kasar a ‘yan kwanakin baya-bayan nan.

Taken labarin shine “A karshe an sako ruwan dam din Lagdo bayan Najeriya ta gaza daukar matakin rage asara, sakamakon rashin daukar mataki hakan ya sanya an samu ambaliya a wasu sassa na Najeriya kamar yadda wadannan kafafe suka nunar #Leadership #Proactiveness #Humanity #Nigeria #ifitechristain.””

Wasu masu amfani da shafukan Facebook sun yada wannan labari kamar a wadannan wurare here da here da here da here da here.

DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan batu, saboda irin hadarin da yada labaran da ba haka suke ba yake, musamman ga batun dangantaka tsakanin kasashen biyu da hadin kai da ke tsakaninsu.

Tantancewa

Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a shafin Google, wanda ya nunar da cewa wannan da’awa ta watsu a watan Oktoba,2022, kamar yadda ake gani a wadannan wurare here da here da here.

Rahotanni sun nunar da cewa sakin ruwan daga Lagdo Dam da ya jawo ambaliyar ruwa a wasu sassa na Najeriya (devastating flooding) musamman a yankunan da ke gefen kogin Niger da Benue abin da ya faru a 2022 bayan da Kamaru ta sako (released) ruwan Dam a watan Satumba,2022. 

A wancan lokacin ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamu ya bayyana (announced) cewa kaso 80 cikin dari na ambaliya da aka samu a 2022 a Najeriya ta samu ne dalilin ruwan sama ba wai dalilin sako ruwa daga Dam din Lagdo ba. Mun samu wannan rahoto a kafar yada labaran  TVC News

Babu wata kafar yada labarai sahihiya a Najeriya da ta ba da rahoto cewa an sake sakin ruwa daga Lagdo Dam a watan Yuli,2025.

Da aka sake turawa Google hoton don tantancewa sakamakon ya nunar da cewa hukumar da ke tattara bayanai na ruwa da ake a kasar (Nigeria Hydrological Services Agency (NIHSA) shared  ta yada wannan hoto a ranar 18 ga watan Satumba,2022, a shafinta na Facebook, wanda abin da ta rubuta ba shi da alaka  da Lagdo Dam.

NIHSA, a abin da ta rubuta, inda ta alakanta rubutun da wasu hukumomi da kafafan yada labarai sahihai a Najeriya, ta ankarar da wasu yankuna ne na kasar su bar wuraren da suke zaune a dangane da tambatsar madatsun ruwa na Dam din Kainji da Jabba   

Ga abin da wallafar ta nunar “#flood #flooding #nihsa_ng al’ummar da ke Tasaragi, Lafiaji Patigie da  Shonga har zuwa Lokoja ana basu shawara su bar inda suke zaune, haka nan manoma da ke a wannan yanki, su gaggauta debe kayan amfanin gonarsu don gudun asara, kasancewar madatsun ruwa na Kainji da Jebba suna tumbatsa.

Did release of Cameroon's Lagdo Dam cause Nigeria's recent flooding?Hoton wallafar daga shafin Facebook na  NIHSA.

Neptune Prime ta rawaito cewa wani bidiyo da ke nuna tsohon babban darakta hukumar agajin gaggawa ta jihar Niger (NSEMA), Ahmed Inga, na ba da bayani cewa sun samu bayani daga hukumar da ke lura da albarkatun ruwa ta kasa a Najeriya cewa za a rika sako dubban galan na ruwa daga madatsar ruwa ta Dam din Kainji da Jebba  wanda zai jawo tumbatsar kogin Niger da ke a jihar ta Niger.

Wasu wallafar da aka yi a shafukan na Facebook kamar a wadannan wurare here da here sun nunar da cewa daga Kainji Dam ne.

Bayan kallo na tsanaki ga bidiyon da aka yi da’awar Lagdo Dam an gano cewa saman Dam din yayi kama da na Kainji Dam sabanin yanayi mai kama da gefen kwarya da Lagdo Dam ke da shi. 

Did release of Cameroon's Lagdo Dam cause Nigeria's recent flooding?Saman Dam din na Kainji da Lagdo kamar yadda aka dauko hotunansu  na bidiyo  Asalin hoto: Africa Energy Portal.

Gaza daukar matakai na kariya

Rahotanni na kafafan yada labarai sun tabbatar da cewa Najeriya bata kammala aiki ba na samar da madatsar ruwa ta Dasin Hausa Dam har zuwa wannan lokaci sabanin asalin yarjejeniiya (agreement) da aka kulla tsakanin kasashen biyu. Wannan ana sa rai ya zama madatsa da za ta rika rage karfin ruwan da ake sakowa daga Lagdo Dam da kare afkuwar ambaliya anan gaba.

Aikin madatsar ruwan na Dasin Hausa Dam ya tsaya (remained) sama da shekaru 40

Gwamnatin Najeriya (Nigerian government)n a watan Maris, 2025  ta ce za ta gaggauta aikin kamar yadda za a gani a wadannan rahotanni here da here da here.

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da da’awar s ako ruwa daga Lagdo Dam

A cewar wasu rahotanni na kafafan yada labarai sun nunar da cewa gwamnatin Tarayya ta yi watsi  (dismissed) da rade-radin cewa za a sako ruwa daga Lagdo Dam abin da ta bayyana da cewa jita-jita ne, labaran karya na yaudara.

Rahotan da jaridar Guardian report ta fitar ya nunar da cewa ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Joseph Utsev ya tabbatar da cewa mahukunta a Kamaru basu sako ruwa daga madatsar ruwansu ba.

Rahotannin suka tabbatar da cewa an jiyo hakan ne bayan ganawarsa da da manajan dam din Ahmad Bivoung a ranar 7 ga waytan Yuli,2025, kuma ruwan ya ma yi kasa da misalin mita 2.06, sannan babu wani sakin ruwa da aka yi a bayan nan, za a iya ganin wanann rahoto a wadannan wurare here da here.

A Karshe

Da’awar cewa an sako ruwa daga Lagdo Dam a baya-bayan nan abin da ya jawo babbar asara, wannan ba haka lamarin yake ba karya ce. An saki Lagdo Dam ne abin da ya shafi Najeriya tun a 2022, Babu ruwa da aka sako daga Kamaru a baya-bayan nan. Hoton da aka nuna Kainji Dam ne ba Lagdo Dam ba. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »