|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya ce hamshakin attajirin duniya Elon Musk ya auri mutum mutumi (Robot)

Hukunci: Karya ce! Elon Musk ba ya auren mutum mutumi, bidiyon da ake yada wa an kirkira ne da fasahar kirkirarriyar basira.
Cikakken Bayani
A wani bidiyon da wani mai amfani da shafin Facebook Saidu Sani ya wallafa, tare da sharhi a cikin harshen Hausa, ya yi bayani kan yadda fasahar kirkirarriyar basira ke samun karbuwa a duniya kuma ake ci gaba da fitowa da abubuwa daban daban na ban mamaki.
A cikin maganarsa ya yi da’ar cewa “Elon Musk ya na auren robot (macen sakago)” a dai dai lokacin da hotunan bidiyon wanda ya kafa Tesla, Elon Musk ke nuna yana sumbatar macen mutum-mutumi, a matsayin shaida cewa ya samar da “matar robot” kuma yanzu haka tare suke zaman aure.
Wannan bidiyon ya dauki hankali sosai, domin zuwa ranar 11 ga watan Fabrairun 2025 an kalli bidiyon sau miliyan daya da dubu dari uku, haka kuma an yi tsokaci fiye da dari hudu akan bidiyon.
Dubawa ta yi bincike domin tantace gaskiyar wannan da’awa ganin yadda labarai na karya suke zama babbar barazana ga al’umma.
Tantancewa
Bincike na tsanaki da Dubawa ta yi, ta lura da cewa wannan hotunan da ke motsi da ke nuna Elon Musk da mutum mutumin ba na gaskiya bane, an kirkire shi ne ta hanyar amfani da fasahar Deep Fake ta kirkirarriyar basira wato AI.
Wasu abubuwan da suka nuna cewa ba gaskiya bane sun hada da yanayin fuska da motsin bidiyon wadanda suka sha ban-ban da yadda mutane ke yi, misali a yayin da yake rawa ya daga hannunsa kamar suna rike da hannun juna da mutum mutumin, amma za a iya ganin hannunta a kasa.
Binciken da muka yi a shafin nema na Google, mun gano cewa wannan bidiyon ba gaskiya bane, Elon musk baya auren mace mutum mutumi (robot) ko gina wani robot a matsayin mata, kamar yadda sashen binciken gaskiya na kafar yada labarai ta France24 ta gano.
Haka zalika binciken da muka yi ya nuna cewa Elon Musk mata uku ya taba aure kuma a yanzu dukkaninsu ba sa tare da shi, ta farkon Justine Musk daga 2000–2008 sai Talulah Riley daga 2010–2012, bayan sun rabu ya sake aure Talulah Riley daga 2013–2016.
Sai dai a shekara ta 2022 ne hamshakin attajirin nan na fasaha Elon Musk ya gabatar da sabon samfurin wani mutum-mutumi da kamfaninsa na motocin lantarki na Tesla ya kera,
Mutum mutumin da aka yi wa suna da ‘Optimus’ ya bayyana a wani taron inda ya rika daga wa mutane hannu kuma ya ɗaga kafafunsa, a cewar kafar yada labarai ta BBC.
Optimus’ – Mallakar Tesla
Sai dai Elon Musk ya ce ana ci gaba da kirkirar robot din, nan da wasu shekaru za a fara sayar da shi, kuma za a saukaka shi ta yadda kowa zai iya saye ba tare da wahala ba.
Kafar yada labaran fasahar sadarwa da kudaden badini wato cryptocurrency ccn.com ta ruwaito cewa sai nan da shekara ta 2026 ake sa ran wannan fasahar za ta fara shiga kasuwa domin al’umma su saye.
A Karshe
Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa Elon Musk ba ya auren mutum mutumi, bidiyon da ake yada wa an kirkira ne da fasahar kirkirarriyar basira.




