|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Gwamnatin Najeriya ta Mayar da Tallafin Man Fetur.

Hukunci: Karya ce! Babu wata shaida da ke nuna cewa gwamnati ta mayar da tallafin man fetur.
Cikakken Bayani
Tun lokacin da aka rantsar da sabuwar gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewar gwamnatinsa ba zata biya kudin tallafin da ake sanyawa a man fetur ba, abinda ya tabbatar da kawo karshen shirin tallafin baki daya.
Yayin da yake jawabi bayan karbar rantsuwar fara aiki, shugaban yace zasu karkata irin wadannan kudaden da ake biyan tallafin da su wajen gina kayan more rayuwa da bunkasa ilimi da harkokin kula da lafiya da kuma kirkiro ayyukan yin da zai taimaki miliyoyin jama’a.
Wannan matakin ya yi sanadiyar tashin farashin kayan abinci da na masarufi, tare da duk sauran abubuwan rayuwa na yau da kullum, lamarin da ya jefa al’umma cikin matsin rayuwa. Sai dai Shugaba Tinubu ya nace cewa cire tallafin shine abinda ya dace ga kasar nan.
Wani shafin jarida na HAN HAUSA a Facebook ya wallafa wani labarin dake cewa gwamnati ta mayarda tallafin man fetur, lamarin da mutane da dama suka yi tsokaci (Comment) har sau 33, yayinda aka yada (Share) har sau 8 kuma aka danna alamar So (Reaction) har sau 66.
Hoton da aka zakulo a Facebook
Ganin yadda ake tattaunawa da tsokaci akan wannan labarin cire tallafin mai a baya bayannan da kuma kasancewar man fetur ya shafi kowane bangare na rayuwar mafi yawa da cikin al’ummar Najeriya, Dubawa tayi bincike domin gano gaskiyar wannan labari.
Tantancewa
A yayin binciken da muka yi mun gano cewa tun a cikin wata uku na farko bayan cire tallafin mai ne aka fara samun rahotannin dake cewa gwamnati za ta mayar da tallafin man fetur. Misali jaridar The Cable ta wallafa wani labari da ta samu daga wata majiya a fadar shugaban kasa. Ba ta bayyana sunar majiyar ba bare mu san sahihancinta illa dai ta ce “jami’i a fadar shugaban kasa.”
Wani rahoton da kafar yada labarai ta BBC Hausa ta wallafa ya nuna cewa gwamnati ta sake mayar da tallafin a fakaice,
Shi ma shugaban kungiyar ma’aikatan bangaren mai da iskar gas wato PENGASSAN, Festus Osifo, ya fada a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels cewa “har yanzu gwamnati na biyan kudin tallafin man fetur” kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
A bayannan Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewar har yanzu Gwamnatin Tarayya na biyan kuɗin tallafin man fetur. Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, inda ya ce Gwamnatin Tarayya na kashe maƙudan kuɗi fiye da lokacin Shugaba Buhari.
Mece ce Hujjar su?
Masu wannan ikirarin na ganin cewa tun da gwamnati ta cire tallafi abin da zai biyo baya shi ne kasuwa ce za ta juya farashin sa, abinda ke nufin idan farashin danyen mai ya tashi a duniya to farashin man fetur zai tashi a Najeriya sai dai har yanzu farashin yana nan yadda yake duk kuwa da cewa farashin danyen mai yana tashi kuma ya sauka.
“Idan mutane suna so su gane yadda ake biyan tallafin man fetur ɗin, sai su kwatanta yadda farashin man fetur da na dizal yake, wanda a ƙa’ida ya kamata a ce farashin fetur ya haura Naira 1000 kan kowace lita,” in ji El rufa’i.
Gwamnati ta Musanta Mayar da Tallafin
Sai dai a bangare daya kuma shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL, Mele Kyari ya karyata wadannan labarun da ake yadawa cewa an mayar da tallafin man fetur a Najeriya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Kyari yayi wannan jawabin ne bayan ganawar sirri da Shugaban Kasa Bola Tinubu a 9 ga watan Oktoban 2023.
Shi ma Karamin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri, ya kalubalanci dukkanin masu wannan ikirarin cewa su kawo shaida akan kalaman su, inda ya kara jaddada cewa tun lokacin da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur har yanzu maganar ba ta sauya ba.
Haka Zalika da jaridar Leadership ta tuntubi Shugaban sashen yada labarai na kamfanin mai na kasa NNPCL, Olufemi Soneye ya karyata ikirarin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi cewa an mayar da tallafin man fetur.
Kamfanin mai na kasa NNPC ya kuma ce yana samun kudaden da ya saka wajen shigo da man fetur a Najeriya ba tare da yayi asara, kuma ya dage cewa babu wani abu kamar tallafin man fetur. NNPC ce kadai ke shigo da mai Najeriya a halin yanzu.
‘Yan Kasuwar Mai
A wata fira da kafar yada labarai ta BBC, Shugaban ƙungiyar Arewa Oil And Gas marketers Association, AROGMA, Alhaji Bashir Dan-mallam ya ce tashin farashin dala ba ya shafar kamfanin NNPCL da ke shigo da man Najeriya kai-tsaye, kamar yadda dillalan man ke sayen dala a kasuwar bayan fage.
Saboda haka ya ce gwamnati haƙuri ta ke yi da ƙaramar riba don tirke farashin man, domin man da ƙasar ke fitarwa waje da dala take sayarwa kuma ta sayo tatacce daga wajen da dala, saboda haka daga cikin wannan kuɗi ne da take samu take haƙuri da kaɗan.
Ra’ayin Masu Sharhi kan Lamurran Yau Da Kullum
Shaihin Malami a Jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto Farfesa Bello Bada na da ra’ayin cewa “a bayyane take cewa tallafi ya tafi”.
A cewar sa idan aka yi la’akari da irin kudaden shiga da gwamnati ke samu a kowane wata to hakan zai tabbatar da cewa ba’a biyan tallafin mai.
“Mu mun san tallafi ya tafi, domin kowane gwamna a jiha kana ganin suna bacaka da kudi kuma wannan kamar jinin mu ne suke bacaka da shi saboda karin kudin mai ne da aka yi mana ta hanyar suke samun wadannan kudaden suna rabawa a kowane wata, inji Farfesa Bada.
Farfesa Bello Bada yace sanadiyar rashin karin kudin mai shi ne gwamnati tana tsoron abinda zai biyo baya, “saboda an kai talaka a bango” talakawa zasu iya yin bore.
“Gwamnati bata mayar da tallafi ba, saboda idan ta mayar da tallafi da sai an sayar da man fetur naira dari biyu”
A Karshe
Karya ce! Binciken da muka yi babu wata hujja gamsashshiya dake nuna cewa gwamnati ta mayarda tallafin man fetur a Najeriya.
An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.




