African LanguagesHausa

Farashin man fetur ba zai sauka zuwa N550 idan har Dangote ya fara sayar da man a cikin gida ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa : Dangote zai sayar da man fetur a kan N550 kowace lita .

Farashin man fetur ba zai sauka zuwa N550 idan har Dangote ya fara sayar da man a cikin gida ba

Hukunci : Yaudara ce! Bincike ya nuna mana cewa babu inda matatar man Dangote ta ce za ta sa farashin man fetur a kan N550.

Cikakken Bayani

A wani labarin da shafin LegitHausa ta wallafa, ta yi da’awar cewa ‘yan kasuwar man fetur a Najeriya sun kawo sabon farashin mai a daidai lokacin da matatar man Dangote ke shirin fara sayar da shi a kasuwa, shafin ya kuma kara da cewa rahotanni sun ce ‘yan kasuwar sun bayar da shawarar sanya sabon farashin a kan Naira 550 kan kowace lita. A cewar jaridar wannan matakin na zuwa ne saboda kamfanin NNPC na sayar da man wa dillalan man a kan Naira 556 su kuma su saida N640.

Ganin yadda tsadar farashin man fetur babban labari ne a Najeriya musamman a wannan lokacin da ake fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi, mutane da dama ne suka yi tsokaci a kan labarin a musamman a shafin Facebook inda  Kabiru D Chinan Jan ya ce “Hmm Najeriya ke nan, wai dan kasuwa ke tsaida farashin mai a Najeriya?”

 A yayin da shi ma Ank Malm ya yi tambaya makamancin na Kabiru ya na cewa  “yaya za’a ce dan kasuwa zai tsaida farashi?” irin wadannan tambayoyin ne suka sa DUBAWA ganin anya? da walakin goro a miya. Bacin haka wannan babban labari ne da an gani a manyan kafofin yada labarai a duk fadin kasar.

A lokacin da muka ga wannan labarin mutane sama da miliyan daya sun latsa alamar like, akwai tsokaci 60 kuma an sake yadawa sau 24.

Ganin yadda batun farashin man ya dauki hankali ne ya sa DUBAWA tantance gaskiyar labarin domin ko a watan Fabrairu, jaridar Premium Times Hausa ta dauki labarin inda kotu ta umurci gwamnatin Tinubu ta rage ta kuma tsaida farashin man fetur da na kayayyakin masarufi

Tantancewa 

DUBAWA ta fara da amfani da mahimman kalmomi dan gudanar da bincike kan sahihancin labarin da ma dubawa a gani ko sauran kafafen yada labarai masu nagarta sun dauki labarin. Daga nan ne muka ga bayanan da suka fito dangane da sayar da man matatar Dangote a shafin VOA wato Muryar Amurka, sai kuma shafin LegitHausa, sa’annan duk sauran labaran da muka gani dangane da matatar man tsoffi ne wadanda aka yi tun lokacin da aka fara kaddamar da matatar man a bara.

To sai dai labarin na VOA bai ce ‘yan kasuwa sun tsaida farashi ba ko kuma ma Dangote zai rage farashin man ba. Iyakaci dai ya ce an fara fitar da bakin mai wato dizal da man jiragen sama zuwa wuraren da ke bukata a cikin gida kuma dangane da batun man fetur kuma ya yi bayani kamar haka:

“Matatar man Dangote ta Najeriya ta fara samar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida, Shugaban ma’aikatar Dangote, Devakumar Edwin, ya bayyana, kuma in ji kungiyoyin sayar da man fetur, wani muhimmin mataki ne a yunkurin da kasar ke yi na samun dogaro kai a fannin makamashi.

“‘Yan kasuwar man na gida sun amince da farashin Naira 1,225 wanda ya yi kasa dalar Amurka 1 a kowace litar dizal bayan wata yarjejeniya da suka kulla, in ji Abubakar Maigandi, shugaban kungiyar masu kasuwancin fetur mai zaman kanta.”

Haka nan kuma a shi kan shi labarin da LegitHausa ta yi, a maimakon tabbatar da cewa lallai Dangoten zai sayar da man a kan N550, ta yi karin bayani ne a kan cewa kungiyar masu sayar da man fetur din wato IPMAN shawara ce ta ke bai wa matatar man na Dangote. Mun kuma tsakuro kadan daga cikin bayanin da ta yi kamar haka: 

“A cewar shugaban IPMAN, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ‘yan kasuwa da matatar Dangote yanzu haka. Hakan Zai Rage Farashin Man Fetur Idan Matatar Dangote Ta Amince da bukatar IPMAN.” 

Ana dai kyautata zaton matatar man Dangote za ta taimaka wajen kawo karshen dogaron da Najeriya ke yi kan kayayyakin man fetur da ake shigowa da su daga kasashen waje duk da cewa Najeriya ita ce kasa mafi yawan al’umma a Afirka, kuma ita ce kan gaba wajen hako mai, amma duk da haka tana shigo da kusan dukkan man da take amfani da shi saboda rashin matatu.

Sai dai bisa dukkan alamu ko da ma za’a rage farashin man ba wannan farashin na N550, tunda ba su da hurumin tsayar da farashin man fetur, kuma ko da ma za’a rage farashin za’a yi la’akari ne da abubuwan da ke faruwa a kasuwannin man da kuma tattalin arzikin kasar kamar yadda wani kwararre a fannin ya bayyana mana.

Ra’ayin kwararre

DUBAWA ta tuntubi Thomas Audu wadda ke aiki da Calm Waters Integrated Services, wanda kamfani ne da ke kula da sufuri na man fetur da iskar gas, wanda ya fara da bayyana mana cewa matatar man Dangote ba ta ma fara sayar da man fetur ba tukuna, kuma ko ta fara ba zai yiwu ta sayar akan farashin 550.

“Da kyar ne za’a sayar da man a wannan farashin saboda darajar musayar kudi da kuma farashin danyen mai,  hade da farashim dauko man fetur a kawo da kuma farashim sarrafa kayayyakin aiki. Zai yi matukar wuya ya samu a hakan,” Audu ya bayyana.

Ya shaida kuma shaida mana cewa ko shi bakin man ba zai saidu a saukake ba sanadiyyar darajar masayar kudi. 

A Karshe

Da’awar dake cewar matatar man Dangote ta tattauna da IPMAN da cewar zata sayar da man fetur a farashin 550, Yaudara ce!

Mai binciken ta yi wannan aiki ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024, a shirin samun kwarrewa na Kwame KariKari da hadin gwiwar Debora Majingina Habu, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button